Trending Hausa Novels

Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Majnoon Part 1.txt

Chapter 22 of 36

Yana komawa gida yashiga hada kayansa,

Saida yagama hada kayansa kaf Sannan yaje dakin daddy yasanar dashi cewa yanzu zai wuce kogi (lokoja),

Daddy bai hanashi adu'a kawai yamasa yace Allah yakaisa lafiya,

Sannan yajuya zai fita momy ta kwalla masa kira yajuyo, tace "dan Allah faisal karka saka damuwa da tunani a cikin zuciyarka idan kaje cen" yayi murmushi yace "insha Allah momy bazan yi hakanba, kudai kawai kutayi da adu'a"

Nan dai sukayi bakwana cike da kewar juna, sannan yafice yabar dakin

Yana fita harabar gidan yakarasa bakin motarsa yasaka kayansa a but sannan yashiga motar yatada yafice yabar gidan,

Tafiya takeyi yana hawaye duk tunanin rumaisa ya hanashi sukuni, tukin kawai yake amma hankalinsa gabaki daya baya kan tuki,

A hakan yaketa tsala uban gudu akan titi, yafi rabin tafiyarsa dare ya raba sosai,

Ta hasken motarsa yake hango kamar Mutune kwance cikin jini, babu nunfashi a tattare dashi, a yashe a gefen titi, sassauta gudun motarsa yayi harya karaso gurunsa, yatsaya yana kallon mutumen, kamar bazai fitoba,

Jin wurin yayi tsit babu alamar motsin mutum, ko dabba hakan yasa ya bude kofar motar yafito amma har alokacin jikinsa rawa yake,

Yakarsa kusa da mutumen yana kallonsa, babu alamar harbi ko alamar sukar wuka a jikinsa,

Durkusawa yayi a gaban mutumen yadora kunnensa akan kirjinsa, sai yaji kijirin na duka a sannu2, zuciyar mutumen tana harbawa,

Da sauri yamike yana mamakin meya sami wannan mutumen,

Jiyayi yanason yatai maka masa domin yabashi tausayi, kuma mutumen yana bukatar taimakon gaggawa,

Tallabosa yayi yasakashi a motarsa sannan ya shiga motar yatada yabar gurin,

Gudu yakeyi yana juyowa yana kallon mutumen, ko zai farka amma sai yaji shiru.. haka dai yaci gaba da tafiyarsa

Kusan asuba yakarsa cikin garin kogi,

Da shigarsa bai tsaya ko inaba ya zarce asibiti,

Cike da tsoro yakarasa cikin asibitin,

A nan yayi kicib'us da wani doctor yana kokarin fitowa daga wani daki,

Dasauri yasha gabansa, doctor yace "malam lafiya"
Faisal yace "ina tare da marar lafiyane, tun jiya yake a some har yau bai farkaba"

Dr bukar yace "subhanallah yana ina"

Faisal ya nuna kofar waje sannan yace "yana cikin motana "

Dr bukar yace "to yanzu zan saka nurses subiyoka da gado aje a daukosa kafin naje nadauko wani abun a office"

Kai kawai faisal ya kad'a masa

Da sauri Dr bukar yasaka nurse suka janyo gado aka biyo bayan faisal

Suna karasawa bakin motar yiya sauri ya bude musu kofar motar,

Suna ganin wadda ke cikin motar kwance cikin jini suka zare edo, suna mamaki, daya daga cikin nurse din tace " wannan ai Prince Adnan ne " dasauri kaji sauran suna fadan eh wlh shine,

Dasauri suka daukesa aka dorashi akan gado, suka kaisa emergency room,

Dr bukar nafitowa daga cikin office dinsa, wata nurse cikin wadanda suka dauko prince Adnan ta karaso gurin a tsorace, ta sanar da dr bukar cewa ga Prince Adnan cen a emergency room, bayi wata2 ba yabi bayanta suka wuce dakin,

Faisal yana zaune a kujera dake cikin harabar asibiti, har alokacin hankalinsa bai kwantaba duk tsoro yakeji,

Yana zaune har gare ya washe,
sannan likita yfito yana dube2 shi yake nema, dasauri yakaraso gurinsa,
"Doctor meye faradu dashi "

Dr bukar yace "dimuwace da firgita, sai yan wasu kananun raunuka dake jikinsa, amma yanzu komai nomal"

Faisal yace "alhmdullah" yana fara'a

Dr bukar yayi saurin katse masa fara'a dacewa"a ina kasamu sa ne"

Nan Faisal yamasa bayanin komai tayadda yasamu Prince adnan,

Dr bukar ya girgiza kai yace "yaron chief ne na garin nan, kuma shine kadai yaronsa daya rage masa a duniya, gaskiya zaiji dadi idan yasamu labarin kaika taimaki yaronsa, kuma nasan zai maka alkhairi sosai"

Faisal yayi murmushi yace " hakane, amma ni yanzu bashine a gabanaba, inason naje masaukinane na huta domin agajiye nake"

Likita yace "bakomai zaka iya tafiya, amma yanzun nan zan kira gidan chief domin susan halin da ake ciki, mezai hana kabayar da number ka koda mai chief yanemi yasan wanda yatai makawa yaronsa"

Murmushi faisal yayi sannan yadauki numbersa yabawa dr bukar,

Sai kuma yafita yabar asibitin....

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:51 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

93 and 94
Via *OHW*
_A love story_💝

Mamaki yakeyi me photon majnoon yakeyi anan,

Haj zainab tayi gyaran murya

Haka yayi sanadiyar dawowar mai martaba da faisal duniyar tunanin dasuka shiga,

mai martaba ya juyo ya kalli haj zainab,

Haj zainab tace " kullum kazo gurin photon nan saikayi hawaye, yakama murika manta abunda yawuce, tunda wannna yaron ya mutu adu'a itace kadai abinda yake bukata"

Mai martaba yashare hawayensa sannna yace "nima naso nayi hakan amma bazan iya mantawa da Mubarak ba, yatafi yabarni a lokacin da nake bukatarsa, Allah yajikansa da rahama"

Duk falon kaji an kwashi sautin ameen,

Shikam faisal jukum yayi yana mamaki, to idan wannan ya mutu, toshifa wancen daya baro abuja waye shi, kuma shin taya akayi wannan ya mutu, kuma a ina" duk a zuci yake wadan nan tambayoyin, yana so yasan amsar wadannan tambayoyi kafin yabar gidan nan,

A duk lokacin dataga mai martaba yana yiwa photon Mubarak kuka, jitakeyi kamar ta mutu saboda bakin ciki, amma bata nunawa mai martaba hakan, kullum cikin lallashinsa take,

hannun prince adnan taja sukabar falon suka wuce sashensu,

Bayan haj zainab tabar gurin mai martaba yasa aka kai faisal masaukinsa...
***** **** ****

Suna karasawa sashensu, dasauri haj zainab tasa makulli ta kulle kofar dakin ta zaunar da faisal kan gado tana dubansa tace "jiya kana gayamun magana saikuma wayarka ta tsinke, meke faruwane"

Cike da tashin hankali, a lokacin datayi masa tambayar a lokacin ya tuna da yadda yaga fuskar majnoon cikin jini, saida gabansa yafadi sannna yace " umma Mubarak nagani a grin abuja"

Mummunan tashin hankali ya ziyarci zuciyarta, tuni gumi yafara karyo mata, muryarta na rawa tace " Mubarak fa kace, daman bai mutuba "

Prince Adnan ya fashe da kuka cike da tashin hankali yace "ina gudu a mota zan dawo gida, akan titi wani mahaukaci ya hauro titin da karfi,ni kuwa ban anakaraba saina kad'esa, bayan nakadesa nafito domin na dubasa, shine naga Mubarak kwance cikin jini ga dukkan alamu yanzu yamutu, yadan yi shiru yana shanshekar kuka kafin yaci gaba dacewa " tashin hankali dana shiga yasa nabar gurin, tsoro da firgita suka kamani, bayan na shiga mota nakara gudu sosai domin nayi saurin isowa gida ina cikin gudu kuma wata dabba takara karamun akan titi, nayi yunkurin na kauce mata amma nakasa, kukan dukan danayi mata kawai naji amma dagashi bankara jin komaiba, bansan meya faru daniba farkawa kwai nayi naga kaina a cikin ciyawa, da kyar na iya fitar dakaina nasamu nahauro titi , ina haurowa kuma sai jiri yafara dibana naga duniya tafara juyamun nan nazube kasa, tun a lokacin bansan meya sake faruwa daniba sai kawai farka nayi nagakaina a asibiti" yaja majinar data cika masa hanci, yana kuka yashare hawayensa, haj zainab duk tafita hayyacinta, tsintsar fargaba ce karara akan fuskarta, tama rasa mezatace, duk jinin jikinta ya tsaya,

Prince adnan yana kuka yace " yanzu umma idan yaya Mubarak yadawo shikenan nayi asarar sarautar nan, saida komai yazo karshe yanzu kuma kOmai na neman jagulewa..."

Haj zainab tatoshe masa baki ta hanashi karasa maganar, tana girgiza masa kai itama hawaye take "bazamu rasa sarautaba adnan, kaine sarki a wannan masarauta, ai ta yadda muka kawar dashi tsawon shekaru biyu hakan kuma zamu kara karashi lahira, mudin bokana yana raye to insha Allah babu kai babu asarar masarauta, gobe zanje nasami boka zamuyi magana dakai idan nadawo tashi kaje dakinka, karka nunawa kowa kana cikin damuwa"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.