Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel
Reading file: Auren Aleena Book One Complete Hausa Novel.docx
Chapter 16 of 28
Chapter 1ï¸âƒ£6ï¸âƒ£: Dokokinta 👑💅🧕 Gidana 💼ðŸ
SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃
Kwanaki goma kenan da Omar ya tare a sabon gidan nan. Gidan kuwa? Gida ne mai kyau sosai – na zamani, mai lafiyayyen tsari, da kayan ciki da suka nuna kuɗi da kima. Amma agaskiya? Da ba don iyayensa ne suka bashi wannan gida a matsayin kyauta saboda auren sa da Aleena ba da tuni ya cigaba da zama cikin penthouse dinsa inda babu mai tsoma masa baki cikin rayuwar sa.
Omar yana zaune ne a living room yana breakfast dinsa – egg da toast bread da coffee – amma zuciyarsa na can, cike da tunani iri-iri da suka cika shi kamar ruwan sama. Penthouse ɗinsa kuwa, gidan mulkin sa ne – duniyarsa. Wurin da yake kai mata ba tare da kowa ya dame shi ba, kuma yana more rayuwarsa ta yadda yakeso – babu sharadi, babu dokoki. Duk inda burinsa ya kai shi, can ne. Har ma yana jin wani salo na daban: samun 'yancin yin sex a ko ina, ba a bedroom kadai ba. Wannan yanayin yana bashi dadi wanda ba zai iya bayani da baki ba.
Amma a nan? Cikin wannan gidan da Aleena ke ciki? Bai da tabbacin ko zai iya cigaba da zama da walwala irin ta penthouse. Kuma ba wai don yana jin tsoron Aleena Khan bane. Wannan fa Omar ne. Babu mace da zata bashi tsoro. Kuma wannan ba matsala bace wajen shi, Idan har ta damu da abinda yake zai iya ce mata kawai ta zo su yi tare – ya karasa da wata dariyar sharri a fuskarsa. "Damn," ya furta a hankali yana cigaba da dariya da mamaki shima game da abinda yake tunani. Me yasa nake haka? Ina behaving kamar dan iska? Omar yace yana girgiza kai da dariya.
Amma, cikin zuciyarsa wani murya ya sake tashi yana cewa: "Amma duk da haka... bazan yi complain ba idan har zata amince dani. Because, agaskiya—"
Kwanaki kaÉ—an na zaman mu, duk da bama magana, amma fah na lura: Aleena tana da mugun sexy body. Sosai. Irin wanda nake son mace da....!!"
No, wait. No, no, no—
Ya girgiza kansa da sauri, yana kokarin korar tunanin daga kwakwalwarsa.
A'a, a'a, Omar! Kar ka shiga can! Don't even go there, Ka tuna, You hate her, and she hates you too.
But what if... idan kuma... watarana tace zata bar Emir ya zo gidan nan fa? Omar Ya yamutsa fuska yana girgiza kansa da ƙarfi, tunanin hakan ma yana sa masa ciwon kai. Wani bacin rai ya fara taso masa yana neman rufe shi gaba ɗaya, kuma ya kasa cire wannan tunanin daga zuciyarsa. Yayi shiru, sai yace; "Na san ni mai son mata ne, amma ganin Emir ya zo gidan nan, wajen Aleena? Wannan abu ne wanda bazan taba dauka ko yarda dashi ba."
Ya dauki coffee dinsa ya sha kadan, dacin caffeine ya dawo dashi cikin hayyacinsa. Idanunsa suka zaga cikin falon kamar yana neman nutsuwa.
A penthouse dinsa, master bedroom É—insa yana da girma, da kyau, da komai. Amma yanzu anan? Aleena ta kwace master bedroom ta barshi ya kare da guest room. Ba yanda zaiyi haka yasa aka gyara masa guest room zuwa cikin taste dinsa don yaso room din.
Omar kuwa? Ya bata room din ne kawai amma ba wai don yayi mata kirki bane – a'a – ya gaji ne. Gajiya da rigima. Gajiya da taurin kai da girman kanta. Amma kam bawai kirki bane yasa kawai guje duk wani fada da ita ne, "Ya bari ne kawai don ya huta."
Amma gaskiya? Zuciyarsa ta ci gaba da tafasa.
"Ta yaya na bari Aleena ta dauki komai? Ta karbi komai mai kyau a gidan nan? Me yasa ta ke ganin kamar komai nata ne kawai?"
Omar ya jingina a kujera, ya matse toast bread É—insa yana ci kamar wanda ke haÉ—iye fushi. Zama karkashin rufin gida daya da Aleena? Wani babban challenge ne.
Omar yayi shiru, sannan ya sauke idanunsa yana kallon fuskarsa da ke haskakawa a saman marble ɗin dining table. Sai yace, "Ban so in ci gaba da faɗa da ita, musamman bayan ta ce zata koma gidan su. And I didn't care ko ta faɗa wa Emir bata ra'ayina, ko kuma cewa ba za ta bari in taɓa ta ba — ban damu ba. Ko kaɗan."
Hell, I didn't care idan ma ta ci gaba da son Emir a zuciyarta. Wannan ba matsalata bace.
Omar ya kara damke cup ɗin yana kallon coffee kamar wanda yayi masa laifi... abinda ya fi bata min rai shi ne — ta yaya zata yi tunanin cewa zata koma gidan su kawai ta ci gaba da rayuwa da Emir — kamar wannan aure ba shi da wani mahimmanci?
Inda iyayena sun ji hakan fah, tabbas da an samu matsala. Kuma wannan ba wai yarinta bane. Kawai tsantsar rashin girmama ni ne, da kuma raina auren da aka É—aura mana.
Taya zata zama so careless da abu mai mahimmanci haka? Aleena bata ganin cikakken hoton abin. Don haka lallai dole ta fahimta cewa ni mijin ta ne. Kuma ta karɓi gaskiyar da take gudu.
Omar ya sauke numfashi mai nauyi, ya ajiye cup ɗin, ya ɗauki wayarsa. Auren da muka yi ba lallai bane duniya ta sani, but still, this marriage? It was real. And sealed. Kuma an ɗaura shi agaban kakarta da iyayena — kuma hakan ya sa su farin ciki matuƙa da auren nan. Auren da Aleena ke kokarin wawurtarwa kamar wanda ba shi da asali.
Uh-uh. No chance.
Omar ya murza idonsa, bacin rai ya taso a zuciyarsa da wannan tunanin. Baya son iyayensa su san dangantakar Aleena da Emir, musamman saboda yasan Aleena tana matuƙar son Emir. And abinda kawai ya iya shine kwantarwa da iyayensa hankali kan cewar friends ne kawai. Ko da yake wani ƙaramin ɓangare a zuciyarsa yana samun jin dadi da wani irin twisted gamsuwa Idan ya ga Aleena ta shiga cikin problem. Amma sai dai gaskiya baya son yasa iyayensa cikin stress ko damuwa.
Amma sai gashi, Papa da Mommy suna matuƙar son Aleena... kuma abin takaici, suna matuƙar son Emir ma.
Omar kuma fa?
Shi kadai ne dansu, A makale a tsakiya.
Omar ya dubi agogonsa – 08:47 a.m. na safe.
Karamin lokaci ya rage kafin ya fita, sai kawai ya hau kan social media yana scrolling ahankali. Wani video na wasu 'yan mata suna rawa ya ja hankalinsa. Daya daga cikinsu ta fi fice - motsin jikinta yana tafiya a hankali, ƙirjinta yana girgiza da kowanne step, jikinta cike da ƙiba mai kyan gani. Hakan yasa ya saki murmushi. A ko yaushe Omar yana son yaga yan mata masu kyau suna rawa.
Gosh, ina kewar jin daɗi. Omar ya fitar akarkashin numfashin sa. Me ya sa na jima banyi wani nishadi bane ba? Ehh, Haka fah...Saboda na shagala da baƙin ciki, da aiki da T-Phone. Kuma gaskiya, ban ma san dalilin da yasa ban ware lokaci na yin annushuwa ba. Watakila komai ya min yawa ne a cikin ƙaramin lokaci da ya wuce.
Dole ne in fara tunanin yadda zan dawo da jin daÉ—i a rayuwata.
Kafin Omar ya gama zancen sa da tunanin hakan, sai ga notification ya shigo a wayarsa – daga wurin Ali.
Ali: "Kemal da ni mun riga mun fito. Zamu kiraka daga baya."
Ali da Kemal suna kan hanyarsu zuwa Antalya domin wani business deal. Nan take Omar cikin sauri yayi musu typing reply, sannan ya koma duba kan feed din kan wayarsa.
Ya dago kansa daga wayarsa lokacin da yaji ƙarar tafiya daga saman bene.
Aleena ke saukowa, tuni ta shirya cikin kayan fita na yau — she was dressed like a modern Turkish elite. Riga ce doguwa mai laushi sosai, mai sheki da kamala, silk navy blue wacce ta zauna jikinta kamar an zana, ta rufe kanta da karamin veil mai launin sky blue da ta lullube fuskar ta da light makeup. Tsayinta, da yanda take tafiya da nutsuwa, sun isar da duk wani bayani game da ita. Idanunta suka hadu dana Omar na dan wani lokaci kadan, amma nan da nan ta mayar da hankalinta kan wayarta, tana manna ta a kunnen ta.
"...No need, Sweetheart. Zan wuce office yanzu. Ina da meeting da wuri yau," ta fada ba tare da ta sake kallon Omar ba. tana ci gaba da tafiya har ta fice daga cikin gidan.
"Uh-uh. What about lunch mu ci tare anjima?..." Muryarta ta dishashe yayin da ta bace gaba É—aya.
Omar ya sauke numfashi yana juya idonsa. Ya mayar da hankalinsa kan wayar sa. Tabbas, da saurayinta take waya.
Hakan bai bashi mamaki ba... Saboda kwata kwata basa magana. Suna sharing gida daya amma kasancewar Aleena acikin gidan kamar wata fatalwa ce.
Amma duk da haka—duk da wannan nisan da ke tsakanin su—Aleena sai da ta nemo hanyoyin da za ta dinga bata masa rai.
Tumatir.
Tun da ta gano cewa Omar baya son tumatir ta mayar da fridge din gidan nan wata ma'adanar kayayyakin da suka danganci tumatir.
Kowane lokaci da ya bude fridge din, sai ya ji kamar ya tsinci kansa a cikin wani irin "personal hell" tasa. Tumaturan — jajaye, sun nuna,
su ne ke ci gaba da tuna mishi dalilin da yasa yake jin tsanar wacce somehow ke da ikon sa masa damuwa da karamin abu kadai.
Don haka, domin kauce wa rigima da kuma neman dawowa da nuna iko, Omar ya siyo sabon fridge nasa.
Ya tabbata ya faÉ—a mata clearly cewan; "Kada ki taba min wannan fridge. Wannan nawa ne. Ni kaÉ—ai. Kin fahimta?"
Amma Aleena sai kawai ta daga kafada kamar ba komai. Kamar ta ci nasara. Sannan maimakon ta hakura, sai ta nemo sabon strategy — ta fara hada tomato juice, kullum da safe tana kunna blender da ƙarfi, yayinda Omar yake zaune a dining table yana kokarin cin breakfast dinsa cikin lafiya.
Kamshin tumatir din yana mamaye falon da cikin gidan gaba daya, yana ratsawa har cikin zuciyarsa. Sai yaji kamar zai yi Amai, Sai dai kawai ya tashi ya fice zuwa office koda lokacin fitan sa baiyi ba. Tabbas Aleena tasan yanda zata dinga tusa masa bacin rai cikin zuciyarsa. — She is so childish. Omar kuwa bashi da lokacin wasan yaran. Shiyasa yau ya zabi yaci breakfast dinsa a living room cikin nutsuwa.
Amma yau daban take. Bata yi wani abu da ya shafi tumatir ba. Balle ta kunna blender ba, babu wani tsokana ko kokarin bata masa rai. Kallo daya ne kawai ya hada su sannan ta fice daga gidan shiru kamar ba ita ba.
Good, ya faÉ—a cikin zuciyarsa.
A day without tomatoes? That's all I needed.
Sai dai duk da haka, ya lura da abu daya. Omar yace a ƙarƙashin numfashin sa, ehh tabbas nima fah mutum ne... after all. Kuma muna rayuwa a ƙarƙashin rufin gida ɗaya.
Ina da tabbacin Aleena ta dawo ne da safe yau. Da alama bata kwana a gidan nan ba. Watakila ta kwana wajen su Leila, ko kuma gidan su. Saboda gaskiya? Bata cika kwana nan ba.
Watakila sau É—aya ko sau biyu kacal.
Wani lokaci sai ta dawo daga office da yamma, amma kafin dare yayi — ta kara ficewa. Kamar yau. Ta dawo da safe, around 7am, ni kuwa zuwa lokacin tashi na kenan daga bacci—sanda na hango ta tana tafiya zuwa bedroom dinta, jakarta a hannu. Bata ce komai ba, nima ban tambaya ba.
Hell, I didn't want to know.
Kamar yadda na faɗa — we don't really talk to each other. Sai idan hanya ta hada mu cikin gidan ko kuma akwai abun da ya zama dole na aiki mu tattauna.
Ko kuma... lokacin nan da ya shafi tumatir.
Bamu da Line ID din juna.
Kuma bawai don ina bukata ba — because honestly, ni da Aleena ba komai bane face kamar strangers a gida ɗaya. Duk da mommy ta bani line id nata ni abun ma dariya ya bani, Idan ina bukatan magana da Aleena zanyi, Don haka naga kaman bama bukatan line id na juna. saboda gida daya muke zaune.
Maganar mu ta karshe kuwa ranar nan ce, wata rana da Aleena ta dawo daga office ta kawo maganar T-Phone Gen 6 components.
Ta ce Khan Electronics suna aiki tukuru yanzu, har suna iya kera 500 units a rana.
Ni kuma bance wani abu ba sosai. Sai nace,
"That's good. At least kuna ƙoƙari."
Na juya kawai na wuce É—akina.
Na lura da yadda hakan ya bata mata rai, saboda ta yi ajiyar zuciya mai cike da takaici.
Meyasa taji haushi?
A tunani na, I was being kind and nice. Irin na yaba mata aikin su ne. Ko kuma, tasa ran wani amsa daban ne? Ko kuma tana so in buƙaci wani abun ne?
Honestly, I didn't get it.
Na fadi hakan ne kawai saboda ina da wasu plans din.
Bayan na yanke shawarae daga launch din T-Phone Gen 6 zuwa December — kusan watanni shida masu zuwa — don sauƙaƙa musu, I had another idea.
Kuma hakan duk yana cikin hanyoyi don na taimaka musu.
Sai dai ban gaya mata ba.
Wannan plan din shima ya kasance ne bisa roƙon da Papa yayi.
Lokacin da na bayyana masa matsalolin da ke tattare da components, ya ce mu nemo wata hanya daban, kada mu dora wa Aleena nauyi.
Na amince, ba wai don ina so in kara sadaukar da komai ba, a’a — kawai saboda at the end of the day, duk wannan ba komai bane illa pure business da logic.
A ƙarshe, na umarci team ɗina su fara bincike domin nemo wani sabon manufacturer.
Wannan shine dalilin da yasa yanzu haka su Ali da Kemal ke kan hanyarsu zuwa Antalya — domin su duba wata sabuwar kamfani da muka gano wadda ke da kwarewa wajen ƙera electronic components.
Ko da yake basu kai matakin Khan Electronics ba, amma lokacin da suka aiko mana da sample, Ali ya gwada shi da prototype na T-Phone Gen 6 — kuma result ɗin ya kusa zama perfect.
Ƙananan gyare-gyare kaɗan ne kawai ake bukata.
Aƙalla, sun fi kowa kusa da buƙatuna, kuma na yarda da su har na amince su rike production.
Zan sa su kera ragowar adadin da Khan Electronics bazai iya cikawa ba.
Ta haka, za a raba sourcing ɗin components ɗin daga kamfanoni biyu —
efficient, balanced, problem solved.
Omar ya mike, ya ɗauki suit jacket dinsa, yana ƙoƙarin kawar da tunanin gidan, Aleena Khan, da duk wani nauyin da ke ransa.
Time to head out.
💘AUREN ALEENA💘
Amal Musa âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.