Complete Hausa Novels

Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel

Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx

Chapter 15 of 28

Chapter. 1️⃣5️⃣ Tomato Juice 🍅🥤

SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃

Daga ƙarshe, Emir bai yi gardama ba. Kamar yadda daman yayi tsammanin Omar zai tunkare sa da kuma fada masa maganganu da kuma cewan ya yanke hukunci. Amma kuma sai dai Emir abu ɗaya kawai yace wa Omar, shine: “Soyayya ba kullum take bin tunani ko lissafi ba,” duk da cewa sati biyu da suka wuce ya faɗa wa Omar cewa ba zai dawo wurin Aleena ba.

Amma gashi ya dawo. Bai tsaya kan maganar sa ba. Kuma hakan yasa Aleena cikin farin ciki da godiya gare shi. Amma duk da bayan gama wayar su hakan ya barta cikin damuwa, jin kunyan kanta da kuma tunanin hakan daidai ne kuwa?

Ga Aleena yanzu, a cikin sabon gida kyauta daga iyayen Omar. a ƙarƙashin rufin gida daya da mutumin da tafi ƙiyayya dashi a duniya.

Idanunta suka zagaye dakin suna kallon kowane kusurwa suna duba ko ina.. Kayan dakin sun kasance masu kyau, komai sabo ne. Aleena ta shafa gefen table da yatsunta tana jin sanyin itacen a karkashin fatarta.

Gidan bai kai katafaren gidan da ta taso da Granny ba, balle gidan Thorne family da ke da girma. Amma shima yana da nasa girman da kyau. 4 bedrooms - daya Master bedroom sai guda uku guest room na baki da kuma babban falo da dining area babba wanda yake hade da kitchen da kuma bar wajen shan su lemo da giyar Omar.

Ta bude sliding door glass ta falo, hasken yamma yana shiga ciki sannu a hankali yayin da ta fita wajen gidan. Bayan gidan yana da fadi sosai tafkeken swimming pool ne awajen wanda ya hadu hasken yamma dake sauka ciki.

Ta durkusa ta tsoma yatsunta a cikin sanyin ruwan sanyinsa ya bada dumi mai nishaɗi akan fatarta. Ta mike sannan idanunta suka sauka akan wata doguwar kujera a gefe mai laushi da table a tsakiya – duk kamar suna jiran a zauna. Aleena tana san swimming sosai, Don haka wannan wurin tasan zai zama wurin da zata fi so agidan.

Ta ja numfashi mai zurfi iska mai sanyi amma hade da kamshin kasa sannan ta juya ta koma ciki. Kafin ta kai sama tafara jin karar tafiya abayan ta. inda ta ga mataimakan da ta kira daga gidansu suna kawo kaya da akwatunanta.

Dakin ya fara daukar siffa - kayanta suna turawa zuwa master bedroom.

Room din yana da fadi da gado mai girma king size da ke tsakiyar ɗakin. girmansa kadai ya isa ya jawo hankali. Ta bude sliding door wanda ya kai ta cikin wardrobe wajen canza kaya ta ciki sannan ta kuma bude wata sliding door din ta shiga bathroom wajen wanka – Katuwar jacuzzi ce kusa window da ke kallon bayan gida yana haskaka bango. Wani sabo da ƙamshin towel sababbi suka cika da iska.

“Madam Aleena, an kawo komai nan. jerawa kadai ya rage daidai da yadda kike so,” ɗaya daga cikin ’yan aikin ta faɗa tana tsaye a bakin ƙofa. Aleena ta juya ta ganta daidai bakin kofar bathroom, ta wuce ta tana tafiya sanyi kasan yana shiga tafun kafarta.

“Idan kun gama, kuna iya komawa babban gidan,” tace dasu. sannan ta zauna a gefen gadon ta haye kafafun ta yayin da take kallon su suna bude kayan ta.

Sai shiru ya cika ɗakin – sautin kayan da ake jerawa da buɗe jakunkuna kaɗai ke tashi.

Ta fitar da numfashi mai zurfi. Tace, Wannan dakin… wannan dakin zai zama nawa.

Amma sai idanunta suka sauka a saman headboard na gadon, Ta rufe ido fushin ta yana tashi. Surukanta sun sanya wani babban frame picture ne aka rataye shi ita da Omar a asibiti lokacin da ta sa masa zoben aure. Bata san waye ya ɗauke su ba – ko mahaifinsa ne, ko mahaifiyarsa ce bata sani ba. amma ga shi nan abin mamaki.

Tana bude ido abin farko da ta gani shine, Omar ya tsaya a bakin kofa. Hannu daya ya ajiye cikin aljihunsa, dayan kuma ya rataye a gefensa. Ya sanya wando da riga, ya yi kama da mutumin kirki, amma yadda yake kallon ta bai kasance hakan ba. Kallonsa idanunsa kamar suna ƙirga sassan jikin ta yana duba ta daga kai har kafa.

Ta daga gira, sannan ta kalli rigarta. Bata sanya kayan kirki ba, t-shirt ce da gajeren wando kawai. Omar bai boye kallon sa ba, abin ya bata mamaki tace, Da gaske kallona yake haka? Wannan mara kunyan karamin dan iska…

Da ya lura da kallon dake fuskarta da sauri ya kau da idanunsa, ya dubi dakin kafin ya shiga ya tsaya agefen gadon kusa da ita.

Sai wani déjà vu ya bugi zuciyarta. Kamar ta taɓa ganin irin wannan yanayin exactly sanda ta zauna a Thorne family, Tsayuwarsa, numfashinsa, harbin kallonsa tashin hankalin iri daya. Ba tare da tunani ba, ta mike ta kuduri aniyar baza ta sake rayuwa ta irin wannan lokacin ba, wanda ya bar ta ba numfashi a karkashin nauyin kasancewarsa.

“Wannan dakin abin da nake so ne. Style din irin nawa ne - color din bango, yanayin dakin. Meyasa zaki same shi?” Ya ce, yana murmushi.

Ta kalli idanunsa fuskarta normal. “Allah sarki,” tace cikin sanyi. “Dakin nan yafi dacewa dani. Kai kuma? Ka zauna a guest room yafi maka kyau Omar. Enjoy.”

“To shikenan. Ni zanci girma na zama babban mutum,” ya ce, da dariyar tsokana a muryarsa.

Aleena ta juya idanun ta. Babban mutum? Kamar gaske.

Sai ta lura kallonsa ya wuce ta, murmushi ya bazu a fuskarsa yana kallon picture dake bango. “Wow, I don’t like this room anymore. Ta yaya zan iya bacci da wannan babban hoto haka na bikin auren mu? Ai zan ta kallonsa ne yayin da nake bacci - No, wannan ai mamaye kowane mafarkina zai yi kuma yana farauta ta.”

Ta juya zuwa hoton da ke bangon tana murmushin takaici.

“Meyasa zaka gan shi koda yaushe yayin da kake bacci? See?” Ta nuna da yatsunta, “A saman kan gadon yake. Baza ka ganshi sosai ba idan kana kwance.

Sai dai, idan tabbas, kana son ka kalle shi don ka gamsar da kanka, saboda wasu yan dalilai, Banyi murmushi acikin hoton ba, amma kai kuwa fa? Ga har dimples dinka sun fito.”

Kallonsa yayi kaifi, amma bata girgiza ba. Ta ci gaba da maida hankali. “Ina mamaki lokacin da nasa maka zoben mai kaji, tsanata ko farin ciki?”

"It was unconscious. Ko watakila anyi editing hoton. Papa yana da kirkire-kirkire irin haka,” ya mai da mata martani, kalmomin masu cizo.

Ta juya idanu cikin rashin yarda tace. “Hakane… hakane.”

Sannan, ba tare da ɓata wani lokaci ba, ta tura shi ta nufi kofa. Bata mood ko ra’ayin kara magana dashi.

Amma tabbas Omar ne fa…Sai ya bi ta.

Ta sauka kasa zuwa kitchen ta bude fridge ta zuba tomato juice a cup. Ta sha kadan kafin ta zauna a kan dining chair.

“To, akwai wasu dokoki da muke bukatan mu kafa tun da zamu zaune a karkashin rufin gida daya,” Omar ya fara, ya zauna akan chair kusa da ita hannuwansa ya ajiye a kan table stand. “Zan sa masu aiki guda biyu daga chan Thorne house suna zuwa nan kowace rana don gyara ko ina idan sun gama sai su tafi.”

Ta gyada kai, tana shan tomato juice din ta, sannan ta juyo gabansa akan chair.

Ya yi murmushi, ya jingina gaba. “Ban sa doka masu tsauri ba, dalili kuwa? Kawai saboda ni mutum ne mai kyakkyawar zuciya.”

Ta kusan jefa juice din ta afuskarsa, jin yana kiran kansa mai kyakkyawar zuciya.

Ya ci gaba, “And … muna bukatan privacy. Kin samu master bedroom don haka kiyi duk abinda kikeso dashi. Dakina kuma yana daga karshe, so hakan zai fi sauki baza mu dinga jin juna ba sosai. Kiyi minding business enki nima nayi nawa.”

Ta sauke glass cup akan table da kara sautin yasa yana kyafta ido cikin mamaki.

“Abin mamaki!” Tace, takaici a cikin muryarta.

Da alama ya yi tunanin magangarsa zata sa komai yayi daidai, amma azahiri, bai yi ba.

Idan ta ra’ayin Aleena ne, baza ma taso ta kasance a karkashin rufin gida daya dashi ba. Amma ba yanda ta iya.

“Yauwa and again,” ya ci gaba bayan dan tsayawa, “Babu taɓa kayan juna.”

“Good. Ehh, babu taɓa kayan juna… kwata-kwata,” tace, tana jingina kadan, tana kallonsa yana jan baya.

“Kuma ba don saboda kana zaune tare da ni ba, hakan yana nufin zaka ketare wani iyaka. Saboda nasan kafi kowa record mai muni akan mata. Don haka nasa doka babu taɓa abinda ya shafeni ko kadan.”

Ya daga gira, ya dube ta kafin ya hade hannuwansa. “Duk da ina son mata, sai nayi tunani sau dubu kafin in yi wani abu dake. Saboda ke ba kala ta bace, ko kusa.”

For some reason, kalmominsa sun soke ta fiye da yadda ya kamata. Ta damke hannuwanta ta ja baya.

“Oh really? hakan yasa ina tunanin baka da taste mai kyau.”

Ya bude bakinsa ya amsa, amma ta katse shi.

“Ina nufin…” “Ko kusa da yanayi na? Idan hakane ashe basu kai ni kyau ba.. Omar. Ka kalle ni…”

Ta nuna fuskarta da yatsa. “Wannan? Ka ce ba taste din ka bace? Eh to, lalle kana da mummunan taste, gaskiya. Amma hakan da kyau, Saboda zai sa abubuwa su yi maka sauki. Just don’t look at me, Or…” Ta mike tana matsawa kusa, Ta tsaya kusa da shi, ta jingina ta rada a kunnensa. “Kada ka kara yin kokarin kallo na kamar yadda ka yi dazu acikin dakina, Karka dauka ban lura da shi a idanunka ba. And zai sa ka ji saukin yin bacci da daddare sanin cewa baza ka taɓa samu na ba.”

Ta ja baya, murmushin ta ya karu, amma sai ta dan yamutsa fuska da ta lura kallonsa ba a fuskarta yake ba. Yana kan kirjin ta, Yana jika lips dinsa, yadda yake kallonta yasa taji rashin kwanciyar hankali ya shige ta.

Ta kara jan baya sosai tace, wannan dan iskan bashi da kunya akan mata kwata-kwata.

Aleena tayi gyaran murya, ta nade hannuwan ta akirji ta kalle shi. Omar ya kyafta ido tare da firgita, da sauri ya kau da kallonsa. Ba tare da bata lokaci ba, ya kwace juice cup dinta ya shanye shi lokaci daya, Nan take ya shake ya tafi da gudu zuwa wajen sink, yana tari yana kokarin tofa shi.

Aleena ta daga gira, tana kallonsa yana ci gaba da wanke bakinsa da ruwa, yana amai.

“Mene ne?” Ta furta cikin rudani.

Babu wani laifi da juice dina. Tomato juice ne kawai, kuma yana mun dadi ni.

Meya same shi? Yana da kayan takaici, wallahi.

Ya juya, yana goge bakinsa da tissue, yana kallon ta. Sannan ya dauki wani juice daga fridge ya sha shi da sauri.

“Mene matsalar ka?” Ta tambaya, har yanzu cikin mamaki.

Ya ja numfashi mai zurfi, ya ajiye juice akan table. “Ba na son tomato. Meya sa ma kike shan shi? Ki jefar da shi! Na haramta shi a wannan gidan!” Ya ce da tsauri.

Fahimtar ta same ta. Tasan abu daya da baya so yanzu, Murmushin ta ya karu, tayi dariya mai karfi cike da gamsuwa, da kyar ta riƙe. Ohh, Allah, wannan shine karon farko da ta yi dariya tun da granny ta mutu, and it somehow feels... good.

Kallonsa yayi tsanani. “Da gaske nake. Zan jefar da komai dake da alaka da tomato. Bana so, Aleena!”

Ta dan daina dariya, sannan ta yi murmushi.

“Oh, Omar, Allah sarki. Ina son shi sosai. Kuma yana da kyau ga lafiyar idona. Don haka tabbas zan ajiye da yawa a fridge.

Watakila ma fiye da na yanzu.”

Ya yi tsaki, ya jingina gaba, yana kokarin tsorata ta.

“Ban damu da abin da kike so ba! Zan jefar dasu!”

Ta mayar da martani, “Ni ma ban damu da abin da kake so ba! Idan ka jefar dasu, zan sake kawo su. Again and again!”

Ya nuna ta da yatsunsa, “you are such a…-”

“What?” Ta tura yatsunsa da karfi. “Kada ka mai da wannan wani abu babba. Tomato ne kawai. Kaje ka jefar dasu.

Bari in ga sau nawa za ka jefar kafin ka gaji da gwadawa.”

Da haka, ta juya ta tafi, amma dariyarta ta karu. Ta ji dadi sosai. Zan zama babbar abokiyar tumatir daga yanzu.

Ina son ya shake, ya ji haushi, ya ci gaba da tashin hankali koyaushe - kuma ko ta yaya, abin da zai faru ke nan. Kamar wannan.

Ina bukatar in koyi abin da ya dameshi, abin da ya sa shi ya tashi.

Zan mai da rayuwarsa jahannama kafin ya iya mai da tawa, kamar yadda ya yi barazana a gidan babban Thorne.

💘AUREN ALEENA💘

Amal Musa ✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.