Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels
Reading file: Majnoon Part 1.txt
Chapter 5 of 36
Da karfi tatashi zaune, caraf idonta yasauka kan fahad dake zaune a gefe yana kallonta yana murmushi,
Firgita tayi ta tallatsa ihu mai matukar kara
Dariya taga yanayi mata saida tagaji sannan tadaina ihun sai ta saka kuka tana fadan " dan allah kayi hkr kamaidani gida "
Murtuke fuska yayi, yana kallonta yake fadan "aikuma keda fita daga gidan saikin haifemin yarana domin kinshigo kenan bake ba fita, naso ace munyi harkar azriki dake kishigo gidan nan amatsayin amarya amma sai kikaki, amma yanzu gaki kinshigo gidan nan a tsayin karuwa kuma bake ba fita, ya mike tsaye sai kuma yasaka dariya sannan yace "barka da zuwa sabowar alawa " yana gama fadan haka yafita yana dariya yamayar kofar dakin yarufe....
Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's
Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:40 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_
_Author_:- *MR, SMILES*😃
21 and 22
Via *OHW*
_A love story_ðŸ’Â
Rumaisa kuwa Kuka tayi
harna fitar arziki itakam tata kaddarar a haka tazo mata,
Data daiga kuka bazai kara sheta da komaiba hakan yasa tadan tsagaita kuka, tatashi tashiga neman bandaki a dakin, cen ta hangi kofa takarasa gurin kofar ta bude, taga ban dakine shiga tayi ta watso ruwa sannan tayi alwala tafito, kayan baccine kawai a jikinta tarasa yadda zatayi tayi sallah, duban dakin take gefe da gefe edonta duk sun kumbura,
Babu abinda tasamu wadda zai suturtata a dakin, fara bincike daken tayi a kasan gado taleka tana dube2,
wani farin kyalle tagani dasauri ta dauko tana kokarinn warware kyalle,
Ware ido tayi tana mamaki a hankali bakinta ya iya furta "HIJAB" mamaki take meya kawo hijab din macce anan, gbanta yayanke ya fadi kardai ace fahad da gaske yake yana wiwa mata fyade,
Hawaye tasoma tana tunanin makomarta, a tsorace ta karkade hijab din tasaka sannan ta karkade kasan cafet din dakin tafara sallah, bata jimaba tagama sallar sannan tarafa kwararo adu'a akan Alllah ya kubutar da ita yasa fahad yakasa aikata komai akanta, adu'a tayi sosai kafin tagama saida tayi kuka,
Bayan tagama sallar tayi zamanta akan sallayar tana kallon dakin, yunwa takeji kamar yan hanjinta zs su fito,
Tashi tayi tashiga nemi abinda zataci, kaf dakin bata samuba hakan yasa ta koma kan gado ta kwanta tana kuka,
**** **** ****
Tunda Abban rumaisa yafita gidan daddy yanufa yasanar dashi komai dake faruwa, lamarin yayi matukar girgiza daddy, saidai yanajin yadda zai fadawa faisal wannan lamari,
Daddy ne zaune a falo shida momy sunyi jugum2 suna jimamin abinda yafaru da rumaisa, sake sake suke kala kala,
Faisal yafito daga cikin dakinsa cikin shirinsa na fita office, farin yadine a jikin filtexs irin mai shara2 dinnan yayi matukar yimasa kyau,
Cikin ladabi da biyayya ya durkusa yagaida momy da daddy,
Ganin yanayinsu kamar da dadamuwa a tattare dasu yasa yakasa hakura saida ya tambaya, duk da shima kuwa tun yafarka yau da safe yakejin gabansaa na faduwa,
"Daddy meya farune naga kamar kuna cikin damuwa" faisal yana kallon daddy yana jiran yabashi amsa , nunfashi daddy yaja yanajin nauhin yadda zai gaya masa maganar, daddy ya kalli momy, momyma haka daddy take kallon sai kuma sukayi shiru,
Faisal kasa fahimtar komai yayi duk ya soma tsorata domin yanaji a jikinsa akwai abinda yafaru,
Ya juya yakalli momy yace "momyna tambaya nake amma kuyi shiru meyake faruwane" momy taja nunfashi kamar zatayi magana saikuma tafasa, daddy ya dubeta yace "fada masa mana"
Momy tayi jim kafin tace "Faisal, rumaisa ta bata, yanzu haka nemanta ake" wani irin tashin hankali yaji ya ziyarci duk ila hirin jikinsa, tuni hawaye suka soma fita a edonsa, kasa yadda da maganar yayi, ya dube daddy yace "daddy idan bazaka amince da aurena da rumaisaba basai kasa ammin karyaba domin karya bata kama cekuba, momy kufa iyayena meyasa bakoson farin cikina"
Daddy ya sunkuwar dakai, wani irin bacin rai yakeji, koda yadagonkansa eedo sa sunyi ja sosai, ya daga hannu ya wankawa Faisal mari, yanaa huci zuciyarsa har wani zafi take cike da masifa yake fadan "so haukane, ko kuka so zai iya sakaka kafada iyayenka magana, idan mun maka karya meye ribarmu...to.to" daddy yakasa yin maganar domin wani irin bacin rai yakeji, Faisal yana dafe da kumatu, yana mamakin wai yau daddy ne yadaga hannunsa ya maresa hawaye kadai ke fita a cikin edonsa, ya dube daddy da momy, muryar na rawa yasomma magana "yaune karo na farko daka fara dukana daddy, badan komaiba sai dan akan innason rumaisa, yadanyi shiru kamar zaiyi kuka, sai kuma yafasa sannan yaci gaba da cewa "bazan hanaka dukanaba domin kai mahaifinane kuma kanada incin dukana aduk lokacin dakasoz, amma bazaka iye cire soyayyar rumaisa a cikin zuciyata ba, idan kuwa kukayi yunkurin rabani da rumaisa ts karfi da yaji to tabbas kuna kokarin rabani da rayuwata ne, kuka yasomayi sannan yamike har a lokacin dafe yake da kumatunsa, kamar zai tafi saikuma yatsaya ya juya musu baya yana fda "idan har kuka rasa wani farin ciki a cikin gidan nan ni zanyi duk yadda zanyi nadawo muku dashi,, ammani abu daya kalilan kukasa cikamun, da kunsan irin yadda nakeji akan son rumaisa da bazaku hanani auren tabs, da kunsan yadda zuciyata kemun zafi a yanzu dabazakuyi yunkurin fadamun wannan maganarba, amma bakomai bazanga laifin kuba amma dai zance kunyi sonkai" yanaa gama fada yanufi hanyar fita,
Momy tani zuciyarta tayi snyi, hawaye take cike da tausayin d'anta daya kasa fahimtar abina suka fada masa, daddy kuwa edinsa sunyi ja sosai yama rasa mezaiyiwa faisal,
Faisal kuwa tunda yatashi tsaye yakejin jiri, yana dibarsa yana kai daf da kofor fita yaji bugun zuciyarrsa yasoma karfi, dafe kirrjinsa yayi yana jan nunfashi da karfi, a hankali ya sulale ya fadi kasa...
Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's
Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:42 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_
_Author_:- *MR, SMILES*😃
29 and 30
Via *OHW*
_A love story_ðŸ’Â
Tana tsaye a gurin tana kuka, a hankali ta sulale kasan carfet, Tana rokon Allah daya kara tsareta daga shairin fahad,
Cike da mamaki Fahad yabar dakin, baitaba jin tausayin macce ba idan yazo kosantarba sai Rumaisa,
Dakinsa ya wuce, ya cire rigarsa, daga shi sai singlet da wandon rigar daya cire, yayi zaune bkin gado, yana maida nunfashi, telephone kawai yakira yasa a odo masa giya, bada jima waba kuwa ma'aikacin gidan yashigo dakin da kwalabe a hannnunsa,
ya zubesu a gabansa sannan yafita, fahad yabude kwalba daya yafara korawa yana lumshe edo, kamannin rumaisa kadai kemasa gizo, yarinyar kara shiga ransa take...
Giyar yasha yayi mankas har kusan karfe 2 na dare baiyi bacciba, tunain rumaisa yahanashi bacci, tashi naga yayi yana tangadi kamar zai fadi, yana sambatu yafita, yana tafiya kamar zai fadi yanufi dakin rumaisa, yana zuwa ya tura kofar dakin yashiga..
A inda yabarta a tsaye anan ta sulala kasa, tayi bacci, tayi sharkar kasan carfet, yakarasa gurinta yayi tsaye a kanta, yana kallonta yana tangadi kamar zai fado mata,
kakin amai yasoma yi hakan yayi sanadiyar tashin rumaisa daga bacci taganshi a kanta, da karfi ta zabura ta miki tana fadan innalillahi wa innalillahi raju un,
Amai yafara kwararowa tana tsaye tana kallonsa, wani irin tashin zuciya takeji kamar itama zatayi aman wani irin kyankyami, tayi mamakin ganin fahad yanashan giya, a take cewa lallai kuwa wannan yana cikin bala'I ga nema mata kuma ga shan giya,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.