Complete Hausa Novels

Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel

Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx

Chapter 2 of 28

Chapter. 2️⃣ Rikin Aleena Da Omar 🔥💢 ⚡️

A ganina dai, da akwai wata kyauta da za a ware masa:

"Mai cike da isa, wanda ya fi kowa isasshe da raini a Turkey."

Da za a ba da irin wannan lambar yabo... babu wanda zai iya karbe masa ita.

Kuma waɗanda yake jan hankalinsu kuwa? Ba matan da za ka kira na yau da kullum ba ne. Zabin sa ya bambanta — yana da high taste babba. Mutum ne shi mai tsauri kuma baya neman yardar kowa a lamarinsa.

Yan Jaridu da kafafen watsa labarai na cike da labaran soyayyarsa; yan fim, mawaka, shahararrun jarumai, da fitattun mata masu mukamai. kuma ko wacce tafi ta baya shegen kyau da jan hankali.

Ranar da na taɓo maganar sabon kwangilar nan a gaban kakata, fatan in juye takaicina. Amma da nasan haka zata mun, da ban ɗaga maganar ba. Maimakon ta tausaya min, sai kawai ta sakar min murmushin daya tattare da fahimta da tarihin daya cika zuciyarta. Wani irin murmushi ne wanda yake kama da wanda akeyi idan ana tuno abubuwan da suka faru shekaru da dama da suka wuce.

“Tabbas, ya tsaya. Wannan yaron fa haziki ne,” in ji kakata cikin murya mai laushi, kamar wacce ke magana da zuciyarta. Kin sani kuwa, Aleena? Tarihin danginmu da na dangin su ya tsufa sosai, kamar zaren da aka saka cikin zane. Dukkan shawarwari da nake yi da dangin su, suna ɗauke da nauyin tarihin nan. Kakansa da kakanki abokai ne na jini. Sun gina kamfanoninsu tare a shekarun baya, kuma har zuwa mutuwarsu, ba su rabu ba.”

Ta juyo gareni, tana kallon yadda zuciyata ta cika da mamaki. “Amma har yanzu, ban gane meyasa bakya son wannan yaron ba. Yana da kirki sosai. Tun lokacin da kika tafi U.S., Amurka, kullum sai ya zo ya duba ni. Wannan kuwa bayan dawowarsa ne daga karatu.”

Na yi shiru, ba wai saboda wannan tarihin dake tsakanin danginmu ya bani mamaki ba. a’a — abinda ya bani mamaki shi ne cewa Omar Thorne yana yawan ziyartar kakata ne a lokacin dana ƙetare bana kasar. kuma babu wanda ya gaya min.

Dana tambaye ta dalili da kuma ta yadda hakan ta dinga faruwa. Amma sai murmushinta ya sake faɗaɗawa, Wani irin murmushi ne dake nuna sha’awa da jin daɗin tunani, kamar wacce wani sahirin ɗan shaidan ya riga yayi rinjaya akanta. kamar ta manta da abubuwan dana gaya mata game da shi.

“Ba shi da kakanni yanzu, Ya gaya min cewa iyayensa sun ce mu Khans Electronics ne kadai amintattun su. Kuma gaskia ya taimaka min sosai wajen rage kewar ki. Yaro mai kirki ne.”

Kirki? Wannan kalmar bata dace da Omar ba. Saboda yafi kowa nisa da wannan kalma. Sai dai kawae na danne zuciyata — Na san daidai, kar na shiga gardama da kakata game da shi, saboda da zarar ta fara jawabi, sai ta kawo na rahama da karamci. Ni kuma ba zan iya murmushi ba domin karya game da Omar.

Da zarar na yi haka, za ta shiga wa’azin alheri da jin ƙai da tausayi. Amma game da Omar Thorne, babu wata ’yar murmushi da zan iya kwaikwayawa.

Kafin na sauke numfashi, sai ta ƙara kallona ta ce da murya mai cike da hikima:

“Aleena, ki yarda da ni. Wannan yaron shine ainihin abin da Khan Electronics ke bukata. Idan har kina son wannan sauyin kasuwanci yayi nasara, kada ki bar kamfaninsa. Kakan ki zai yi bakin ciki idan kika yanke wannan zumunci. No matter what, ki yarda dasu saboda suma sun yarda damu. Ki tambaye shi dalilin da yasa ya tsaya. Watakila zai fada miki cewa iyayensa sun bashi irin wannan shawarar da nake baki yanzu.”

Wannan dangantakar dangi da dangi tamkar albarka ce a gefe guda, amma a wani gefen kuwa, kamar sarƙa ce wacce na kasa iya yankewa duk yadda nayi ƙoƙarin na balle ta.

*****

Yau sati ɗaya kenan da tattaunawar da muka yi da kakata—zancen da har yanzu bai bar zuciyata ba.

Ba tare da sani ba, na tambayi Omar a lokacin taronmu na gaba bayan sabuwar kwangilar da aka sanya hannu. A zahiri, so nake in tabbatar wa kaina cewa kakata ta yi kuskure—kuma abinda take tunani game da Omar ba gaskiya ba ne. A ganina, dalilin da yasa ya tsaya tare da mu bai wuce kasuwanci ba.

"Ina son sani, Omar. na ce cikin wani salo mai kaifin jin zafi, me yasa ka yanke shawarar cigaba bayan irin wannan sauyi da aka yi? Shin saboda kasuwanci ne kawai? Ko kuwa wata tsohuwar al’ada ce ta kamaka da ba za ka iya saki ba?”

Sai ya saki wani irin murmushi—murmushin ba’a da rainin hankali, wanda ya haɗa fariyar zuciya da girmankai. Irin murmushin da zai ruɗar da kowa, amma a wurina, sai ya ƙara hura bacin raina.

“Na gaji da yawan neman sabbin masu kaya,” ya amsa cikin natsuwa kamar yana magana da iska. Ina bukatar in mai da hankali kan wasu fannonin kasuwanci na. Thorne Comm yana buƙatar ci gaba, bayan haka. sharuɗɗanki? sun fi komai sauƙi—kamar yadda mahaifiyata ke tambayata in dafa mata shayin dare kafin ta kwanta. To me zai sa naki amincewa? And maybe,” ya ƙara da wani murmushi mai kaifi, “I’m being generous. Da kuma taimakon ki daga halakar da zaki jefa Khan Electronics da irin shawarwarin banza kamar wannan.”

Omar ya miƙe tsaye a hankali, ya gyara rigar suit ɗinsa, ya zura hannayensa cikin aljihunsa, sannan ya ɗan lumshe ido yana ɗaga gira kamar wanda ya gama nasara. “You should be grateful for that, Aleena.” ya fada da wata murya mai cike da izza. Don’t question my generosity again. ba abu ne da nake yawan yi ba. Take your lesson from this.

Haƙorana sun matse da ƙarfi, har sai da na ji kamar za su fashe saboda ɓacin ran da ya turnuke zuciyata.

Leila—mataimakiyata a matsayin Vice CEO—ta lura da fushina. Dan haka cikin basira da sauri tasa hannu a bayana, kamar tana ƙoƙarin saukar da hucin zuciyata kafin in aikata wani abu da zanyi nadama a kai… kamar in fizge kaina da karfin tsiya in ɗaura masa mari.

Bayan wannan taron, na ɗauki alkawari mai tsanani: Bazan sake yin hulɗa da shi ba har abada. Na kiyaye mu'amalar mu ba komai a zahiri ba. Duk wani abu da ya shafi Thorne Comm na mika shi ga Leila, mataimakiyar ta Vice CEO, ko Mariam, sakatariya ta.

Kwangilar nan mun sanya hannu a kai shekaru huɗu da suka gabata. Kuma a tsawon waɗancan shekarun, na samu salama—na samu damar guje masa kai tsaye. Wannan ya zama mafita ga lokacin rayuwata da kuma lafiyar tunanina.

Amma duk da haka, ko a lokacin da ban kusa dashi Omar sai da ya sami hanyoyin da zai yi mini ba'a, da waɗansu kalmomin zolaya masu kaifi da yake tura wa kai tsaye ko ta hanyar wasu, kuma ko ta yaya suke komawa gare ni. Abin da yafi ɗaga min hankali shi ne: a wasu fannoni… muna kama. Dukkanmu mun kasance masu kishin aiki, masu azama, da rashin sassauci. Amma bambanci guda daya ne: ni ina gina gada… shi kuwa yana cinna musu wuta yana kallon yadda suke ruftawa.

Yanzu ga shi nan—ni da shi—fuska da fuska muka fuskanci juna a cikin wani taron gaggawa da Thorne Comm ta kira. Na makale a taron da na kasa tserewa. Mutumin da ya san ainihin yadda ake tura kowane ɗayan maɓallina. Thorne Comm ya kira taron gaggawa. Kuma ban shirya ba—wallahi ban shirya ba kwata-kwata. Da na sani, da na sha coffee mai ƙarfi ko na rike ƙwallon tausa don in rage hawan zuciya.

Amma a maimakon haka, sai kawai na zauna, haƙorana na matse, muƙamuƙi a damke hannuwana na haɗe a jikin table, ina ƙoƙarin rike kaina, yayin da yake gabatar da buƙatunsa cikin irin murmushin nan nasa na rainin hankali, kamar yana jin dadin ɗaure ni da kalmomi.

“Ina so Khan Electronics su kammala wannan aikin cikin wata biyu,” inji Omar, Ya ce, yana jingina da kujerarsa kamar ya mallaki dakin. Sabuwar "T-Phone Gen 6, yanzu tana mataki na karshen samfurin, dole ne ta karbi kayan aikin ba tare da bata lokaci ba. An tsara ƙaddamar da ita cikin watanni biyar daga yanzu, a cikin October, kuma bazan yarda da gaggawa ko gyara mara inganci ba. Dole ne komai ya kasance cikakke kafin ta kai ga hannun jama’a. No mistakes."

Muryarsa na kwance, tana diga tare da tsayuwar daka wanda ke tunawa kowa da kowa a dakin ainahin wanene shi da yadda yake tunani na.

Na sauke numfashi a hankali, sannan na daidaita kallona kan takardun dake gabana.

Watanni biyu kacal ga irin wannan aiki mai sarkakiya? bai dace ba kuma bai da ma’ana kwata-kwata. Shi kansa ya sani, kuma bazan bar shi ya gane cewa abin ya dame ni ba.

“Mr. Omar,” na fara da murya mai natsuwa amma mai ɗauke da ɗan ƙunci, hannuwana na riƙe da gefen table kamar zan narke. "Shirya wani abu makamancin haka a cikin watanni biyu, musamman na kashin farko na raka'a 60,000. Wannan ai hauka ne.”

Daga gefen idona, na hangi Mariam tana miƙo min wani file ba tare da ta ce uffan ba. Na buɗe shi da gaggawa, duk motsina na nuna takaici.

“Iyakar abin da injinanmu za su iya a kullum bai wuce raka’a 300 ba. Idan muka matsa sosai, zai ɗauki watanni bakwai kafin mu iya kaiwa wannan adadi da ake buƙata.”

A gabana, Omar ya dafa habarsa da yatsa, yana kallonmu da wata murmusawa ta rainin hankali, amma idanunsa ba su yi dariya ba—suna cike da ƙiyayya mai sanyi.

“Hmm… interesting," ya ce, muryarsa a hankali, mai tsawo, mai izgili. “But tell me… how is that my problem?”

Na ɗauki wani dogon numfashi, yayin da yatsun hannuna ke shiga cikin tafin hannu na saboda tsananin ɗaga zuciya. A zuciyata, hoton dake fuskata shine na ja hannunsa in buga shi a gefe, don kawai ya daina wannan murmushin raini hankalin.

“Ku ne masu kaya,” yaci gaba, muryarsa na daidaita kamar karfe mai kaifi, kowanne kalma na fantsama da daci. “Ni kuwa abokin ciniki ne. Zan fadi abinda nake so, ku kuma aikinku ne ku kawo shi.

No excuses."

Ya mike a hankali, cikin natsuwa da kuzari, ya ajiye tafin hannayensa a kan table, sannan ya matso gaba, yana kallona da idanu kamar yana karanta zuciyata. “Remember,” ya fara da muryarsa mai ƙayatarwa amma cike da ji da kai. “wannan zai nuna ko zaki iya gudanar da aiki da inganci a lokacin wahala, ko kuma Idan Khan Electronics ba wani abu ba ne face ƙungiyar marasa nasara da suka dade a cikin kwanciyar hankali da makalewa a yankin su masu aminci ne."

Idanunsa suka cakuɗa da nawa tamkar suna kira da cewa, ‘Ki amsa, idan kina da ƙarfin zuciya.’

Sai na fashe. Kujerar da nake zaune ta tashi da ƙarar da ta cika ɗakin yayin da na miƙe tsaye da karfi, na bugi table da tafin hannu na cikin fushi.

“Kai! Omar Thorne!” Na hura numfashi cikin tsawa, “Ka shigo nan haka kawai, da wasu buƙatu da ya kamata ace ka kawo tun watanni da suka gabata, kuma yanzu kana kokarin dora mana laifin rashin hangen nesa?” Na nuna shi da yatsa, murya ta na karuwa. “Wannan ba ƙarancin ƙwazo bane, Omar wannan wawancinka ne. postpone the T-phone launch. Shine kadai za a iya samun mafita. Shi ne mafita ɗaya mai ma’ana.”

Leila da Mariam, wadanda ke zaune a gefena, suka sa hannu suna ƙoƙarin Jana baya. Amma ni ko motsinsu ban ma lura da shi ba.

Omar bai motsa ba. Murmushinsa ya faɗaɗa, yana kallona da wata iriyar rainin hankali kamar ni ƙwari ce a ƙarƙashin gilas.

"So emotional," yace cikin dariyar da bata kai ga idonsa ba. “Ki duba fa yadda kika rikice, A matsayinki na CEO, hakan abin takaici ne sosai.”

Ya miƙe tsaye gaba ɗaya, yana sanya hannunsa cikin aljihun rigarsa, muryarsa ta sauya—ta ƙara daci da sanyi. “Idan ba za ki iya da wannan kalubalen ba, watakila lokaci ya yi da za mu sake nazarin yarjejeniyar haɗin gwiwarmu.”

Kalamansa suka shiga zuciyata kamar mari mai ƙarfi. Bafarin numfashina ya rikice, na kasa daidaita shi, yayin da ya ɗan karkatar da kansa, muryarsa ta ƙara girma da sanyi lokaci daya.

“T-phone muhimmiyar na’ura ce wadda ba za a iya jinkirta fitarta ba,” ya furta da idanu masu kaifi. “Jinkiri zai jawo tambayoyi daga jama’a, shakku kan ingancin samfurin, da yawan maganganun gazawa. Wannan ba abin da za a amince da shi bane—ba daga gare ni, ba daga kamfanin Thorne Comm, kuma ba daga duniya ba.”

Sai ya ƙara da murmusawa mai kaifi da saƙo a cikinta.

“Watakila irin wannan tsari mai zurfi da dogon tunani ba irin naki ba ne. Ke dai baki da hangen nesa… kamar ni.”

Na matse yatsuna a gefen jikina, fuskata na cike da ɓacin rai. Hannun Leila ya taɓa hannuna, kamar tana ƙoƙarin janye ni daga halin da nake ciki, amma na gurgunta hannu na daga nata, na wuce, na nufi Omar da ƙarfi.

“Aleena, ki tsaya,” Leila ta furta cikin muryar da ke cike da tsoro da damuwa.

Amma ban tsaya ba. Bazan iya ba.

Omar bai motsa ko ɗan kwakkwara ba yayin da na ƙarasa kusa da shi. Fuskar sa cike take da nutsuwa mai haɗe da lissafi, gefen leɓensa yana ɗan motsawa kamar yana kalubalantar ni da cewa: “Zo ki rasa iko.”

Na tsaya inci kadan daga kusa da shi, muryata a kasa, mai dafi. “Bari in fayyace maka wani abu, Omar. Kai ne wanda baka yi nazari da hankali ba.

Ka yi hasashe marar tushe, kuma yanzu kana ƙoƙarin dora mana laifi?

Ka daina raina mana hankali!”

Murmushin sa bai gushe ba, sai ma ya faɗaɗa. Sai ya ɗan matso gaba, ƙamshin turarensa ya mamaye sararin tsakaninmu – mai nauyi, mai shakewa.

“Bani bane nayi kuskure, Aleena,” Yace muryarsa a sanyaye babu sauri. “Sassan da kuka kawo ne suka jawo matsala da samfurin gwaji.”

Haƙorana na matse su kamar za su fashe. Kalaman da nake shirin fitarwa sun makale a ƙirjina. Kafin na samu damar magana, ya miko hannu, yatsansa yana goga layin kuncina kamar yana ƙoƙarin nuna iko. Hankalina ya kasance nan da nan, Na ja da baya cikin hanzari.

“Gyara kayan aikin ku,” ya ci gaba, muryarsa ta ƙara sauka da sanyi mai sa zuciya bugawa, idanunsa na kallo kai tsaye cikin nawa kamar zai hango abin da ke cikin zuciyata. “Mai da fushinki kan ma’aikatan ki. Watakila sai su san yadda ake aiki daidai a wannan karon.” Ya juyar da kansa kadan, bakinsa ya matso daidai da kunnena, yana furta kalmomin da suka busa dumin numfashinsa cikin fatar wuyana. “Kin guji ganina tsawon shekaru huɗu. Smart choice, Saboda duk lokacin da kika haɗu da ni, abinda kika iya yi shine ɓata min lokacina mai daraja.”

Yaja da baya, hannunsa ya zube a gefensa, ya juya ya nufi ƙofar fita da niyyar barin dakin taron. “Wata biyu kawai zan baki,” ya fada, yana juyawa ba tare da kallona kai tsaye ba. “Idan kika kasa, to ki fara shirin neman sabon abokin hulɗa wanda zai maye gurbin Thorne Comm. Ina tunanin rasamu zai girgiza raunin da Khan Electronics ke ciki. Hmm… Ina mamakin ko ‘Masoyiyar Turkey’ zata iya jure hakan, ko kuwa kawai zata zauna ta fashe da kuka kamar yarinya.”

Ya tsaya, ya juyo ya sake kallona, murmushinsa na gefe mai sanyi kamar reza.

“Jami’ar Yale ta yi kuskure da ta baki lambar yabo. Da alama hikima bata cikin kayan aikinki.”

Ya kai ga ƙofar dakin, ya tura ya buɗe ta. iska ta sauya kamar ya riga ya ɗauki nasara. Amma kafin ya ɗaga ƙafa ya fice,—na riga na kai, na ruƙo ƙofar da karfi, na banko ta da ƙarfi. Saƙon karar ya daki bangon ɗakin taron. Sai na juyo, zuciyata na tafarfasa, na ture shi da hannu kamar wani abu da ya hana numfashi.

Idanunsa suka faɗa da mamaki, amma bai ɗauki lokaci ba ya maido da murmushinsa na raini da jaraba.

“Ka kai waɗancan maganganun inda suka dace, Omar — ƙasan mararka,” na furta da murya mai kaifi da haɗarin gaske. Tareda hura numfashi cikin fushi. “Idan ka qagu da a tsinke kwangilar da har yanzu tana da shekaru uku a gaba to babu matsala. Ka shirya. Let's have that meeting."

Haƙoransa suka matse juna, fuskar sa ta nuna haushinsa. Amma ban tsaya ba. Ban ji tsoron kowa.

"But let me tell you this: “Ka sani, girman kai naka zai jawo maka bala’i. Koda ka yanke hulɗa damu, dole ne sai ka jinkirta fitar da sabuwar T-phone ɗin, yayin da kake ta faman neman wanda zai maye gurbinmu. Kuma a lokacin idan hakan ya faru, zan yi dariya — koda zan sake gina komai daga tushe — because at least I'll be free of you."

Na ja da baya, na sake tura ƙofar da karfi. "Now get out, Kuma ka tafi da girman kan ka gaba ɗaya.” Na zuba masa ido, ina nuna masa ƙofar da idanuwa. Ya girgiza kai, yana murmushin nan nasa na raini yana shafa goshi da yatsunsa.

“Kin tabbata wannan hanya ce da kike so ki bi? Ya tambaya cikin wata murya mai sanyi da lallashi amma tana ɗauke da keta da jaraba. “Baki da niyyar fahimtar buƙatata ko? Ba zaki iya la’akari da neman hanyar da za ta ƙara yawan samar da kayan ba? Koda sau ɗaya ki gwada cika buƙatata?” Idanunsa na walƙiya da keta, kamar yana jiran in kuskure ne. "Tell me, Aleena,” ya ce, yana taƙaita tazara da ni. waye mai girman kai a nan?

Amma dai to. Mu gani. Mu ga ko wannan ne ƙarshen haɗin kai da ke tsakanin danginmu. Let's see who suffers more. You or me."

Daga nan, ya zaro baƙin gilashinsa daga aljihun rigarsa, ya saka su a fuskarsa, ya saki murmushi na ƙarshe – sannan ya fice daga ƙofar da jin daɗin nasara a tattare da duk motsinsa.

*****

“Lallai wannan bala’in ya kai bango,” na furta da ƙunci, yayin da na faɗa cikin kujera kamar wacce aka tsinka da gajiya. Da wuya na iya ɗaga kafada saboda irin ɗumbin damuwar dana tara, wadda ta fara tasiri har cikin ƙasusuwa na.

A gaban teburin, Leila da Mariam suka zauna, fuskokinsu cike da damuwa, kamar yadda layukan damuwa suka bayyana sarai a kuncinsu.

“Aleena,” Leila ta fara da wata murya mai nutsuwa amma mai ƙarfi, “dole ne ki sassauta wannan rikicin. Thorne Comm shi ne babban abokin hulɗarmu. Sauran kamfanonin da muke tare da su? Zasu iya rabuwa da mu a cikin ƙiftawar ido ba tare da wani tunani ba.”

Na jingina da kujera, na dafe goshi da yatsuna, ina ƙoƙarin danne sautin muryarsa dake karaɗe kwakwalwata tun daga fitarsa.

A gefe guda na hango Mariam na yin kallon fahimta da Leila, kafin ta zagayo zuwa bayana. Ta sanya hannunta a hankali a kafaɗuna, tana latsa su da tausasawa kamar yadda za ta shawo kan ciki mai ɗaci.

“Ki saurara, Aleena,” ta fara cikin natsuwa da laushi, “na fahimce ki. Aiki da Ya Omar ba sauki ba ne, amma cikin shekaru hudu da na riƙa zuwa taruka da shi a madadinki, ba ya yin haka. Abin da nake gani yanzu tamkar na musamman ne gare ki. Kuma gaskiya, yau kin fada tarkonsa da ƙafa biyu — kin bari ya ɗaure ki cikin damuwa fiye da kima.”

Na saki numfashi a hankali, mai zurfi, wanda nake fatan zai hana ni zubar da ƙara kamar wacce za ta tarwatse da ihu.

"I can't helped it," na furta a hankali, ina zare hannayenta daga kafaɗuna. Mariam ta matsa gaba, ta jingina da gefen table, fuskarta na nuna tausayawa, amma kalamanta na daure kai.

“Bana son jin kina kiransa ‘Ya Omar,’” na bige da faɗa, muryata ta fito da ƙarfi fiye da yadda nake nufi.

“Kin san yadda nake jin tsanar sa kuwa? Wallahi Omar bai cancanci ko ɗigon girmamawa ba. Ba daga gare ni ba, ba daga kowa ba!”

Mariam ta daga hannayenta alamar tuba, tana dariyar sanyi, tana komawa kujerarta da natsuwa.

"Alright,ta ce da sauƙin murya, “amma har yanzu zan ci gaba da kiran sa Ya Omar. Yana bani daɗi hakan. Kuma gaskiya? Zai iya yanke min kai idan ban kira shi da haka ba.”

Leila ta yi dariya kaɗan, tana girgiza kai da annuri.

"He is older than you, Aleena," ta faɗa da murmushi mai nau’in zolaya. “Kada ki bari ƙiyayyarki gare shi ta cinye Mariam da batada laifi.”

Na ɗan runtse ido na, sannan na lumshe su da gajiya, na saki wani ƙaramin numfashi cike da kunci. Na jingina da kujerar bayana kamar wadda ta gaji da rayuwa.

“Ta yaya kuke sa ran za mu iya kera raka’a dubu sittin cikin wata biyu?

Injinanmu, ma’aikatanmu—ba su da ƙarfi fiye da raka’a 300 a rana.

Wannan ba zai taɓa yiwuwa ba.”

💘AUREN ALEENA💘

Amal Musa ✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.