Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels
Reading file: Majnoon Part 1.txt
Chapter 14 of 36
*Wacece zarah...*
Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's
Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:45 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_
_Author_:- *MR, SMILES*😃
61 and 62
Via *OHW*
_A love story_ðŸ’Â
*Wacece zarah*
Zarah heesham shine asalin sunananta, black beauty ce ga diri ga k'ira sonkowa kin wadda yarasa,
Zarah ta kammala karatunta na degree yanzu haka tana aikine a wani company, a company ne suka hadu da faisal, tun farkon haduwarsu da ita tafara nuna masa so amma shi saiya rika basarwa,
Hakan yasa tanace harsaida takai data furta masa, tun da ta furta masa cewa tana sonsa kuwa a take a gurin ya yi watsi da maganar tare da dayima wulakanci, ko da gargadin cewa karta kara bijiro masa da irin wannan maganar,
Amma duk da haka zarah bata daina binsa ba tanayi masa magiya akan yakarbi soyayyarta amma faisal yaki, kullum wulakancinsa kara karuwa yakee. Zarah tayi masa kuka har ba iyaka amma kwata2 yakiji tausayinta, shi ace warsa baya kaunarta, shi bata yimasa baki daya, duk wulakanci na duniya faisal yayiwa zarah akan yaga yacire mata sonsa a cikin zuciyarta amma ina yakasa...hakadai zarah taketa hakuri dashi, tana kara lallashin zuciyarta akan ta dage wata rana zatayi nasara akansa, ( wace rana ce wannan ) oho
Iyayen zarah ma'aikatan kwainatine, mahaifinta da mahaifiyar duk aiki suke, mamarta doc ce, mahaifinta kuwa librarian ne a wata university,
Su biyune a gurin iyayensu daga ita sai kanwanta Nafisat wacca suke kira da feena...
_Wannan kenan_
***** ***** ******
Haj lubace zaune a daki tasaka rumaisa gaba tana tambayarta akan tagaya mata yadda wannan abin yafaru kuma ta sanar da itada meye silar faruwarsa, rumaisa kuwa bayan kuka babu abinda take, hajja luba tace "to nidai nagaji da wannan kukan naki, tunda bazaki fadamunba, ni zan koma waje idan kingama kukanki saiki kirani kisanar dani" tana gama fada ta mike tsaye,
Rumaisa tayi saurin riko hannunta, tana shanshekar kuka tace "zan fada, dan Allah kizauna wlh zanfada "
Haj luba tayi ajiyar zuciya sannna ta zaune tace "fadamun ina jinki, meye silal faruwar komai" ta fada ta kallon rumaisa edo cikin edo,
Muryar rumaisa na rawa tafara fadawa hajja luba, komai daya faru, harda dukan da abbanta yamata akan saita aure faisal, tun bata karasa gayawa hajja luba,
Hajja luba ta dakatar da ita, zuciyarta tadau zafi zanta yabace sosai cike da masifa take fadan "shi Usman (abban rumaisa) shine zai miki auren dole, harda duka, wato kenan badan Allah yasa kinzo nanba , dasaidai kawai naji auranki daga sama, to wlh bai isaba, yadda yake nuna ikonsa akanki nima haka inada iko akansan domin nice na haifesa, hajja luba tayi shiru tana huci, sannan ta kara kallon rumaisa tace "kikace kinada wadda kikeso koh" Rumaisa tace "eh inada"
Haj luba tace "ya sunansa kuma d'an gidan waye" gab rumaisa ya tsinke yafadi, domin acikin labarin data bawa hajja luba bata sanar da ita cewa mahaukaci take soba, rumaisa tayi shiru tana kallon hajja luba, batasan sunan majnoon ba ballema hartasan sunan iyayensa, a wane gari yake oho, itama bata saniba, tsoro takeji karta fadawa hajja luba cewa wadda yakeso mahaukacine ne, domin tasan dacewa, zata dauki maganar tata ashirmen banza,
Tayi shiru hajja luba ta tsureta da edo, bakinta na rawa ta soma furta " bansan..."
Hajja luba ta dakatar da ita domin duk zuciyarta tadau zafi, wani irin haushin abban rumaisa takeji, tace " bana mason kifadamun sunansa ko sunan iyayensa, wlh babu makawa shizaki aura kuma nayi miki alkawarin indai ba mutuwa nayiba saikin auresa" sai kuma ta koma fada " maganar banza maganar wofi yanzu ai zamani ya chanza andaina yiwa mata auren dole, 'yar jikan tawa kwaya daya tak, za'a nemi amata auren dole salon idan aka kaita gidan mijin bakin ciki yanemi kasheta, toh bai isaba wollah"
Rumaisa tayi shiru sauraronta kawai take, tasoma ganin nasara acikin lamarinta da majnoon, amma saidai tana fargabar ya Hajja luba zata dauki abin idan har taji labarin cewa mahaukaci takeso"
Dafa kafadunta Hajja luba tayi hakan yayi sanadiyar fitowarta daga duniyar tunanin data shiga Hajja luba ta dubeta tace "kitashi kije kiyi wanka, kizo kici abinci, insha Allah gobe zamu koma abuja, kuma ina mai tabbatar miki dacewa zaki aure wadda kikso"
Rumaisa ta rungumeta tana kuka " nagode inna" kukan farin take,
Sannan A hankalin tafito daga jikin Hajja luba tana share hawayenta sannan ta mike tafita tabar dakin tanufi ban daki,
Wanka tayi tafito koda tafito Hajja luba ta ajiye mata abinci, zaunawa tayi taci ta koshi, sai alokacin tasamu natsuwa,
Daki takoma takwanta saman gado, tunina barkatai suka rika zomata, yanzu ya fahad yake oho itama bata saniba, sai dai har yanzu akwai sauran tausayinsa a zuciyarta, wannan me yake nufi *so'ne ko tausayi*,
Majnoon dintafa yanzu wane hali yake ciki, tabbas tayi kiwarsa sosai, kalaman Hajja luba suka rika dawo mata a kwakwalwa nacewa dole saita aure wadda takeso,
murmushi tayi cike dajindadi, a zuci tace "Allah yasa hakan nee" nan dai taci gaba da tunani kala kala, har bacci yazo mata...
Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's
Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:45 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_
_Author_:- *MR, SMILES*😃
63 and 64
Via *OHW*
_A love story_ðŸ’Â
*Washe gari*
Tunda sassafe hajja luba tazo tatashi rumaisa, tun agurin ta sanar da ita cewa, idan tagama salla tayi wanka tazo tasameta, domin motar safe zasubi suwuce abuja,
Haka kuwa akayi bayan rumaisa tayi salla sannan tayi wanka ta shiya, tazo tasami hajja luba zaune a harabar gidan itama ta shirya, karin kumallo kawai sukayi, suka wuce tasha, basu dad'e sosai ba a tashar suka sami mota nan suka hau hanyar zuwa abuja,
***** ***** ******
A *Abuja*
Fahad yana kwance kan gadon asibiti edonsa suka fara motsawa, sunana kokarin budewa, a hankali har edon suka yashe, kallon dakin yakeyi gefe da gefe, firgir ya mike zaune, yana mamakin wannan dakin inane, juyowar dazaiyi suka hada edo da ummansa, cike da farin ciki take kallonsa,
Shikuwa mamaki yacikashi, abubuwan da suka faru jiya yarika tunawa, muryarsa na rawa yace " ina rumaisa"
Abba yana tsaye ya kura masa edo cike da rashin fahimta, maganarsa, wace rumaisa kuma? Abba ke tambayar kansa,
umma takaraso gurinsa ta rike hannunsa tace "wacece kuma rumaisa"
Abba shima yakaraso gurin yana cewa "wacece kuma Rumaisa son" duk mamaki yacika su,
Fahad ya dafe kansa dake masa zafi yana kokarin tashi tsaye abba ya zaunar dashi, tuni hawaye suka cinciko masa edo, nan yasoma kuka yana fadan "kubarni natafi gurinta abba, wlh banzan samu salamar zuci ba matukar banga Rumaisa ba, itace farin cikina, dan Allah kubarni natafi"
Umma ta dube abba, abba ya dube umma sudukansa mamaki yacikasu, wace irin rumaisa ce wannan data rikita musu yaronsu,
Ganin basuce dashi komaiba yasa Fahad yakara fashe da kuka yana cewa " nacuce kaina, na cuce zuciyata, ya dube abba sannan yaci gaba dacewa "abba daga yau nadaina shan giya, wlh duk abinda rumaisa bataso zan daina, zan dawo mutumen kirki sabida ita, dan Allah abba kanemamin aurenta, idan bansamu auren rumaisa ba wlh bazan iya rayuwaba, dan Allah abba kanemamun auren rumaisa..." yakarasa maganar yana kuka sosai duk ya fita hayyacinsa,
Umma duk ta rikice, tunda take bata taba ganin kukan fahad ba akan macce sai yau,
Abba kuwa tuni edonsa sunyi ja sosai, yana tunanin wannan wacece ita kuma 'yar gida waye, tabbas zai nemota kuma zai nemawa yaronsa neman aurenta koda kuwa dukiyarsa zata kare kaf akan wannan matsalar,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.