Trending Hausa Novels

Majnoon Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Majnoon Part 1.txt

Chapter 24 of 36

Cike da inda2 adnan yace "umma ni bansan mezan masaba"

Haj zainab ta ja tsaki "kai matsalta dakai kenan, komai baka iyaba sai an koya maka, to kawo kunnen ka kaji"

Adnan yayi murmusshi sannan ya tura kunnensa kusa da bakin haj zainab, nan tashiga rada masa magana"

Sundan jima suna maganar kafin adnan yajane kunnensa yana murmushi yace "hakan za'ayi umma"

Haj zainan ta girgiza kai "haba kokaifa,

Sai kuma sukadanyi shiru, suna nazari wani abu , haj zainab tace "yanzu tashi kaje dakin ka kwanta, domin kasamu karfin jikinka"

"Toh" kawai yace mata ya mike tsaye yafice yabar dakin,

Koda yakoma dakinsa bai tarar da faisal ba , a hankali bakinsa ke furta "shikuwa wannan ina yayafi" tabi baki yayi bayan yagamaa maganar, yakarasa bakin gado yakwanta,
â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– â– 

Faisal kuwa bayan fitar adnan, yaga yajima bai dawoba, zuciyarsa ta yanke masa shawara kawai yaje yafada umman mubarak cewa yaga yaronta,

Haka kuwa akayi kawai yatashi yafita, yana dube2 ta wacce hanyace suka tarar da umman Mubarak, yajima yana yawo a cikin gidan kafin yagano hanyar..

Tafiya yakeyi cikin natsuwa da kamala, harya karasa tangamemen falon da umman Mubarak ce kadai a ciki tana kallo photon dake manne a ginin dakin"

Karasawa yayi kusa da ita, yana kallonta yayi murmishi, yaga ita ko motsa edonta batayiba,

Tausayinta yakeji har cikin zuciyarsa, durkusawa yayi kusa da ita ya rike keken guragun datake zaune yayi gyaran murya sannan yace "inada labari akan yaronki Mubarak" yana gama fada sai kuma yayi shiru yana kallonta,

Duk inda jijiwowin jikinta suke saida suka motsa, bugun zuciyarta yakara karfi, yana rike da keken yaji keken yafara rawa a hankali yadago kasan yana kallonta , a daidai lokacin hawaye suka soma fita acikin edonta, a hankali take dago kanta tana kokarin furta magana sai kuma takasa,

Makwogaronta yasoma zafi, tari tasoma yi babu kakkatawa, kamar ranta zai fita, faisal ya mike tsaye cike da tsoro, yana fadan " lafiya kuwa meke faruwane"
Itakam tari taci gaba dayi da karfi sosai harsaida ta fado daga kan keken datake zaune, faisal yace " oh shet" nanfa yaji tafiyar mutanen suna kokarin shigowa gurin.....

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com

[10/20, 10:52 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

99 and 100
Via *OHW*
_A love story_💝

Dasauri ya gudu yasami guri ya labe bayan kofar falon suna shigowa shi kuwa yafita da karfi, da gudu yakarsa dakin da aka saukesa,

Yana shiga dakin yafada kan gado yana sauke nunfashi,

Gabansa sai faduwa yake, Allah2 yake kardai ace shine silar tashin ciwon umman Mubarak, tunani barkatai suka rinka zomasa,

Ma'aikatan nashiga gurin sukaga halin datake ciki dasauri suka je suka sanar da mai martaba,

Cikin firgita ya iso falon ganin halin datake ciki yasa yayi saurin kiran dr bukar domin shine family doctor nashi,

Bada jima wataba kuwa dr bukar yakaraso, yadubata sannan yayi mata allurar bacci, saida ya tabbatar data samu sauki sannan yabar gidan,

Bayan fitar dr bukar, Mai martaba ya dube ma'aikatan cikin bacin rai yace "waya shiga sashenta"

ma'aikatan sukace su wlh basuga kowa yashiga ba,

Ajiyar zuciya kawai mai martaba yayi sannan yace su fice subashi guri, haka kowa ya watse akabar mai martaba shikadai yayi tsaye yana kallon umman Mubarak, yajima yana kallonta kafin shima yafita yabar dakin...

*BAYAN KWANA BIYU*

ABUJA

Majnoon yasamu sauki sosai, sun saka masa suna *kabir* haka suke kiransa, shikuwa yana amsawa,

Suna bashi kulawa sosai, A duk lokacin da akayi masa maganar aurensa da rumaisa, toh komai farin cikin dayake nan take farin cikin zai gushe,

Hakan yasa aka daina masa maganar auren, saidai kullum rumaisa tana tare dashi , abubawa kawai take koya masa, tasamu farin ciki sosai atare dashi,

Yauma kabir yana zaune akan gadonsa na jinya, rumaisa tana zaune kusa dashi, tana masa bayanin yadda ake alwala, har suka kammala, kuma yana fahimta sosai,

Rumaisa tayi murmushi tace "Yanzu dai kasan yadda akeyin alwala saura sallah, tayi gyaran murya, a lokacin suka hada edo tayi masa murmushi shima yamata, sannan tace "ita kuwa sallah idan zaka farata, zaka fuskanci alkibla, tadago kanta ta kallesa tace " kasan meye alkibla" kai kawai ya girgiza mata alamar baisaniba yana murmushi, tace "gabas itace alkibla, tanuna gabas da yatsanta,sannan taci gaba cewa "bayan ka fuskanci alkibla sai kuma kayi ikama...." tana batun fara karanto masa ikama
Sukaji a turo kofar dakin anshigo, suka tsayar da karatunsu, suna kallon mai shigowa, abba ne yashigo da takarda a hannunsa, ya dubesu yayi murmushi yace "saiku tashi kushirya muwuce gida domin likita ya sallamemu" yakarasa maganar yana dariya,

Rumaisa tajidadi sosai, ta dube majnoon tace "kabir zakaje gidanmu"

Girgiza mata kai yayi "eh zanje mana, ai gidanku gidan mune"

Murmushi tayi sannan tace "toh shikenan, tashi kashirya mutafi"

Nan fa suka shiga hada kayansu, umma da haj luba suka tayasu aka hada kayan sannan suka fita, bayan sun fita suka saka kayan a mota, sannan kuma kowa yashiga motar, Abba yaja motar suka nufi gida,

Bayan sunkarasa gida, abba yabawa kabir daki daya daga cikin dakunan dake gidan, tare da nunnuna masa komai na gidan,

Haka dai suka wuni cike da farin ciki da walwala,

Bayan sallar isha, suka taru a falo suna fira cikin nishadi da kwanciyar hankali,

Abba yakatse musu fira dacewa "munsaka ranar auren rumaisa da kabir nanda sati daya, me kukace?"

Haj luba tayi saurin karbe maganar cike dajindadi tace " hakan yayi, domin ni na matsu babbar garin nanba, banaso natafi banga auren 'yar jikan tawaba, Allah yatabbatar mana da alkhairi"

Duka falon suka amsa da ameen,
Rumaisa tana kwance akan cinyar umma, ta rufe fuskarta saboda kunya,

Kabir kuwa yana zaune akan kujera, tunda abba yayi maganar aurensu, yaji kansa na sarawa, kwakwalwarsa nai masa zafi, da sauri ya mike tsaye yabar falon, suduka suka bishi da kallo, sun kasa fahimtar lamarinsa, a duk lokacin da aka dauko zancen aurensu, sai kawai suga ya canza yanayi, wani lokaci kuwa saiya tashi yabasu guri,

Babu wanda ya furta ko uffan, domin inda sabo sunsaba da wannan halin nasan,

Sundan taba fira kadan sai kuma suka watse kowa ya nufi dakinsa...

Washe gari

Abba yasa akafara gyaran daya daga cikin gida jensa, inda rumaisa da kabir zasusha amarcinsu,

Komai na auren abba yayi,

Suna bawa kabir kulawa sosai, duk ya sake jiki dasu, kamar daman cen sunsan juna....

□□□□■□□□□□●□□□●□

KOGI

Umman mubarak tasamu sauki sosai amma dai haryanzu ba abinda ya chanza akan rashin lafiyarta , mai martaba yasa aka maidata falon da take ciki,

Taci gaba dazamanta domin tafison zama cen fiye da ko ina, acikin gidan

Faisal da adnan sun shaku sosai, kullum sai adnan ya fita yawo tare da faisal, domin yasamu ya gusar masa da tunanin fadawa wani labari akan Majnoon,

Kullum suna waje, idan kaga sundawo gida to sai dare idan sunzo bacci,

Kwanan faisal biyu a dakin da mai martaba yabashi,

A rana ta ukku, prince adnan ya umurcesa akan cewa yadawo dakinsa da kwana,

Duk dai sunyi hakanne dandai kawai su gusarwa faisal da tunaninsa daga fadawa wani labarin Majnoon,

Dominsu sunaji a jikinsu cewa shine Mubarak, ba wani mai kamadashi,

Yau dadare bayan sundawo daga yawonsu, dakin adnan suka dire,

Faisal yazaune kan gado yana nishi "waii wlh yau dukna gaji, kasala nakeji" yafada yana kokarin kwantawa,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.