Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx
Chapter 21 of 28
Chapter 2️⃣1️⃣ Mari da Kiss 👋💋🔥
SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃
Aleena ta buɗe idonta, haushi yana ƙara hura cikin zuciyarta, ta furta a hankali.
“Idan har Omar yana jin wani abu game da ni a zuciyarsa, ko kuma yana tunanin saboda igiyar da take kaina ya mallake ni, toh lallai dole nayi abinda ya dace. Kuma zan fahimtar da shi hakan bazai yu ba.”
Ta tashi daga gado ta shiga closet, ta ɗauko riga ƙarama mara nauyi ta saka sannan ta koma kan gado ta kwanta tana jan babban bargo mai laushi jikinta. Fatan zuciyarta—Allah yasa bacci ya sace ta kawai ta huta.
Ta kalli agogon bango. 1:11am.
“Come on Aleena, ki bacci kawai…” ta furta a hankali tana ƙara lumshe idanunta cikin bargo. Amma duk da haka baccin ya ƙi zuwa. Zuciyarta sai yawo take yi da tunani iri-iri.
Cikin gurnani ta tashi daga kwance ta yakkace bargon da rabin sa ya fadi ƙasa ta mike tsaye.
Ina Omar ya je? Yana ina haka yanzu? Ta ja dogon tsaki tana hura iska ta bakin ta. Babu bacci a idonta kuma baccin ba zai samu ba har sai sun yi magana game da abinda ya faru ta tabbatar da cewa duk abinda Emir yake zargi ba haka bane. Sannan kawai zata iya rufe idonta.
Cikin wannan tunanin, Aleena taji takun tafiya a corridor.
Ba tare da wani tunani ba ta yi saurin nufar ƙofa. Zuciyarta na bugawa da ƙarfi ta ja handle ɗin ta buɗe—daidai lokacin Omar ke shigowa daga karshe kusurwar corridor, yana kan hanyarsa zuwa ɗakin shi.
Ya wuce ta idonsa ya sauka akanta na ɗan sakanni. Ya shiga ɗakin nasa ya rufe ƙofar da ƙaramin ƙara, wanda ya sa Aleena ta dan firgita, zuciyarta ta karye da wani irin nauyi a kirji.
Cikin hanzari ta bi bayansa. Ta shiga ɗakin tana sakin ƙofar ta rufe da ƙarfi.
Omar yana yawo a cikin ɗakin a hankali ko kallonta bai yi ba.
Ya saka hannu ya zame agogon hannunsa, ya ajiye a gefe, sannan ya fara kwance maballin rigarsa. Ya zaro wayarsa daga aljihunsa, ya ajiye akan madubi cikin nutsuwa, kamar babu komai da ya faru.
“Ina ka je?” Aleena ta buƙata da ɗan daga murya. “Dare yayi, Omar. Iyayenka sun zo babu sanarwa, me yasa baka ɗauki kiran su ba? Ka sa su shiga damuwa.”
Ta dafa ƙirjinta tana kallonsa tana shirin ƙara magana—amma yanayin yadda yake cikin nutsuwa kamar babu komai ya sa duk kalaman suka subuce mata. Haushi ya ci ƙarfin ta takaici ya ƙara turnuƙe zuciyarta.
Omar bai ɗaga kai ya kalle ta ba ya ci gaba da sabgarsa tamkar ba ya jin komai.
“Kana kuwa jin abinda nake cewa, Omar? Ko kana pretending baka ji ne?” Aleena ta sake ɗaga murya, amma har yanzu motsinsa a hankali yake kamar wanda bashi da damuwa.
Ya wuce ta gefenta. A lokacin ne ta ji wani irin wari na giya da turaren jiki mai ƙarfi ya buga mata hanci. Haduwar ƙamshin turare ba daya ba biyu ba yasa gabanta ya faɗi cikinta ya ɗan kada.
A take anan ta gane.
Omar abuge yake. Wato mayaudarin ya koma kan sana’ar tasa.
Ya buɗe drawer ya ɗauko kayan bacci ya jefa su kan gado cikin rashin damuwa.
Wannan ya ƙara bata mata rai.
“So… shiyasa baka ɗauki kiran iyayenka ba kenan? Allah ya taimake ka na rufa maka asiri,” ta furta tana kallonsa muryarta ɗauke da ɗaci mai sauti kamar guba. “Inda ba haka ba, da tuni suna nan suna jiranka, kai kuma kana can kana yawon banza da karuwai.”
Kalaman suka subuce mata kafin ta iya dannesu. Wanda hakan itama ya bata mamaki. Amma abinda ya fi bata haushi—ganin cewa Omar yana waje yana shan giya da yawo da matan banza .
Zafin da take ji ya ci ƙarfin ta.
Omar ya tsaya cak, dakin ya ɗauki shiru.
Ahankali ya juyo ya kalleta fuska da fuska. Idonsa sun yi duhu, kamar wanda baya cikin hayyacinsa. Ya tsunduma kallon ta.
“Mey kika ce?” Ya furta a hankali, muryarsa ahankali cikin sanyi amma kalar kallonsa cike da wani irin kaifi wanda yasa Aleena duk tsikar jikinta ta tashi.
Ta dake ta girgiza kai, ta matso kadan kusa da shi, tace:
“What? Karya nayi? Ai kaji abinda nace. Sai da nayi karya na rufa maka yau. Gobe kuma zaka iya yin karya kace ka kaini gidan Nesa, sannan ka fita tare da su Ali da Kemal. Kuma ka daina yawon banza da karuwai, kuma ka yi tunani inda iyayenka sun san cewa baka daina halinka ba.”
Aleena ta yi shiru, sauran kalamanta suka tsaya a makogwaron ta. Idanunsa babu alamar yafiya jikin ta yayi ihun ficewa amma kafafunta suka tsaya cak. Kallon da yake mata yana huda ta kai tsaye, taji zuciyarta tana fada mata da alama: wannan maganar tasu baza ta kare lafiya ba.
“Meysa kika yi shiru? Ki karasa abinda kike fada.”
Omar ya fadi muryarsa dauke da kaifi. Ya kara taku zuwa gare ta.
Nan da nan ta ja baya tana matsawa, zuciyarta tana bugawa da sauri. Aleena ta cigaba da matsawa baya tana kokarin bada space tsakaninsu, amma cikin wani hanzari Omar ya isa gare ta ya chakumo kafadarta. Da sauri ta ture shi tana kara matsawa cikin wani irin sauri. Fuskarta ta kumbura da damuwa babu dariya a cikinta.
Idon Omar ya hau tsane, dauke da wani abu da Aleena ta kasa fassara shi.
“Fada mun Meysa, zan tsaya in saurare ki.” Omar ya fada yana jan tsaki.
“Meysa, ni bazan ji dadin rayuwata ba? alhalin ke kina yawo agari kuma kina karya duk sharadin da na saka miki. akan mey? saurayinki? Kin taba damuwa da iyayena ne? Baki taba damuwa dasu ba koda sau daya saboda irin yadda kike mu’amala da Emir.”
Kalamansa sun buge ta tamkar mari.
“Stop, Omar. Kasan na damu da iyayenka. Kaga Omar, zamuyi magana gobe, yanzu baka cikin hayyacinka. Zamu sake sa sabon sharuddai sannan zan kuma yiwa Emir magana akai.”
“Shut up, Aleena!”
Ya katse ta da tsaki cikin taku daya ya rufe tazarar da ke tsakaninsu.
“Sharuddai? Mene ne su ma? Abinda kika dauke su kamar wasa?!”
Hannunsa ya rike hannun ta tamkar karfe. Aleena tayi kokarin yakkace hannunta amma ya rike ta sosai.
“Sake ni natafi, Omar!” Aleena ta fada jikinta yana rawa da tsananin tashin hankali.
Amma ya kafe ta Idanunsa jajir.
“Meysa zan sake ki? saboda me? Don ki cigaba da zagina? Ko ki ce zaki fada min abinda zan yi?”
Aleena ta ja hannunta da karfi har wajen ya yi ja saboda tsananin rikonsa. Tace da rawar murya:
“Ni dai kawai ina tuna maka akan iyayenka. Da ban rufa maka asiri ba, da komai ya yi muni. Sunzo gidan yau, daga ni har kai bama nan. Baka dauki kiran su ba. Do you know how it feels nayi musu karya akan idonsu?”
Omar ya matso da muryarsa mai nauyi:
“Kin taba tunanin hakan abaya? Da kike kin kwana a gidan? Ko kike yawo a gari da wani? Kin taba tunanin hakan? Ba wai daren yau kadai ba Aleena – iyayena za su iya ganinki ko ina, ko yaushe. Kin taba tunanin hakan lokacin da san kanki ya dauke ki? Don haka, kar ki daura min laifin daren yau. Na sha rufa miki tun daga farkon auren nan. Amma ke? Babu abinda kike sai karya duk wani layi da na zana miki.”
Aleena tayi shiru numfashinta ya tsaya. Magnaarsa duk gaskiya ce, kuma babu wanda bai da nauyi. Amma a cikin zuciyarta sai kalaman Emir suka dawo mata taji wani bacin rai yana taso mata.
Shiru ya danne su. Omar ya ja baya da numfashi mai nauyi bacin ran sa ya karu.
Sai Aleena ta yi wani dan tunani: Omar baya hayyacinsa. Wannan zantukan zai iya mantawa dasu kafin gobe. Kuskurene in ci gaba da magana dashi.
Dole a yanzu daya acikin mu ya sauko.
“Zan koma dakina. Zamuyi magana gobe.”
Aleena ta fada tana jan taku baya. Amma kafin ta kara wani takun Omar ya fisgota.
“Dole ki dena ganin Emir!” ya fada cikin karamin tsaki muryarsa ta yi karfi sosai yanzu.
Aleena taji jinin jikinta ya daskare. Wani dunkulallen abu ya tsaya cikin kirjin ta.
“Bazan iya ci gaba da kallon ki kina raina auren nan ba, Aleena. Bazan taba bari ba.”
Aleena ta buɗe baki da niyyar maida masa da magana, amma sai ta kasa. Bakin ta ya bude ya rufe, kalmomin suka ƙi fitowa. Tsayuwarsa, kalamansa—duk sun daure ta, ji tayi kamar wacce aka kama da laifi.
“Kina ganganci, Aleena. Kuma bazan bar ki kina yadda ranki yake so ba. End it. Relationship ɗinki da shi ki yankeshi. Ki yi respecting auren nan har zuwa December. Bazan ƙara bari ki ci gaba da risking hakan ba. Saboda bazai yiwu ba ace kullum ina tuna miki abin da na riga na zana miki layi akai. This is the last time. Bazan ƙara rufa miki asiri ba.”
Aleena ta ji wani irin zafi ya cika zuciyarta. Kana tunanin zaka iya juya komai na rayuwata, Omar? Ta furta da murya mai rauni amma mai zafi.
“Ni ba mallakinka bace. Ba zan bari kowa ya faɗa min yadda zan yi rayuwata ba. You don’t own my life. Zaka iya ci gaba da fucking karuwanka kamar yadda ka saba… amma ka fita daga harkata da relationship dina. Sakeni yanzu, natafi.”
Ta fisge hannunta daga riƙonsa cikin hanzari, zata fita. Amma wani irin dariya mai hadari da yayi ya sa ta tsaya cak. Ta juya tana kallonsa, zuciyarta na harbawa da bacin rai.
“Abin dariya,” Omar ya furta yana murmushin da ba shi da kyau. “Kince ina fucking karuwai kamar ɗan iska. Wannan ai halinki kike fada mun. Are you not the same with me? Bambanci kawai, ni ban boye ba. Ke kina boye shi da munafurcin soyayya.”
Dukkan wani control da Aleena take riƙe da shi ya narke. Zuciyarta ta yi wani irin fashewa. Ba tare da tunani ba ta ƙarasa kusa da shi, ta zabga masa mari da ƙarfi. Sautin marin ya cike dakin wanda ya girgiza shi, idonsa yayi duhu, bakinsa ya buɗe kaɗan.
“Ka tauna kalamanka kafin ka sake faɗa min!” Muryar Aleena tana rawa cike da kuka da jin nauyin zuciya. “I hate you, Omar. Go to hell!”
Ta juya cikin hanzari zata fita. Amma sai ta ji takunsa a bayanta. Kafin ta kai hannu ta buɗe ƙofa, Omar ya kama hannunta da ƙarfi ya ja ta baya har tana tuntube. Ya manneta da jikin ƙofa riƙonsa babu tausayawa.
Ba tare da magana ba. Ya haɗa bakinsa da nata. Wani dan karamin numfashi ya fita daga bakinta saboda ƙarfin kiss ɗin was deep and demanding hannunsa ya fara taba jikinta ta ko ina kamar wani mahaukaci. Giyar kan harshensa taji yana shiga cikin harshenta Zuciyarta ta rikice kanta taji ya fara juyawa.
Jikinta ya tsaya cak. For some seconds ji tayi ta kasa motsi, zuciyarta tayi mata ihun ta tureshi. Aleena ta ɗaga hannu tana ƙoƙarin ture shi, amma ya matse ta da bango, jikinsa yana manne da nata. Ƙarfinsa ya yi mata yawa.
“Mey haka kake yi?!” Aleena ta furta cikin bakinsa tana ihu tana turashi amma babu amfani. Hannunsa ya kama fuskarta da ƙarfi, idonsa yayi jajir kallonsa yayi zurfi cikin idonta yana karanta duk wani tunani da tsoron dake fuskarta.
💘AUREN ALEENA💘
Amal Musa ✍️
SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.