Trending Hausa Novels

Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Majnoon Part 1.txt

Chapter 21 of 36

Muje zuwa...😊

Koda faisal yakarasa asibitin duk yad'an saki jikinsa, a mota yatsaya yakara daidaita kansa sannna ya nufo cikin asibitin,

Umma tana zaune a kusa da rumaisa tana mata fira cike da farin ciki, domin a yanzu rumaisa takara samun sauki,

Faisal yashigo dakin tare dayin sallama, suka amsa masa a tare,

Yakaraso gurin yagaida umma cike da ladabi da biyayya,

Umma ta amsa masa cike da fara'a,

Rumaisa kuwa tunda suka hada edo dashi sau daya taji gabanta yafadi, ta kauda kanta daga kallonsa,

Faisal yayi mata ya jiki, ta amsa masa da cewa naji sauki,

Ganin yayi tsaye yaki magana sai mazurai yake da edo yana sosar keyarsa, yasa umma ta fahimci akwai magana a bakinsa daya keson yayi da rumaisa,

Hakan yasa tamike tabar bakin tafita waje,

Faisal yakaraso kusa da rumaisa yana kallonta suka kara hada edo, da saurin rumaisa ta kauce edonta akan nasa,

Ya sauke ajiyar zuciya yace "rumaisa karkiyi tsammanin nazone akan maganar soyayyarmu! Aa, wannan karon nazone akan neman gafararki akan tilastaki danayi akan dole saikin soni, kiyafemun"

Rumaisa tayi rau rau da edo duk kwalla tacika mata edo muryarta na rawa tace "nibakamun komaiba, sannan kuma ni bana ganin laifinka domin *DAMA HAKA SO YAKE* bai cika kai kansa inda ake sonsa ba, yafison yaje inda zai sha wahala, tayadda daga baya koda yasamu mai sonsa yarikeshi da daraja, ina mai baka hakuri abisa Rashin karbar soyayyarka dabanyiba, kayi hakuri zuciyatace takasayin hakan "

Faisal yasauke nunfashi ya share wasu guntuyen hawaye dake makkale a gefen edonsa "shikenan, Allah yazabawa kowa abinda yafi zama mafi alkhairi agaresa"

Ameen " rumaisa ta amsa masa,

Sai kuma sukayi shiru, tunani barkatai suka rika zoma faisal, duk yaji bayajin dadi,

Zuciyarsa duka takeyi tara2, yanzu shikenan an rabashi da abarsonsa, abar alfaharinsa, kai ina bazai yuyuba ace zai iya rabuwa da rumaisa, to idanma ya rabu da ita wazaiso, shifa ita kadai yafara so, duk a zuci yake wad'an nan maganganun,

Da karfi sukaji anturo kofar dakin, hakan yayi sanadiyar fitowarsa a cikin duniyar tunanin daya shiga,

Umma ce tashigo dakin cike da fara'a batama tsaya tunanin mesukeyiba, ta takarasa kusa da rumaisa tana murmushi tace "abbanki yace majnoon yafarka, kizo muje idan zaki iya tashi"

Da karfi rumaisa ta mike zaune tana dariya, duk farin ciki ya cikata "umma zan iya tashi, harda guduma zan iya, muje " tafada cike da zumudi tana kokarin tashi

Umma tayi murmushi sannan tataimaka mata takarasa tashi tsaye,

Faisal dake tsaye a gefe duk mamaki yacikashi waye shi wannan majnoon din dahar fadar sunansa zai saika rumaisa dariya da farin ciki haka, kodai shine wanda takeso?

Basu kula Faisal ba har suka fita daga cikin dakin suka nufi dakin jinyar majnoon,

Faisal ya tsaya turus yana mamaki, zaiso yaga wanda rumaisa takeso, yaga dame yafishi,

Kasa hakura yayi dole yabi bayansu,

A tare suka shiga dakin umma da rumaisa, sai kuma ga faisal a bayansu,

Hajja luba, likita , da kuma abban rumaisa duk suna cikin dakin,

Majnoon ya dube mutanen dake zagaye a dakin yana mamakin suyawe su,

Edo kawai ya kura musu yabisu da kallo

Likita yakarasa kusa dashi yace "ya jikin naka, me kakeji a yanzu"
Majnoon ya dube likita yana mamaki, muryarsa na rawa yace "miya samenine "

Likita ya sauke ajiyar zuciya, a lokaci yatuna matsalar ciwon mantau da kedamun majnoon, sannna yace "kasamu hatsarine akan titi"

Cike da mamaki majnoon ya ke maimaita maganar "nasamu hatsari" ya dube likitan yace "a ina nayi hatsari, kuma a yaushe, suwaye wa dannan" ya nuna su abban rumaisa,

Likita ya dube su abban rumaisa yayi murmushi sannan ya juya gurin majnoon yace "wadan nan yan uwan kane"

Majnoon yakara maimaita maganar " 'yan uwana kuma?, ni harda yan uwa nake dasu"

Likita yace "sosai makuwa "

Majnoon duk komai yadaure masa kai a hankali ya dube likita yace " Waye ni ?"

Gaban kowa dake cikin dakin saida yafadi...

(Nimadai mamaki likitan yabani, sai kace ya manta da dacewa majnoon ya manta komai)...

Likita ya juyo ya kalli abban rumaisa, cike da tsoro wace amsa zai bawa majnoon,

Dakin yayi tsit, majnoon sai kallon su yake, rumaisa kuwa duk jikinta yadau rawa, tana fargabar kar majnoon yakasa fahimtarsu,

Wata idea tafadowa likiti, dasauri yace "amm wannan sunansa abba, ya nuna abban rumaisa yana murmushi

Sannan yajuya gefen umma "wannna kuwa sunanta umma" ya nuna umma,

Sai kuma yakara juyawa gefen hajja luba "wannan kuwa sunnan ta kaka" ya nuna hajja luba,

Yana kai ga rumaisa sai kuma yayi shiru, taya zai yiwa majnoon bayanin cewa wannan itace masoyiyarsa mutumen dako kansa baisaniba,

Likita ya nuna rumaisa yace "wannn kuwa itace matarka"

Gaban majnoon yafadi, da sauri yamike zaune yana kokarin tashi, likita yamaidashi kwance yadafe kansa, har saida yayi kara kadan, wani irin zafi yaji kwakwalwarsa tafara dauka, yana nishi kadan kadan, edonsa suka rikide zuwa jan launi,

Likita yace "lafiya kuwa, meke faruwa"

Majnoon ya dago kansa da karfi ya kalli rumaisa yace "ina yarona,,,,"

Tashin hanakali ya ziyarci zuciyar rumaisa, jitakeyi kamar ta zube a gurin, tambayar kanta take, me yake nufi da ina yaronsa, kardai ace majnoon yanada aure,

Daf taji gabanta yafadi...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:50 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

87 and 88
Via *OHW*
_A love story_💝

Rumaisa tasoma ganin jiri, habar bakinta tasoma rawa kamar zatayi magana, likita ya kifta mata edo, alamar tayi shiru,

Likita yayi saurin yin mumushi ya dube majnoon yace "ai bakuyi auren ba tukunna kafin kusami yaron"

Majnoon yayi shiru kamar mai nazarin wani abu, sai kuma yajuyo yaci gaba da kallon mutane,

Kan abba kallonsa yatsaya, yakurawa abba edo sosai, cikin saukankiyar murya yace "abba naji kowa an fadi sunansa amma ni banji anjira sunanaba, meye sunana"

Abba da duk ya tsorata da lamarin majnoon, cikin inada2 yace "amm ...umm..sunanka....ammm."

Likita yakarbe maganar dacewa "sunanka *KABIR*"

Majnoon yayi dariya yana maimaita sunnan sai kuma yayi shiru, ya koma kwance,

Likita yayi ajiyar zuciya sannan ya juya ya dube abba yace "muje waje zamuyi magana" yana gama maganar yafita yabar dakin, abba yabi bayansa,

A office suka karasa, bayan abba yazauna likita yace "saidai kuyi hakuri domin shi a yanzu komai sabone a gurinsa, saikun dinga nuna masa abubuwa, sannan kuma kusaka rumaisa ta shiga jikinsa sosai ta yadda zai saba da ita, kafin ranar aurensu"

Ajiyar zuciya abba yayi ya duban likita " toh shikenan likita insha Allah zamu kiyaye"

Likita yace "yawwa, zuwa nan da kwana biyu idan yakara samun sauki zamu iya sallamarku"

"Tohm" abba yafada yana kokarin tashi, yafita yabar office din,

A harabar asibitin sukayi kicibus da faisal yafito yana kokarin gita daga asibitin,

Kala baicewa abba ba, yasa kai yafice abinsa,

Abba yatsaya yana kallonsa cike da mamaki, girgiza kai kawai yayi yakara dakin jinyar Kabir (majnoon),
â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– 

Koda faisal yafita zuciyarsa cike da k'una da kuma wasu wasi kala2,

Daman akan wannan ne rumaisa takasa karbar soyayyarsa,

Toh me wannna yafishi,

Motarsa yashiga, ya kunna, Sannan ya hau hanyar komawa gida, amma duk hankalinsa yana kan majnoon, duk sai yaji garin yafita ransa, zaiso ma ace a yanzu yabar garin,

Tun acikin mota yayanke shawarar bazai kwana a garin abuja ba, domin yaga abin yazo masa wani iri, daman duk akan mahaukaci ne Rumaisa take wannan abun,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.