Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels
Reading file: Majnoon Part 1.txt
Chapter 16 of 36
Ya dago kansa ya kalleta a lokacin har hawaye sun fara fita a cikin edonsa, murya a sanyaye yace "kada zuciyarsa tayi zargin cewa nazone domin na cuta miki a a, hakika rumaisa bazan taba mantawa dakeba a tarahin rayuwata saboda irin gudun muwar da kika bani wacca ita narasa tun a baya da rayuwata bata kasance a yadda kika tsinceniba, banada alkhairin dazan iya saka miki dashi sai dai ina rokonki Alfarmar abu guda daya agurinki" fahad yadanyi shiru yana kokarin share hawayensa, folon gabaki daya shi ake sauraro, sannan yace "Dan Allah rumaisa ki yarda ki aureni, ta wannan hanyarce kadai zan iya saka miki akan alkhairin da kikaimun"
Gaban rumaisa yayi mummunar faduwa tabbas fahad yabata tausayi amma saidai idan tayi na am da kudurinsa to tabbas ta cuci kanta, domin bashine a cikin zuciyarta ba, hawaye ke fita a edonta tasa hannu ta share, cikin sanyin murya take Takira sunansa, yadago kansa ya kalleta, sannan taja nunfashi taci gaba dacewa "tarayyata dakai banayita tabe danna aureka saboda ni ban taba kaunar kaba, na kusancekanee kawai dan na fidda kai halin dakake ciki amma ni bantaba jin sonka a zuciyataba, kayi hakuri"
Tunda tafara maganar zuciyar fahad tasoma duka tara2 , hankalinsa yayi mutukar tashi dajin kalaman rumaisa, hawaye suka kara sauko masa, yakara marairaice fuska yana cewa "amma rumaisa idan kikamun haka bakimun adalciba, dakinsan haka zakimun dakin barni naci gaba abubawan danake daya fimin, amma danme zaki dandanmun zuma a baki kihanani lasa, dan Allah rumaisa ki amincedani"
Rumaisa tayi ajiyar zuciya tana kallonsa tace "fahad nifa bazan aure kaba, domin ni inada wadda nakeso" tana karasa maganar sai kuma tayi shiru, ganin hankalin kowa a falon yadawo kansu, duk taji ta tsargu, a hankalin sautin kuka fahad yasoma fita, jiki a sanyaye ya mike tsaye yana kallon rumaisa sannan yace "amma meyasa zakimun haka, kinkuwa san yadda zuciyata take bugawa ayanzu, wlh jinake kamar zata fasa jirkina tafito, karki illatamun rayuwa rumaisa, kece kadai wacca nakeso dan Allah rumaisa kiyarda ki ...." rumaisa ta daga mishi hannu tasauya yanayin fuskarta zuwa bacin rai cike da hargo tace "me kakeson nayi maka ne, nidakai munyi alkawarin aurene, ko kuma nace zan aurekane, nagaya maka bana sonka, kafita rayuwata mana aaaa"
Abban fahad duk jikinsa yayi sanyi a hankali yakarsa gurin ya janyo hannun fahad, kuka fahad yake sosai,
umman fahad ma haka kuka take tasa gyale ta toshe bakinta kar sautin kukanta yafita, tana mamakin rashin tausayi irin na rumaisa,
Abban fahad yace "muje koh " ya riko hannun fahad, fahad ya firgi hannunsa daga rikon abbansa yamasa, ya juyo ya kalli rumaisa yace "baki taba yimun ba amma kin nunamin alama, bantaba tunanin imaninki da tausayinki a iya baki kadai suka tsayaba idan aka bukata bazaki iya yiwa mutumba, to Amma wlh inason kisani" fahad yanuna mata dan yatsaya kafin yaci gaba cewa "duk ranar da muka sake gamo dakee..." sai kuma yayi shiru yakasa karasa maganar ya yarfar da hannunsa yana kuka, cike da tausayi,
Abban fahad ya kara janyo hannunsa suka nufi kofar fita fahad sai kuka yake yana fadan "karku rabani da rumaisa wlh itace muradin raina, dan Allah abba kubata hkuri ta amince ta aureni, dan Allah umma kubata hkr" haka yarika jiro kalaman magiya duk ya fita hayyacinsa,
Hakadai suka jasa suka fita dashi, a mota suka sakashi umma ta zauna gidan baya a tare dashi tana lallashinsa, ran abba a bace ya firgi motar da karfi tsiya suka fice sukabar gidan...
Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's
Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:45 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_
_Author_:- *MR, SMILES*😃
67 and 68
Via *OHW*
_A love story_ðŸ’Â
Suna fita abban rumaisa yace "waye kuma wannan a ina kika sansa"
Rumaisa tadan bata fuska kamar batason fada ganin falon kowa ya sakar mata edo, yasa tace " Sunansa fahad, shine wadda yasaceni, akan yana sona" tana karasa fadan maganar ta sunkuye kai,
Falomln gabaki daya kowa yacika da mamaki, hajja luba ranta a bace tace " wannan ai haukane mugun mutum kamar wannan yashigo gidan nan shine bazaki fadaba, meyasa baki gaya mana tun farko shi bane da basai asaka police sukamshiba"
Abban rumaisa yayi saurin cewa "hajiya amma dai bakisan kowauye alhj sani babba bako, ai wannan dakike gani duk kasar nan babu wadda ya isa yakamashi, saidai kawai muyi hakuri tunda Allah yasa rumaisa tadawo lafiya lau, mugodewa Allah"
hajja luba tayi ajiyar zuciya sannan tace "toh shikenan, sai kuma ta dube umma tadan tabe baki kafin tace " ke kuma wlh nasake jin wani tashin hankali yashiga tsakaninki da rumaisa to ina mai tabbatar miki dacewa zamanki a gidan nan yazo karshe" umma tadan share hawaye, domin yanzu nadamce karara a kan fuskarta tace "insha allah babu abinda zai sake faruwa" tana gama maganar tayi shiru,
Hajja luba ta dube abba tace "kai ma ina kara fad'a maka cewa karka kara dukanta kuma karika mata abinda takeso, yarinya karama saiku nemi kusa mata hawan jini"
Abba yayi yake yace "insha Allah hajiya babu wata takura dazata sake shiga tsakanina da rumaisa, yanzu haka sonake tafadamum wata keso, duk wadda takeso to shi zan aura mata, abba yadube rumaisa kafin yace " rumaisa wa kikeso?" Yana tambayar rumaisa,
Gaban rumaisa ya fad'i, ta dago edon tana kallonsu, tanajin yadda zata fadamusu cewa majnoon takeso, jin tayi shiru yasa hajja luba tace " kifada mana wakikeso"
Rumaisa tayi rau rau da edo kamar zatayi kuka, muryarta na rawa ta soma furta " majnoon, abba majnoon nakeso" tana karasa maganar tasoke kanta kasa,
Tunda tafadi kalmar majnoon abba yashiga tashin hankali, yafara tunano abinda yafaru kwanakin baya,
Hajja luba kuwa mamaki yacika kasa hakura tayi saida tayi magana "majnoon fa kikace, mahaukaci kenan"
Abban yayi saurin cewa "eh hajiya wani mahaukacine takeso, nayi kokarin rabata dashi amma taki rabuwa dashi"
hajja luba tamike tsaye cike da masifa tace " wannan ai haukane, niko a tarihi bantabajin mai hankali yaso mahaukaci ba, nima ban goyi bayan a aura miki mahaukaci ba domin wata rana zai iya illataki, meye abinso a cikin mahaukaci mtsw, ni wlh nayi tunanin kinada hankali ashe ke baki hankali ko kadan" takarasa maganar tare dajan tsaki,
Abba ya girgiza kai yana kallon hajja luba yace "kemadai kya fada, meye abinso a gurin mahaukaci, amma babu yadda zanyi tunda kince abata wadda takeso, dan haka shi a aura mata kawai"
Hajja luba tace "ai ko bayan raina bazata auresaba, ni wlh dama nasan akan mahaukaci kike wannna kurciyar da wlh bakisa nabaro sokoto nazo nanba"
Tunda suka fara maganar rumaisa tasoma kuka, hajja luba taci gaba da zabga mata fada, kamar ta daketa, taga rashin hankalin na rumaisa yayi yawa, daga karshe tace "wannan duk kurciyace, dan haka idanma kinada wanda kikeso kifito dashi amma ba mahaukaci ba, idan kuwa bakida kijira zuwansa amma bazamu aurar dake ga mahaukaci ba" tana gama maganar ta dube abba tace "tashi muje kamaidani sokoto, domin ni bazan zauna ina sauraron wannan tatsuniyarba, sanna tasake duban rumaisa tace "ke kuwa idan kika tanace akan cewa sai mahaukaci, to bani bake, karki kara daukata a matsayin kakarki" takarasa maganar tana huci tanufi kofar fita, rumaisa tayi saurin mikewa cike da tashin hankali tashiga gabanta ta durkusa a gabanta tana kuka ta rike mata hijjab " inna dan Allah kiyi hakuri akan abinda nafada, wlh na hakura dashi, zan iya barinsa amma ke bazan iya jurar ganin fushinkiba, saidai inna dan Allah kitayani da adu'a Allah yasa kar ciwon zuciya ya illatani"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.