Trending Hausa Novels

Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Majnoon Part 1.txt

Chapter 10 of 36

Zarah ce zaune akan gado, tadafe kanta tana hawaye, edonta duk sun kumbura, tasha kukanta mai isarta,

Turo kofar d'akin nata akayi akashigo da gudu, bata d'ago kantaba ballema tasan waye yashigo, illadai taji shigowar mutum,

Yarinyace yar kemanin shekaru 10 tashigo d'akin tana murna, tafada kan gado inda zarah take, "anty zarah, kingafa abbanmu yasayimun game boy" tafada tana nunawa zarah game din,

Zarah ta d'ago edota ta kalleta tace "Feena kije nagani banason damuwa" tafada a kasale

Feena tana kallon zarah, tagane kuka take tadan bata fuska tace "anty zarah kuka kike, me akayi miki, mamace ta miki laifi ko Abby"

Zarah ta share hawaye ta tadan langawabe kanta kadan tana kallon feena "basu bane, kidai nace kije kibari anjima zamuyi magana"

"Faisal ne koh?" Feena tafada tana kallon zarah, zarah ta zare ido tana kallon feena cike da mamaki, tayadda akayi tasan faisal, saikuma ai bazatayi mamakiba domin tana yawan bata labarinshi, bata san lokacin da data girgiza mata kaiba, feena ta tsuke fuska "waishi faisal dinnan duk lokacin da kikaje gurinsa saiya sakaki kuka, ni gaskiya anty zarah kidaina zuwa gurinsa, kima rabu dash.." bata karasa maganar ba zarah ta toshe mata baki, tana girgiza mata kai a lokacin har hawaye sunzo mata ta dora kanta akan feena tana fadan "bazan iyaba feena, wlh bazan iya rabuwa dashi ba, kee bakisan MIYE SO ba, shiyasa kike fadan na rabu dashi, I lov him feena, I lov him...." takarasa maganar tana kuka,

Feena ta tausaya mata sosai. tasa hannu ta share mata hawaye sannan tace "anty zarah malamin islamiyarmu yace duk abinda mutum keso toh yakai kukansa a gurin Allah insha Allah allah zai shere masa hawaye, anty zarah mezai hana kifadawa Allah damuwarki"
Zarah tayi murmushin yake tace "ngode sister na, nagode sosai, tashi kije inason na kwanta"

feena ta mike daga kan gado tanufi hanyar fita tana tana juyo tana kallon antynta, harta fita tabar dakin, zarah takara fashewa da kuka....

**** **** **** ****
Kwanan umma biyu kenan a station tayi baki dukta kode, tasha wuya sosai,

Yanzu dai kam abba yagane ba umma bace ta sace rumaisa, domin da ace ita tasaceta data fito da ita kodan wahalar datasha,

Abba duk ya fita hayyacinsa, 'yarsa k'waya daya tilo tabata, anyi nema har an gaji, dole akaje aka bawa malamai adu'a akan sutayasu da adu'a ko Allah zaisa aganta, tafito a duk inda take ,

Abba kullum yana station idan baya station to yana gida amma kwata2 yadaina aikin komai, komai nasa yatsata cak, tashin hankali yashiga sosai, zuciyarsa cike da danasanin abinda yayiwa rumaisa,

Yauma Yana zaune a station yana tunani2

Zunbur ya mike kamar wadda aka tsigala, dasauri yafita yabar office din, yashiga motarsa, ya kunna yahau hanya gudu yake sosai, harya karasa unguwar da ya saba ganin rumaisa....

wace unguwaceee...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:44 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

49 and 50
Via *OHW*
_A love story_💝

Unguwar da majnoon yake zaune, daidai gurin daya zo yasami rumaisa ranar anan yaja birki, yana tsaya yana kallon unguwar, yana jan nunfashi,

A gefen wani gida ya hangi majnoon a rakube, yayi wani irin zama kalar tausayu..

Dasauri abba yafito daga cikin motar yanufi gurinsa, yana karasawa ya gurkusa yazauna kusa dashi edon abba sunyi ja sosai, yadube majnoon sai kuma yasaukar da kansa, yanayinsa yabashi tausayi cikn sanyi murya yace " ina rumaisa"

majnoon yayi saurin dago kansa yana kallon abba, saikuma ya mike tsaye yana kokarin barin gurin, abba yayi saurin shiga gabansa " magana nake maka ina rumaisa" majnoon ya ture abba daga gabansa yacigaba da tafiyarsa, ran abba yasoma baci kara shiga gaba majnoon ya runtumo kwalar rigarsa yadaga murya sosai yace "kai inaima magana ka kashareni, ina kakaimun rumaisata, wallahi saika fito mun da ita saboda komai yafaru da rumaisa kaine sila, abba yakara jinjiga kwalar rigar majnoon yana fadan " ina rumaisa..." yafada yana hawaye, nan take mutane suka taru a gurin suna kokarin babbare majnoon daga hannun abba, shidai majnoon uffa baiceba, sai mazurai yake da edo, abin tausayi duk ya rama,

Abba yana kuka yake fadan " karku barshi yatafi wlh 'yata yasacemun, 'yata tana wurinsa kuce masa yabani 'yata" mutane suka rirrike abba, wasu kuma wasu kuma suka rike majnoon..

daya daga cikin mutanen yace " haba Alhj yazakace mahaukace yasacemaka yarinya, meyasani waddama koshi kansa baisaniba ballema harwata 'yarka, kaidai kaje kanemi wadda yasacema 'yarka amma ba wannanba"

nan kaji mutane gurin sunce "gaskiyane wannan bazai iya sace maka 'yaba " wani matashi yana rike da majnoon yace " wannan mahaukacin yau kwanansa biyu kenan ko wasa yadainyi da yara, kullun yana rakube a gefen titi ko agefen unguwa, gaskiya wannan bashi yasace maka 'yarka ba, kaje cen kanemi wadda yasace maka 'ya"

Abba yace "wlh shine.. wannan ne " yanuna majnoon, mutane suka ce a fa bashi bane, abba kuwa yayi juyin duniya suka koki bashi gaskiya, mutane suka rikesa suka kaisa har bakin motarsa suka sakashi, sannan ya kunna motar yabar unguwar yana kuka, soyayyar 'ya da mahaifi kenan....

**** *** *****
Faisal kuwa duk ya rame abincima kadan yakeci bai wuce a yuni yaci abinci saudayaba, koshi dandai momy na matsa masa ne, ammashi kwata kwata bayajin dadin abinci,

Faisal yana zaune a falo yana kallo bayan dawo daga gurin aikinsa dagashi sai singlet da 3cutr yadora kafarsa kan dani table dake tsakiyar dakin ya jingina jikinsa a jikin kujera, kallo yake amma hankalinsa kwata2 baya gurin yana gurin tunanin rumaisa, gaggar jikinsa ce kawai zaune a gurin amma zuciyarsa bata tare dashi,

Momy ce tafito daga cikin dakinta, ta ganshi saune yayi kuru da edo yana kallon tv, tayi murmushi sannan takarasa gurin tazauna tana kallonsa takira sunansa har sau biyu taji yayi mata shiru, bubbuga kujerar tayi sannan ya zabura yana kallonta " momy" yakira ta yana kikarin yin murshi, yaushe kikazo nan "

momy tayi ajiyar zuciya tana kallonsa tace " taya za'ayi kasan nazo, tunda kadauki damuwa kasaka kanka aciki, wai mekakeson kazamane faisal akan soyayya duk kabi ka susuce, jibi yadda karame sai kace bakaiba"

Faisal ya tsuke fuska, shiko yawan magana yanzu bayaso, shidai yafison kummul abarsgi alone, yace " menayi kuma umma, nifa ba ita nake tunaniba, kawaidai ina kallone"

Momy taja nunshi tace "duk yadda kaso kaboye damuwarka, bazaka iyaba domin fuskarka da jikinka zasu bayyana hakan, kiyi kokarin saita kanka faisal"

Faisal yasaukar da kafafun daga kan dani table di yana kokari saka takalminsa, yace "nifa babu abinda ke damuna momy, ni baccima nakeji " yamike tsaye momy ta bishi da kallo haryabar falon, ta girgiza kanta zuciyarta cike da tausayin yaronta, akan soyayya duk yabi ya susuce...
****** ******** ******
_One day later_

Rumaisa ta koyawa fahad abubuwa sosai kuma sun shiga kansa, yanzu yasan yadda zaiyi sallaj aduk lokacin dayaji ankira sallah,

hankalinsa yasoma dawowa kansa, rumaisa tasakashi harda siyo littattafan addini, (kujimun samun guri irin na rumaisa) yanzu kam tasake dashi sosai,

Yauma suna zaune a falo, tana koya masa adu'oi, tasaki jikinta da gidan kamar gidansu, daman cen a gidan nasu ba wani farin ciki take samuba, yanzu kuwa tasamu freedom,

Kallonta yakeyi kamar zai hadiyata ita kuwa kanta na kasa tana karan ta masa littafin dake gabansa,

Saidai ta lura da hankalinshi baya gurin sannan ta dago kanta tana kallesa taga ita yake kallo, ta kida masa masa hannu da sauri ya zabura, yana murmushi, itama murmushin tayi tana kallonsa tace " littafi zaka kalla baniba"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.