Trending Hausa Novels

Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Majnoon Part 1.txt

Chapter 18 of 36

Murmushi kadan rumaisa tayi kafin tace "ai banice zan baka damaba, zuciyatace, domin ni ai nagama baka dama tunda har nazo gurinka"

murmushi faisal yayi yace "toh shikenan nikuwa zan nunawa zuciyarki cewa duk duniya babu wadda yake sonta kamar yadda nakesonta"

Hmm kawai rumaisa tace masa, haka dai sukaci gaba da firarsu, duk yayi magana saita bashi amsa, amma dai ta gagara sakin fuskar,

Shikam dai ko a haka suka tsaya yaji dadi sosai, koda ace duk yazo zaginsa take to shikam babu abinda zai damesa,

Sun kusan awa daya suna magana, rumaisa dukta tsargu, wani irin zafi takejin zuciyarta nayi, nan take kanta yadau ciwo, jiri tasoma gani,

Ta mike tsaye kamar zata fadi, tace "banajindadi jiri nake gani,kaje saida safe" bata jira yayi maganaba, tabar gurin dasauri,

Faisal ya mike cike da farin ciki, yadan tabe baki, yace "any way! Gobema zan dawo"

Abba yana zaune a falo umma ta kawo masa abinci yana shirin fara ci,
Rumaisa ta shigo falon, ta dafe kanta da kuma zuciyarta, abba yace "lafiya kuwa "

Kala bata ce masaba takarasa dakinta, da sauri yabiyo bayanta, tana shiga dakin jiri ya kwasheta ta sulala a kasa tana tari da karfi ta dafe gefen kirjinta daidai gurin zuciyarta, tana kuka, hajja luba dake zaune akan sallaya tayi saurin karasawa gurinta tana fadan rumaisa lfy kuwa, koda taduba taganta tana aman jini tsorata sosai hajja luba tayi dasauri ta kwalawa abba kira, a daidai lokacin ya turo kofar dakin yashigo...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:46 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

73 and 74
Via *OHW*
_A love story_💝

yana shigowa dakin yaga halin da rumaisa take ciki dasauri yasa aka daukota suka nufi asibita,

Sa isarsu asibitin Aka kaita emergency room, aka bata taimakon gaggawa,

Umma, abba , hajja luba duk sun tsorota da ciwon rumaisa, ace yarinya harda aman jini,

Bayan wasu yan mituna likita yafito daga cikin da rumaisa take ciki a hargitse, dasauri su hajja luba suka karasa gurinsa, tun basuyi maganaba likitan yace "tana bukatar karin jini da gaggawa domin jini yafita a jikinta sosai"

Abba duk ya firgice da sauri yace "toh yanzu likita yaza ayi kennan"

Cikin gaggawa likatan yace "kuzo muje a gwada jininku mugani ko za a samu wadda yadace danata" haka kuwa akayi suka bi bayan likitan akaje aka gwada jininsu, na umma ne yayi daidai danata, aka kuwa d'ibi roba daya akaje aka sakawa rumaisa

*BAYAN MINTI 50*
likitan yakara fitowa daga cikin da rumaisa take ciki a karo nabiyu, sun abba sukayi saurin karasawa gurinsa,

Hajja luba hawaye take tana cewa "likita meya faru da itane"

Likita ya dube abba sannan yaja nunfashi yace "'yarku tana daf dakamuwa da cutar hawan jini, domin tunani da damuwa sun mata yawa, meyake damunta?"yakarasa maganar da tambaya

Abba ya dubi umma, umma ta dube hajja luba, sukansu basusan meye damuwarba, abbane yayi saurin cewa "muma bamu saniba likiti, saidai idan zata iya magana mezai hana a atambayeta"

Likita yace "ba yanzu, domin yanxu munsamu munyi mata karin jini kuma yanzu haka bacci take bazata samu farkawaba sai nan dazuwa awa daya"

Abba yace " to shikenan zamu jirata, yadanyi shiru har likitan zaibar gurin sai kuma yayi saurin cewa "likita yanzu ya jikin nata"

Likitan yajuyo yayi ajiyar zuciya sannan yace "tasamu sauki, sosai" yana gama fada yabar gurin, abba yadube umma duk jikinta ya mutu yace "mungode da bayar da jini" murmushi kawai tamasa shima yamata sannan suka samu guri suka zauna suna jirana farkawar rumaisa,

BAYAN AWA DAYA DA RABI

Umma tana zaune kusa da rumaisa, rumaisa ta tafarka tana kallon dakin a hankali,

Umma ta dubeta tace "sannu rumaisa ya jikin" bata iya cewa komaiba saikawai bin dakin take da kallo,

A daidai lokacin abba da likita suka shigo dakin, abba yace "alhmdulillah ta farka" da sauri yakarasa gurinta ya fadan "ya jikin" suna hada edo da Abba rumaisa ta fashe da kuka mai sauti saida hankalin kowa a dakin yatashi, hajja luba takaraso ta rike mata hannuwa tana cewa "rumaisa kigaya mana menene damuwarki, meye matsalarki"

Cikin kuka rumaisa tace "inna bazan iya sakaku kumin abinda baku soba, haka nima bazan iya hana zuciyata tunaniba, bazan taba samun salamar zuciba matukar bana tare da majnoon, ta dube abba sannan taci gaba dacewa "abba majnoon shine farin cikina shine kadai wadda nakeso Dan Allah abba kabarni naganshi koda saudayane...." takarasa maganar tana kuka sosai,

Dakin yayi shiru nadan wani lokaci,

Abba yashiga tunanin maganar rumaisa, tabbas 'yarsa ta susuce akan soyayya da majnoon

Likita ya katse mata tunani dacewa " waye shi wannan majnoon din, daman tanada wadda takesone"

abba yasauke a jiyar zuciya yace "eh tanada amma kuma ai mahaukacine, ni banga ribar auren mahaukaci ga mai hankaliba "

Likita yace " idan har yana raye yakamata azo mata dashi, idan har kunason tasamu lafiya, yakamata ace kacece rayuwar 'yarka, ka ajiye maganar hauka gefe, domin hauka zata iya warkewa matukar ba mugun asiri akayi masaba, wasu iyayen suna bani mamaki, duk da sunsan matsalar yayansu kuma sunada maganinta amma saisu kafe da nuna iko da isa, wannan kwata2 bai daceba, nidai shawarata anan itace kanemawa 'yarka lafiya ka ajiye maganar hauka a gefe, ai ko mahaukaci mutumne"

Abba yayi jim yana nazarin maganar sai cen yadube likita yace " yanzu kana ganin zai iya warkewa kuwa "

likita yace " insha Allah zai warke, indai har ba asiri akayi masaba, kagama idan har kayi haka kasamu riba biyu kenan ga ribar taimako, kuma sannan kanemawa 'yarka wadda takeso"

Abba yayi ajiyar xuciya yace "to shikenan zanje yanzu nazo dashi" yana gama fada yanufi hanyar fita
Likita yiyi saurin cewa "yasan fuskar kane, domin kasan yadda suke, basa yadda da sabuwar fuska"

Abba yadan tsaya kafin ya juyo ya dube likita sannan yace "eh yasan fuskana, domin nataba zuwa mukayi hatsaniya dashi sau daya"

Likita yace "tare zamuje domin banason yaganka yafirgita "

abba yace to shikenan muje,

Tare suka fita

Nan suka fita sukabar asibitin sukanufi unguwra da majnoon yake,

Suna zuwa kuwa suka ganshi kwance yana bacci duk ya kara hargisewa, jikinsa har wani tsamin datti yake,

likitan yatoshe hancinsa, sannan suka suka karasa gurinsa,

Abban rumaisa yadan dakeshi kadan, ai kuwa da karfi yafarka,

Cike da firgita suka hada edo da abban rumaisa, da karfi yatashi yana ja dabaya,

Abban rumaisa yace "tsaya kaji munzone mutafi dakai asibiti"

Majnoon yanajin zancen munzone mutafi dakai, ya zura da gudu, abban rumaisa da likita suka mara masa baya suna kiransa amma ko juyosu baiba,

Kan titi yahaura babu ko duban motocin dake zuwa , ai kuwa yana kai tsakiyar titi, naji abba na fadan katsaya mota ga banka, kafin majnoon ya ankara kaji wani karrrrrrrrrrrr......

Note" Aslm, ina mai baku hkr akn gaskiya bazaku jini kwana biyu ba domin banada lfy kuma gobe zamu fara exam, nagode da nuna kaunarku akan novel dinnan"

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:46 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

79 and 80
Via *OHW*
_A love story_💝

Abba yadan zabura kadan dominshi harya shiga duniyar tunani, gyaran murya yayi sannna yafara dacewa "bansan yadda zakaji maganarba, amma yazama dole ingayamaka ita, soboda koda ban sanar dakai ita yauba to tabbas gobe ko jibi zan sanar dakai komai, wannan daka tambayeni waye shi, nikaina bansan waye shiba, kaddarace ta had'ashi da rumaisa, kuma shi mahaukaci ne, tayi mugun kamuwa da sonsa, nayi kokarin naraba dashi amma nakarasa yin haka, sanadin hakan yasa kaga komai yana faruwa ba daidaiba, kamar yadda nasanar dakai a waya cewa muna asibiti, jiyane bayan faisal yabar gidana, rumaisa tashigo gidan a hasgitse, ina zaune a falo naga shigowarta, nake tambayarsa meya faru amma tagagara mun magana, abin ya tsoratani, shine nabi bayansta tana karasa dakinta tafadi kasa a cikin dakin nan fa saita fara aman jini... abba yayi shiru yana kokarin goge wasu gajerun hawaye dake kokarin saukowa kan kuma tunsa,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.