Trending Hausa Novels

Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Majnoon Part 1.txt

Chapter 7 of 36

Nan yaje yanununa mata ko ina a gidan duk inda ta daga ido bodyguard take gani, a zuci tace wannan gidan ba wurin fita saidai taimakon Allah ko ina da mai tsaronsa,

haka dai ya gama nuna mata ko ina sannan, yace shizai fita, sai ya yadawo,

Kai kawai takada masa,

Yana fita takoma kichin tafara dafa abinci...
**** ***** **
Tun wayewar ake tursasawa umma akan tafadi inda takai rumaisa amma umma tace ita wallahi batasan inda rumaisa tajeba" tasha duka iya duka, duk jikinta ya kumbura,

Abban rumaisa yana zaune a cikin police station din, domin anan yakwana tare dashi ake ganawa umma wahala, dominshi a yanzu yama daina jin sonta a zuciyarsa, baya mason ganinta, shidai kawai Rumaisa yakeson gani ko a raye ko a mace,

Edonsa sunyi ja sosai domin bai samu bacci ba jiya, daya daga cikin police din ne yaoi gurinsa yana fadan "alhj wlh matar taki fada, nifa ina ganin kamar ba Hannunta a cikin batan wannan yarinyar"

Abba yadago janjayen Idonsa ya kalli police din yace " taya akayi kasan babu hannunta aciki, kaine mijinta, ko kuma kaike tare da ita, ninasan matata kuma nina baku izinin kamata, dan haka idan zaku iya bincikenta ku binciketa idan kuwa bazakuniyaba tokubarta anan har sai zuwa lokacin da akacemun anga 'yata sannan kusaketa" police din zaiyi magana Abba yadaga masa hannu yana huci "karka kara mun magana, bana bukatar jin kowa a yanzu"

Police din ya girgiza masa kai kawai ya fice yabar gurin, abba yajima a gurin yana tunani kala2 sannan yatashi yaje yaja motarsa yabar station din..

**** **** ****
Nikaina bazan iya misilta muku iya kukan da faisal yayiba, a yunin jiya domin yunin jiya yakasance masa kamar ranar mutuwarsa, yakasa cin komai a haka yuni har dare, a daren ma bai samu isanshen bacciba, domin daya kwanta zai fara tunanin rumaisa, dolensa ya mike..

Wayewar gari

Daga wanka yafito yana goge kansa da tawol, jikinsa duk ba kwari, yakarasa bakin mirror yana kallon kwayar idonsa sunyi ja sosai,

Fusakar rumaisa ta soma yimasa gizo a bayansa tana masa Mumrshi ta jikin mirrorn yake ganinta, da sauri ya juya baya saikuma yaga bakomai, hawaye suka sauko masa, a hankali yasa hannu yashare sannan yakarasa gurin shirinsa, kananun kaya yasaka sunyi masa kyau sosai, sannan yasaka ta kalmi cover, ya janyo jakarsa saida ya kallmasa shirinsa na fita aiki sannan yafito waje....

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:43 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

35 and 36
Via *OHW*
_A love story_💝

Kwata2 fuskarsa ba annuri, a falo yasami momy a zaune tayi jim tana tunani, a lokacin daddy yafita suna cen gurin fafutukar neman rumaisa, faisal ya durkusa ya yagaidata, ba yabo ba fallasa momy ta amsa tana murmushi "har ka shirya fitar ne "
Yace "eh, banason nayi late ne"

Momy tace " toh amma ai baka karya ba, mutum na fita baici abinciba"

Mikewa faisal yayi yana wunkurin barin wurin yana cewa "bana jin yunwa" yana kallon momy, momy tace "to shikenan Allah yakai lfy"

Faisal ya amsa da ameen, sanna yasa kai yafita yabar gidan yanufi gurin aiki,

Katuwar office ce mai matukar kamshi turaren airfrshn yake a ciki ga takardu birjin akan table,

Faisal yana zaune akan wata lallausar kujera, tana juyi dashi, yayi kuru yana kallon kofar office din, edo sa sunyi ja sosai, tunani rumaisa yake, a ranar daya fara gininta, ba zato ba tsammani hawaye suka soma gaggarowa a fuskarsa, yarasa meyasa son rumaisa yakama zuciyarsa har ta yadda bazai iya mantawa da itaba, son rumaisa yazame masa wani irin tabo a cikin zuciyasa wadda bazai iya warke waba, amma duk da haka yana zargin kansa, ayya soyayya baso take ta horar dashiba, ayya ba alhakin soyayyane yake fita akansaba,

Hawaye suka kara saukowa kan kuma tunsa, a zuci yake fadan DAMA HAKA SO YAKE lallai kuwa akwai babbar matsala da wadda yakamu da son maso wani, hausawa nacewa son maso wani, koshin wahala, a hankali naji sautin kukansa yafara fita, da karfi ya daki table dinda ke gabansa, yana kuka yake fadan " why! Why! Why lov, meyasa kamun haka, meyasa ka ingizani gurin da baa sona, plx lov I accpt my fault, nasan nayi kuskure plx...! Yakarasa maganar yana kuka, ya saukar da kansa akan table din yana kuka,

Yajima yana kukan kafin yaji an fara knocking kofar office dinsa, da sauri yake kokarin share hawayensa tare da kokarin gyara kansa,

Saida ya tabbatar daya saita kansa sannan yace "yes com in" murya a raunane,

Tunda aka bude kofar kamshin turaren almiski yadaki hancinsa, yaji wata irin ni'ima tasaukar masa a jiki, ya lumshe edo, sannan yadago kai ya kalli kofar a lokacin da take kokarin shigowa, caraf suka hada edo tana murmushi, takaraso cikin office din ta zauna a kan kujerar dake duban tashi, kyankyawar maccice ajin farko ga kyau ga murmushi mai kyau, (to wacece wannan) nakasa bawa kaina amsa..

Shikuwa ya kura mata edo, gizon fuskar rumaisa yake gani akan fuskarta,
Tayi shuri tana kallonsa, cike dajindadi taga yau ya kura mata edo yana kallonta, ashe dama akwai ranar da faisal zai kalleta haka, a zuci take fadan Allah yasa dai yafara sona, cike da farin ciki tayi gyarar murya, yadan zabura a sannu sannan yadawo hayyacinsa, cike da jindadi tace "kwalliyar ta maka ne"
Sai a lokacin faisal yagane cewa ba rumaisa bace a gabansaba, janjayen edonsa yadago ya kalleta sai kuma ya sunkuyar dakai ya tsuke fuska, uffa bai furta mata ba,

Murmushi tayi tana kallonsa tace " nasan haryanzu cikin tsanata kake, amma dan Allah kayi hakuri, yaufa kwanana ukku kenan bangan kaba, kullum sainaso gurin aiki nayita nemanka, lafiya dai kuwa meke faruawa?"

Shiru yayi mata yamaa kasa dago edonsa ya kalleta,

Yanayin fuskarsa take nazari ga alama kuka yayi cikin salon kisisina ta furta " meke damunka ne dear?, ko anmaka laifine?"

A hankali bakin faisal yasoma rawa yasoma fadan "ZARAH plx liv my office, bana bukatar kowa a yanzu inaso na huta"

murmushi naga wadda yakira da zarah tayi kafin tace "aini dama a kullum baka bukatar zuwana gurin ka, nikuwa gashi nadake sai zowa nake, kuma ni bana ganin laifin kaina domin nasan wannan ba komai bane face sonda zuciyata take maka... tadan marairaice fuska kamar zatayi kuka "dan Allah faisal ka aminta da...."

Da sauri yadaga mata hannu yana huci, kalamanta haushi suke bashi, ya nuna mata kofar fita yace "ki fita nace"
Zarah tayi murmushi takara gyara zama, tana kokarin yin magana,

Faisal ya mike tsaye yadaka mata tsawa, I said liv my office"

Da sauri zarah ta miki a lokacin harta soma hawaye muryata narawa kuka yasoma zomata, hannusa yana nunin kofar office din , tana kuka take furta " zan fita, amma wlh zandawo, kai wane irin marar tasaurayine wadda baisan darajar wadda yake sonsa ba, a kullum burinka bai wuce kaga kawulankatani a gaban kowa, amma ni zuciyata a kullum burinta shine na kyautata maka, kai ne muradina amma kakasa fahimtar haka... ina sonka faisal, takarasa maganar tana kuka tana fadan I love you faisal,

yaji tausayinta sosai, domin a yanzu duk ciwonsa daya, amma yakasa nuna mata haka, kara tsuke fuska yayi "kifita nace " yafada yana hawaye,

Zarah ta firgi kofar office din dasauri ta fita tana kuka, jin karar rufe kofar kakeji da karfi gaff,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.