Trending Hausa Novels

Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Majnoon Part 1.txt

Chapter 9 of 36

Dafe kansa yayi kafarsa sai rawa take yakasa tsayuwa guri daya,

Bayan Likita ya kammal mata dressing, sannan ya juyo ya kallo fahad yace "ogaa komai ya kammala insha Allah nan bada jima waba zata sami sauki"

Fahad ya girgiza masa kai, yana hawaye, nan likitan yayi sallama dashi yatafi,

Da kyar ya iya karasa bakin kujera wadda take duban tata shima ya kwanta yana kallonta... jira yake ta farka,

7:52am
Har safiya tafara bayyana, rumaisa ta bude idonta, zafi taji a kanta hakan yasa tasa hannu ta dafe kanta tana wasshh, jin bandeji a goshinta yasa tafara tuna abina yafaru jiya, da sauri ta mike tana kokarin tashi, nan kuma jiri yakara d'ibanta, tangal-tangal tayi zata fadi a lokacin fahad yakaraso gurin da sauri ya rikota tafada kirjinsa tana mayar da nunfashi, shikuwa ya kura mata edo, yana kallonta,

Ita kuwa edonta a rufe yake domin ida ta bude edon gani take dakin na juya mata,

Tajima a kirjinsa, kafin ta fara bude edon a hankali, caraf edonta suka sauka akan nashi, da karfi ta mike tana kallonsa, ranta a bace, wani irin haushinsa takeji,

Harara ta auka masa sannan tanufi hanyar dakin datake,

biyota yayi yana kiran sunanta amma ko juyosa bata yiba, tana karasawa bakin kofar dakin tashiga sannan ta turo kofar da karfi kamar zata game da hannunsa da sauri yaja baya, tasaka key ta rufe kofar, ta jingina jikinta a jikin kofar, kuka ta somayi mai sauti a hankali take sulalewa kasa tana kuka hartakai zaune,

Fahad kuwa sai knocking kofar yake yana kiran sunanta amma taki budewa, jin sautin kukanta dayake yakara tayar masa da hankali,

A hankali ya ke furta "plx rumaisa kiyi hakuri, wallahi bada sanina komai yafaruba, dan Allan kibude kofar"
rumaisa tayi bnza dashi kuka kawai take,

Fahad yaja nunfashi yace " nayi miki alkawarin daga yau nadaina shan giya, dan Allah kibud'e kofar"

Duk da kukan datake amma saida tayi murmushin karfin hali, jin kalaminsa nacewa zai daina shan giya,
Amma kuma saita gagara tashi ta bude masa kofar,

Fahad yayi jim, yajita shiru, hakan yasa yajuya ba'ason ransaba zaibar kofar,

Sautin karar budan kofar yatsayar dashi, yatsa cak guri daya, yana kallon kofar,

Tana bude kofar takoma bakin gado tazauna ta dafe kanta tana hawaye,

A hnkali ya turo kofar dakin yashigo, yakarasa bakin gadon, kusa da ita yazauna, yashare hawayensa, ya kalleta yace " wai garin yayi wannan abin yafaru, ni bnsan lokacin dana aika hakan agarekiba"

Rumaisa tayi bnza dashi ko uffan tagagara ce masa, a lokacin ta tuna da batayi salla ba,

Tana yunkurin tashi Fahad yace " talk mana" harara ta dalla masa tamike tanufi toilet,

dasauri yatashi yabita baya,

Takai bakin kofar toilet din taga yana kokarin binta hannu ta daga masa " karka kuskura kabiyoni"

Tana gama fada bata jira yayi maganaba, tafada toilet din tamayar da kofar ta rufe,....

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:43 PM] ‪+234 905 395 7618‬: [8:12am, 09/08/2016]
_Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

43 and 44
Via *OHW*
_A love story_💝

Shiru yayi yana kallon kofar ban dakin kafin yajuya yadaki ginin dakin, yana yajan nunfashi sannan ya koma bakin gado yazauna, yana tunanin rayuwarsa wai yau shine kebiyar macce, shida bai mayar da mace komaiba, amma yau gashi macci na wahalar dashi,

A lokacine yaji kamar kafarsa na masa ciwo, kallon kafar yayi yaga jini, kwalbar giyar daya fasace yataka kuma harta fasa kafar, yadago kafar yana kallon, zafi yakeji sosai,

A daidai lokacin rumaisa tafito daga ban dakin, yana jin fitowarta yayi saurin sauke kafarsa yana murmushin sai kaice wadda babu abin kedamunsa,

Bata kulashiba, yana kallonta ta karkade kasan cafet din tafara sallah, yana zaune yana kallonta tana salla,
Jiyayi yana sha'awar yayi sallah,

Amma ya gagara tashi, yana zaune har rumaisa ta kammala sallar, sannan tazauna tayi adu oi, tana gamawa ta soke kanta kasa tana hawaye,

"Harkin gamane " fahad yafada cike da fargaba,

Rumaisa ta dago kanta amma bata juyo gurinsaba tace "meya dameka da sallana, aikai bakayi" tana gama fada saikuma tayi shiru, .

Fahad yayi murmushin, yaji dadin data amsa masa maganar mike wa yayi yakarasa gurinta yazauna kafarsa namasa zafi sosai ya dubeta yace "fushe kike dani Rumaisa" yafadi maganar a marairaice ,

Sai a lokacin rumaisa tadago edota ta dubesa, ta share hawayenta sannan tace " dole nayi fushi dakai domin kasauka akan tafarkin addininka kakama addinin yahudu da nasara, Fahad takira sunansa, ths is th fst tmy data kira sunansa, sai yaji abin wani daban, the way yadda takira sunan yamasa dadi, yace "yes "
Rumaisa tace "baka sallah, sannan kuma baka tunanin lahirarka, kadauki duniyar nan kamar wani gidan jindadi, kamanta cewa a koda yaushe zaka iya mutuwa kuma kakoma ga Allah, mezaka fada masa idan kaje garesa, zaka fada masa cewa shan giya da neman mata shiya hanaka yin salla, bazaka iyaba, a ranarma bakinka bazaiyi magana domin baki zai iya shirya karya, sassan jikinka sune zasuyi magana wadanda kasan dacewa kana aikata barna dasu, fahad kaiba yaro bane, kamallaki hankalin kanka, yakamata kagyara zamanka da uban gijinka" nadai tashiga karoro masa nasihohi daban-daban...

Jikinsa yayi sanyi sosai, ajiyar zuciya yayi sannan yace "shikenan naji, zan daina komai, indai har hakan zai sakaki farin ciki, ya kara kallonta yana murshi kafin yace "amma namanta komai kikoyamun yadda zanyi"
Dadi sosai rumaisa taji,

Acen kasar zuciyarta tace yes my mission started,...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10:43am, 09/08/2016]
_Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

45 and 46
Via *OHW*
_A love story_💝

kallonsa tayi tay murmushin tace "shikenan zan koyama"

Shima murmushin ya mata,

Zafin kafarsa yakai masa ko ina yayi yunkurin tashi, sai a lokacin rumaisa ta lura da jinin dake fita a kafarsa,

Tace "subhanallah, jin ciwo kayine" ya girgiza mata kai,

Oh sorry" tafada tana kokarin taba masa kafa, da sauri ya janye yana kallonta yace "babu kyau macce tataba kafar daba ta mijintaba"

Rumaisa ta kallesa tayi murmushin tajidadin maganar har cikin ranta tace "babu shamaki gaduk wadda zai tamakawa musulmi dan uwansa a duk lokacin da yake cikin neman taimako, dan haka idan har taimakonka zanyi babu laifi idan natabaka"
Fahad yayi dariya yace "ok shikenan" ya miko mata kafar ta kama ta matse jinin daya taru a ciki sannan tamike taje toilet ta dibo ruwam zafi a heater tazo tana gasa masa kafarshi, tana dan kara yimasa bayanin akan addini,

Haka dai harta kare, sannan tatashi taje tashirya musu breakfast, bayan sun gama suka dawo falo suka zaune tafara kowayar abubuwa, ranar tasaki jiki sosai dashi,

A ranar babu inda yafita yana gidan har yamma tayi, kuma ya koyi abubuwa dadama daga gurin rumaisa,
****** ***** ****
Allah sarki majnoon,
Majnoon nagani a rakube a gefen tati yana kakkarwar sanyi, duk ya rame yakara fita hayyacinsa,

Duk da babu hankali a tatare dashi amma dai yaji rashin zuwan rumaisa gurinsa, yashiga da muwa sosai amma babu wadda yadamu dashi balle yasan damuwa sa, yanzu yama soma daina yawan wasar nan da yara, burin shi kawai shidai yaga Rumaisa. ..

ALLAH SARKI SOYAYYA...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:43 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

47 and 48
Via *OHW*
_A love story_💝

*Bayan kwana biyu*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.