Trending Hausa Novels

Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Majnoon Part 1.txt

Chapter 12 of 36

fahad dake tangadi yace "zonan Rumaisa" rumaisa ta makale kafad'a tana shirin yin kuka,

Fahad yace" bazaki zoba, toshikenan bara nazo ni" yayi taku daya zuwa biyu yana kokarin karasawa gurinta tangadi ya hanashi sandin cafet din yajasa yafadi rakwassss a gurin daidai dani table din da ke tsakiyar falon yafadi, dani table yarabu gida biyu,
Rumaisa ta toshe bakinta takara tsorata ganin fahad kwance cikin glass,

A hankali takira sunansa, taji shiru, dafe kai tayi ta rosa kuka tace na shiga ukku"

Dasauri ta nufi hannyar fita domin yanzu ba bodyguard ko daya agurin, takara bakin gate tana kuka a lokacin mai gadi yafito, da fitila a hannunsa" hajiya lafiya, yana fada yana dalla mata fitilar

Rumaisa tace " fahad zai mutu yana ciki" takarasa maganar tana kuka,

Mai gadi ya tsorata sosai, dasauri yace " hajiya yana ina" rumaisa ta nuna masa kofar shiga falon " yana ciki"

Mai gadin baijira takara magana ba ya zura da gudu yanufi cikin falo,

harta daga kafa zata bisa, saikuma ta tsaya cak, zuciyarta na harbawa tara2, yau gata a bakin gate, kuma ita kadai, ai kuwa bazata watsar da wannan damar ba, dole tabar gidan da sauri takarasa wurin key din kofar tana kokarin budewa, cikin sa'a kuwa yabude, ta tura kofar tafita waje, unguwar shiru kake jinta, tsoro yakata jitakeyi kamar ta koma cikin gidan, wata zuciyar tace "ina ai komai tsoron da zataji gwara tatafi" tayi tsaye a bakin kofar tana kuka.

tambayar kanta take, to ina kuwa zata je, kalaman mahaifinta ta tuna nacewa zai mata aure da faisal kotanaso kobataso, hakan yasa taji batason zuwan gidan, toh ina zataje,

Kakarta tafadi mata a rai, mahaifiyar abba, gurinta zataje domin tana da tausayi sosai kuma tana son rumaisa,

Tohm amma kuma ba'a garin takeba a sokoto take, taya za a yi tasamu motar sokoto a yanzu cikin daren nan, ta tsaya tana nazari...

jin mai gadi yafito yana kiran hajiya! hajiya!! a cikin gidan ta kara firgita, mai gadine yana kokarin fitowa waje..

Rumaisa tace kafa menaci banbakiba, nan ta famtama da gudu tsiya tabar kofar gidan ta ratsa unguwar cikin duhun dare...

Mai gadi na fitowa yaga babu hajiya, kuma kofar gidan a bude abin, yadafe kansa yafashe da kuka, domin yasan dacewa gudu tayi, yafito waje yaleka yaga babuta babu alamarta, kuka yafarayi....

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:45 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

55 and 56
Via *OHW*
_A love story_💝

*NOTE* _ina mai baku hakuri, saida nayi typing ya goge hakan yasa nayi wannan a gurguje, sai kunyin hakurin ganin correcting mistakes, ngd_

"Nashiga uku, yanzu idan oga yatashi yasan dacewa hajiya ta gudu wlh zai iya illatani,wlh bazan zauna a gidan nan ba, dole inje innemota, idan kuwa ban sameta bazan dawo gidan nan ba" mai gadi yafada, Dasauri yashiga dakinsa yafara hada kayansa yana kuka,

saida yagama hada kayan kaf sannan yafito, cike da tsoron kar wani yagansa, ya sulale yafita yabar gidan,

Rumaisa kuwa sharara uban gudu kawai take, ita kanta batasan inda takeba, ballema harta samu hanyar zuwa sokoto,

Daidai wani layi ta karyo kwana, karnuna na kwance a gurin sunaji gudun mutum, suka tashi suka fara haushi, a daidai kwanar tayi kicibus dasu,
Cike da tsoro da fargita ta famtama ihu, daman dai tuncen rumaisa tsoron kare take,

karnukan sukaji ihu ta, ai kuwa nan suka biyota, cab bata mayi guduba yanxu tafarashi domin wani masifaffen gudu danaga rumaisa nayi, nikaina banzaci zata iya yinsaba, gudu take tana kuka, Wani irin sabon karfi yazo mata, su rumaisa anga mutuwa... lol😝

Karnukan na biye da ita suna mata haushi, ita kuwa tana gudu tana kuka ratsa unguwar kawai take bata masan inda takeba, tana cikin gudun kawai jitayi tafada ciki wani rame fancamm!!! saida bakinta yadaki gabar ramen, bakin ya fashe da jini, duk jikinta ya goge, ta duke a kasan ramen tana maida nunfashi,ta toshe bakinta duk da zafin dayake mata amma a haka tadaure, saboda batason karnukan suji kukanta,

Karnukan sukazo gurin sai haushi suke amma basu gantaba, suka yi tsaye a gurin suna sintiri, saida suka gama zagayensu sannan suka bar gurin, saida taji gurin yayi shiru sannan ta saki bakinta shanshekar kukanta kakeji sannu2,

Sai a lokacin tasamu natsuwar duba ramen data fad'a, da kyal ta mike tsaye tana hawaye, duk jikinta ciwo,

Irin ramun nanne na gefen titi, (lamba 2) tana daga kanta kuwa sai taga titi, wata irin ajiyar zuciya tayi tana nishi,

Da gyar ta iya kama bakin ramen, tafito tahau titin tayi tsaye, tana kallon titin gefe da gefe, tsif kakejin tati babu ko motsin lade, a hankali tafara tafiya tana tangadi tare da hawaye, zafin ciwon yasakata kasayin kuka, ta dafe kafarta dai dai gurin dake mata ciwo, tadan jima tana tafiya kafin tafara jin kukan wani ubu a bayanta kamar motace ke shirin zuwa gurin, da sauri ta juyo, tana juyawa kuwa saitaga hasken fitilar mota, tayi tsaye a gurin ta d'aga hannu tana yiwa motar alamar ta tsaya,

Motar bus ce taxi, tundaga nesa driver ya hangi mutum namasa hannu, hankalinsa yatashi duk jikinsa yadau rawa a tunaninsa irin yan fashin nan ne wadanda zasu nemi taimako, idan katsaya kataimaka musu sai kuma suyi maka fashi, tsoro yakashi sosai, yanayinta bai nuna tana cikin natsuba sannan kuma sai yaganta tana hawaye hakan yasa wata zuciyar tace masa yatsaya,

Daf da ita dirver yazo yatsaya, ya kura mata edo yana kallonta, rumaisa tana kuka take fadan "dan Allah malam katai makamun walh saceni akayi" shidai yayi kuru yana kallonta kyankyawar gaskice, a zuci yake fadan "wannan ba mutum bace Aljanace" nan yafara kwararo adu'oi, naneman tsari

Ganin baice mata uffan ba yasa tafara Taku takaraso kusa da motar, a lokacin driver ya dube bakinta yaga duk jini, yakara tsorata sosai, azuci yace "wayyo Allahna yau hadu da aljana mai cin mutane" muryarsa narawa yake furta "kukuke ganinmu bami muke gani kuba, dan Allah karki cutamun wlh ni taimakonki natsayayi"

Rumaisa tace "wlh ni mutum ce kamar kai, idanma baka yardaba ga hannuna kataba kaji" ta zura masa hannun tana kuka,
Jikinsa narawa yakai hannunsa saman jikin Rumaisa, sai yaji laushi,

Yadubeta yayi ta maza yace "malama lafiya meya fito dake cikin wannan tsohon daren,"

Rumaisa ta fashe da kuka tana fadan "dan Allah kataimakeni kakaini sokoto, wanine ya saceni,na samu kubuta daga hannunsa, shine na gudu"

Har a lokaci bai yarda da rumaisa ba leko kansa yayi ta glass din motar yana kallon kafar Rumaisa ko zaiga kofato, sai yaga kaface irin tasa a lokacin ya kara tabbatar dacewa itama mutum ce kamar sa, ajiyar zuciya yayi sannan yace "kwantar da hankalinki, Allah ne yakawo miki ni, domin ni yanzu haka Sokoto zan nufa, ya bud'e mata kofar motar sannan yace "shigo muje"
Bakaramin dadi rumaisa tajiba, tace "nagode, nagode" tashare hawayenta sannan ta zagaya tashiga motar suka lula zuwa sokoto,

A cikin motar yadauko wani tsumma ya mikawa rumaisa yace " ga wannan ki goge jini dake jikinki, kafin zuwa gobe idan mun sauka sai mu nemi clinic agubaki"

Ba musu rumaisa ta karba, ta goge jikinta sannan tasa tsumman ta toshe bakinta dai dai gurin dake fitar da jini,

Divern yadan kauda kansa daga tukin dayake ya dubi rumaisa yace " kekuwa garin yaya aka saceki daga sokoto zuwa abuja"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.