Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels
Reading file: Majnoon Part 1.txt
Chapter 3 of 36
Rumaisa tayi kuru da ido tana kallonsa cike da tausayi, tabbas taga alamun hakan a idonsa domin gasunan duk sun kunbura nunfashi taja kafin tace "kaci abinci yau" ya girgiza mata kai, alamar a a
Tayi shiru tana kallonsa tace "jiya dadarefa " haka yakarasa girgiza mata kai a a"
Wani irin kallon tamasa saida hawayen dake cikin Edonta suka zubo, da sauri tashare sannan takasa hannunta cikin jakarta ta ciri kudi har zata bashi sai kuma ta makale hannu tace "nabaka kudi zaka iya sayen abinci da kanka"
Ya girgiza mata kai yana Murmushi yace "eh zan iya, idan naje wurin talatuwa mai abince sainace tabani, nikuwa saina mika mata kudi"
Rumaisa tayi murmushi tace yawwa, gashi kaje kasiya " tamika masa kudin,
Karbar kudin yayi yana wasa dasu yace sannan yadago kai yana kallon rumaisa yace "kinsan wani abu, Rumaisa tace "a a saika fada "
Ya sunkuyar da kai yace " jiya ina bacci wata mota tatashi takani"
Dam taji gabanta yafadi, mafarkinta yafara dawo mata a kwakwalwa da sauri tace "amma dai bata taka kabandai koh"
Ya girgiza mata kai yace " eh, yana gama fadan haka sai kuma yayi shiru yana wasa da kudin dake hannunsa,
Rumaisa tace "kaje kasiye abincin nizan wuce nakoma gida"
Majnoon ya tsuke fuska bayason tatafi yace " yanzu yaushe zaki dawo" rumaisa tace " sai gobe irin wannan lokacin"
Majnoon ya kalleta saikuma ya sunkuyar dakai yace " bazakizo dadare "
Rumaisa tayi ajiyar zuciya tace "bazan zoba Majnoon domin abbana yahanamun zuwa gurinka "
Dasauri Majnoon yadago kansa yana kallonta yace " abba baya sonane"
Rumaisa ta girgiza masa kai tana murmushi tace " yana sonka mana, kaida zaka aure 'yarsa mezai hana yasoka, tana kallonsa tace " kodai ka fasa aure nane"
Da sauri majnoon ya Girgiza kai yana dariya yace "a a, ina sonki sosai" yana gama fada ya sunkuyar da kansa kasa yana wasa da yatsunsa, shi ala dole yaji kunya,
Yanayinsa yabawa rumaisa dariya,
Baba driver yana a mota sai mamaki yake me rumaisa takeyi a gurin mahaukaci gashi yaganta sai Murmushi take, ta mirror motar ya hangi wata mota a bayansa wadda tayi sanadiyar sakashi firgita fiye da kima, bakinsa na rawa ya iya furta "alhaji"
Da sauri yafito daga cikin motar, yana kiran rumaisa, domin tayi sauri tazo sutafi, tana juyowa yayi daidai da lokacin da abbanta yafito daga cikin motarsa, sukayi edo hudu ko kashe motar bai tsaya yiba, yanufi gurinsu,
Rumaisa kuwa tuni tayi mutuwar tsaye,
Fuskarsa ba annuri kwata kwata, yakarasa gurinsu, kafin yayi magana saida yadauke Majnoon da wani irin wawan mari, rumaisa ta kanne edonta domin bazata iya ganin ana duka Majnoon ba, a dai dai lokacin Hawaye suka sauko kan kuma tunta,
Kafin ta bude idonta itama taji saukari mari tas tas, saida ta ja da baya kamar zata fadi,
Yana dafe da kumatunsa Ganin an mari rumaisa yasa yayi ihu cikin sigarsa ta marasa hankali yayi kan abban rumaisa ya kamo kwalar rigarsa, ya ware hannu zai mazga masa mari rumaisa tayi saurin rike hannunsa tana kuka tace " karka maresa abba nane "
A hankali Majnoon yasaki wuyan abba yana huci,
Abba kuwa gabaki daya ya tsorata, ganin yadda majnoon ya damkesa, indai baibar gurinsaba to komai zai faruwa,
Majnoon ya rike hannun rumaisa, wannan shine karo na farko dataji majnoon yataba jikinta, wani zar taji, ta lumshe ido, tayi mamakin jin hannunsa da laushi,
Abban rumaisa yagyara rigarsa yana huci yace "sakarmun 'ya"
Uffan Majnoon baice dashiba, rumaisa kuwa kuka kawai take, tana fana dan Allah abba kayi hkr wallahi bazan sakeba,
Da karfi da yaji abban rumaisa yashiga Firgar rumaisa daga hannun Majnoon shikuwa Majnoon yariketa gam saikace abarsa,
Nan take mutane suka taru a gurin, da kyar aka iya b'amb'are rumaisa daga hannun Majnoon, mutane suka rirrikesa..
Abba rumaisa ya fincikota tana kuka, yanunawa majnoon yatsa yace "kaiiii dani kakee sa insa" sannan yayi kalci yaja hannun Rumaisa dakarfi yanufi mota da ita,
Janta yake amma tana juyowa tana kallon Majnoon, wanda mutum sama da biyar duk sun rirrikesa,
Rumaisa kuka take sosai,
Abba na karasa bakin mota ya bude kofar motar ya jefata a ciki, sannan ya zagaya ya shiga motar yabar unguwar.
Baba drive duk ya tsorata,
tsoro yakeji kar ya rasa aikinsa...
Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's
Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:35 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_
_Author_:- *MR, SMILES*😃
13 and 14
Via *OHW*
_A love story_ðŸ’Â
Bb driver kuwa Cike da fargaba abinda zai tarar a gida yashiga motar yatada yabar unguwar..
**** *** ****
*FAISAL* yana kwance saman gado ya tayar da edonsa sama yana kallon ginin dakin, edonsa sunyi ja sosai, da duk kan alamu kuka yayi sosai, kaman nunta yafara zayyanowa mai kyauce da fasali, bayajin zai iya rabuwa da ita,
Kofar dakinsa yaji anturo da sauri yashare hawayensa, yana kallon kofar,
Abbansa yashigo cikin shigar kamala, da jikar aiki makkale a kafadarsa,
Basai an fada masa yasan halin da yaronsa yake ciki, domin zai iya kasan cewa shine silar matsalar,
Kallo daya faisal yayi masa ya kauda kansa gefe,
Karasowa abba yayi kusa dashi yana kallonsa, tabbas faisal yana cikin damuwa sosai, murya kasa2 faisal yace "daddy ina kwana" daddy yace "lafiya lau" yadan shiru nadan wani lokaci kafin yayi ajiyar zuciya sannan yace "meyasa baka fito mukayi break fast ba"
"Daddy banajin yunwa" faisal yafada yana kokarin komawa kwnace,
Daddy ya nisa yace " jiyafa bakaci abinciba yau ma haka zaka wuni, kawai aka na hanaka auren rumaisa, nifa cetonka ne nake akan bakin cikin da zaka shiga bayan anyi aure domin yarinyar nan ba sonka takeba, kayi hakuri kacire yarinyar nan a ranka domin ni banzan yarda ka aureta ba" Faisal yayi saurin tashi yana hawaye "daddy dan Allah kayi hakuri, wlh nakasa cire son rumaisa acikin zuciyata, ban taba tunanin zan iya bijirewa umarninkaba amma a yanzu zuciyata takasa hakura daddy" yakarasa maganar kamar mai shirin yin kuka ,
Daddy yayi ajiyar zuciya yana kallon tilon d'ansa faya susuce akan soyayya,
Daddy ya furzar da iska yace "rumaisa bata sonka danme dazaka cewa dole saika aureta, nifa badan MAhaifinta yana amininaba da tuni na dade da tarwatsa wannan lamarin, look faisal, daddy yadafa kafadarsa sannan yaci gaba dacewa "hakuri shine jigon komai kasawa zuciyarka salama insha Allah wata rana zaka manta da ita, kaji faisal" yakarasa yana kallonsa ido cikin ido
Shiru faisal yayi nadan wani lokaci kafin yace " daddy wlh inasonta plx dan Allah kabari na aureta, nikobata sona zan iya zama da ita plx daddy" yakarasa maganar cike da magiya
Daddy ya girgiza kai yana mamakin almarin faisal shi ana gaya masa magana amma ko dauka bayayi, baice dashi komaiba, ya mike tsaye sannan yace "shikenan zanyi shawara akai tashi kaje kaci abinci, saina dawo zamuyi magana" bai jira me zai furtaba daddy yafice yabar dakin, sai a lokacin faisal yaji sanyina zuciyarsa, sannan ya mike tsaye.. soyayyar rumaisa itace a cikin kowanne bugun zuciyarsa a koda Yaushe. ..
*_Waye faisal_*
Faisal d'a daya tilo a gurin mahaifinsa Alhj nura(wato daddy)Yataso cikin gata da azriki, iyayensa suna matukar sonso domin shine kadai d'ansu daya tsaya a duniya, sun haifi wasu yaran kusan hudu amma duk sun rasu, faisal ne kad'ai yatsaya,
Hakan yasa suka dauki son duniya suka daura masa, sun bashi tarbiya akan tsarin addinin musulunci..
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.