Trending Hausa Novels

Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Majnoon Part 1.txt

Chapter 25 of 36

Adnan yayi murmushi yace " hmm nima wlh nagaji, amma dai bazan kwantaba sainayi wanka"

Tabe baki kawai faisal yayi "uhim kaika sani nikam wanka saida safe, Allah bazan iya tashi ba yanzu"

Adnan yayi shiru yana murmushi, sai da yagama cire kayan dake jikinsa, dagashi sai singlet da boxer, ya juyi ya kalli faisal yace "yawwa daman mantawa nayi ban fadamaba "

Faisal yadago kansa "eh menene "

Adnan yace " daman umma ce tace, sati mai zuwa muje abuja muzo da wancen mutumen maikama da yaya Mubarak, "

Faisal ya koma kwance yana cewa "tohm shikenan Allah yakaima, sai kuma yadago kansa ya dube faisal yace "saidai kuma akwai matsala"

Dasauri adnan yace "matsalarme fa"

Faisal yace " daman naso nasanar dakai cewa shifa waccen mutumen, yanada matsala domin ya manta da komai daya taba faruwa dashi a baya, ma'ana yakamu da cutar amnesia"

Gaban Adnan yayi mummunan faduwa, awani bangare kuwa dadi yaji, domin ayanzu yanada damar dazai tunkare majnoon babu fargana tunda yamanta komai,

Ajiyar zuciya yayi, zuciyarsa cike da farin ciki sannan yace " ba cutarsa bane damuwarmu, damuwarmu shine munemawa umman Mubarak lafiya, domin na tabbatar dacewa tana ganinsa zata samu lafiya, bayan tasamu lafiya daga baya mayi mata bayani, wlh ni matar tausayi take bani" yakarasa maganar cike da makirci,

Faisal yace "toh shikenan nima ina goyon bayanku dari bisa dari, kuma zan baku duk wani taimako, daya dace, Allah yakaima sati mai zuwa"

Adnan yace "ameen, nidai na zanshiga wanka saina fito"
Yana gama fada yanufi toilet,

Faisal yayi yaja nunfashi sannan yajanyo filo yagyara kwanciyarsa,
Zuciyarsa cike da tausayin umman Mubarak,

Tun kwanan baya daya shiga sashen umma Mubarak yatayar mata da ciwo, tun daga ranar bai kara shiga sashen ba tsoronma zuwa gurin yake domin baya sonma taganshi....

https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:52 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

101 and 102
Via *OHW*
_A love story_💝

*Bayan kwana hudu*

Ranar takama ranar juma'a bayan abban rumaisa yadawo daga masallaci,

Yazauna falo yana fira shida Momy, suna cikin firarsu abba yace "ina rumaisa takene"

Umma tace "tana cikin dakinta, ita da kabir, nashiga dazu nagansu suna karatu"

Murmushi abba yayi sannan yace "bari inje insame, zamuyi magana dasu" yana maganar yana kokarin tashi harya mike, sannan ya wuce dakin rumaisa,

Suna zaune rumaisa ce ke ja masa karatun shikuwa yana zaune kusa da ita yayi jugum,

Yafada duniyar tunani, idan suna tare da rumaisa, sai yarikajin yanason kamar ya iya tuna wani, amma sai kuma yakasa,

Abba yaturo kofar dakin yashigo, hakan yayi sanadiyar juyowarsu gabaki daya suna kallon kofar,

Murmushi abba yamusu, suma sukai masa, yakaraso kusa dasu yayi tsaye a kansa yace "karatu kawai kukuyi"

Rumaisa tace "wlh kuwa ai mumma kusa gamawa"

Abba yayi murmushi yace "yawwa hakan yanada kyau" sai kuma yadanyi shiru kafin yace "amm daman maganar auren kune gobene, kuma ni banason yawan taron jama'ar nan, nasa angayyatomin malamai sannan kuma abban faisal shizai wakilci kabir a gurin daurin auren, sannan kuma cikin harabar gidan nan nakeson adaura auren, dan haka idan kinadawa wasu kawaye dazaki gayyato saiki sanar dasu, amma fa bada yawaba"

Farin ciki gabaki daya ya lullube rumaisa, tana murmushi race "ni abba banida wasu kawaye da yawa, yan skull dinmune kadai, kuma bazasu wuce mutum biyarba, sannan kuma suduka nasanar dasu"

Abba yace "yawwa hakan ma yayi"

Kabir ya dube abba yace "abba ni ina nawa abokanai"

Murmushi abba yayi sannan yace "gamu! ! ai mune abokananka, kuma danginka, kakwantar da hankalinka, kaji?" Abba yakarasa maganar yana kallonsa yana dariya,

Kabir ya girgiza kai,

Sannan abba yafita yabar dakin, yabarsu sukaci gaba da karatunsu,

Rumaisa sai farin ciki takeji a cikin xuciyarta,

Burinta ya kusa cika, Majnoon zai zamo mijinta...

*Washe gari*
ranar aure,
Tunsa sassafe abba ya yasa aka share harabar gidan tasss,

sannan yadauko wayarsa yakira daddy faisal yasanar dashi cewa kafin 10:00 yakirawo malaman gabaki daya su hallara a harabar gidansa, zuwa karfe 11:00 a daura aure,

"Toh" kawai daddy yace sannan suka kashe wayar,

Suna kashe wayar daddy yakira faisal,

Yana kwance a cikin blanket yana bacci mai dadi, yaji wayarsa tadau kara, a hankali ya zuro hannunas yadauki wayar yakara a kunnesa, batare daya duba wayake kiraba,

Hello son" shine sautin daya daki kunnensa, sai lokacin yasan da cewa daddy ne kekira, cikin muryar bacci yace "daddy antashi lafiya"

Daddy yace "lafiya lau, amm daman tun jiya naso nakiraka nasanar dakai cewa yaune daurin auren rumaisa ita da wanna marar lafiyan"

Wani irin mummunan faduwar gata ya ziyarci faisal, da karfi yace " what! !!, da sauri yaye blanket dinda ke jikinsa, daddy yace " lafiya kuwa meke faruwane "
Cikin gaggawa faisal yace "daddy ina zuwa ..." da sauri ya tsinke wayar, yace "ohh shet"

Juyawa yayi gefen adnan, dake bacci sai kwasar minshari yake yasamesa yana bacci, da karfi faisal yake bubuga kafarshi yana kirana sunansa, "kai tashi akwai matsala"

A hankali yake bude edonsa ya dube faisal yace " lafiya kuwa ?"

Faisal yace " ina kuwa lafiya, yanzun nan daddy ya kirani wai yaune za'a daura auren, mutumen abuja mai kama da yayanka Mubarak,"

Da karfi adnan yamike cike da tashin hankali yace "ehhh, nashiga ukku" cikin gaggawa faisal yace " yadace ace mun isa garin abuja kafin a daura auren nan, domin kasan idan aka daura auren nan baza a barmu muzo dashiba"

Adnan yace "hakan za'ayi maza jeka dakinka kayi wanka nima yanzu zanshiga nayi wanka anan " dasauri adnan, yafada toilet,

Shima Faisal yakoma dakinsa yashiga wnka, bawani wankan kirki adnan yayiba domin duk ya tsorata, yana fitowa cikin gaggawa yasaka kayansa, yana gamawa yanfi dakin ummansa,

Yana shiga dakin yatarar da ita zaune akan sallaya, nan yashiga fada komai dake faruwa, bakaramar firgita tayiba, cike da tashin hankali tace " bazakuje a mota ba, jirgi zaku hau yanzu yasaukeku abuja, kushirya maza kuje airport kafin mai martaba yatashi daga bacci"

Haka kuwa akayi bayan sun gama shirya duk yadda abin zai kasance,

Atare suka fito shida umma,

Koda suka fita suka tarar da faisal tsaye a bakin kofar dakin adnan, shima haryazo bai gansa cikin dakinba shine yatsyawa waje yana jiransa,

Nan suka wuce zuwa harabar gidan, driver yadaukesu a moto ya lula dasu zuwa airport....

Aha muje zuwa....😃

https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:52 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

103 and 104
Via *OHW*
_A love story_💝

Suna karasawa airport sukayi sa'a kuwa jirgir safe bai tashiba, nan suka shiga.... suka lula zuwa abuja..
â–¡â–¡â–¡â–¡ â–¡â–¡â–¡â–¡ â–¡â–¡â–¡â–¡
Rumaisa tana zaune a daki, tare dawasu kawayenta su biyu, leemart da kuma maryam, suna fira, amma ita sam zuciyarta bata gurin, tunani takeyi ashe daman burinta zai cika akan MAJNOON, yau za'a daura mata aure tare da kabir (Majnoon) tazamo mallakinsa shima yazamo nata, daman hausawa sunce komai yayi farko zaiyi karshe

Maryam ta dafata, ta baya, saida ta zabura "waike tunanin me kike ne, tun dazu muke miki magana amma kinyi shiru"

Rumaisa ta sosa kanta, cike da jin kunya tace "amm bakomai, me kikace ?"

Maryam tace " cewa mukayi kitashi kije kiyi wanka kingafa lokaci yana tafiya"

Murmushi rumaisa tayi sannan tace "Tohm shikenan kujirani yanzu zanfito" tana gama fada tamike tafada toilet,
â–¡â–¡â–¡â–¡ â–¡â–¡â–¡â–¡ â–¡â–¡â–¡â–¡
Abba kuwa tuni yayi wankansa cikin farara shadda, sai fara,a yake, anata shirye-shirye fara daura aure,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.