Complete Hausa Novels

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 15 of 33

*LITTAFIN KUÆŠI NAIRA ÆŠARI UKU NE TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0078174806 STARLING BANK, TURO SHAIDAR BIYAN TANAN 08142105218*
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

*23 & 24*

Tunda yagama shagalinshi mukai wanka mukai sallah na hanashi sakat da kukan shagwaɓar dana sanya mai wanda tun ina na hawaye har seda ya zamto na soma wanda bana hawayen ba, shikam baya da aiki se lallashina da bani baki.
Kamar zeyimin kuka! ya É—agoni ya karani jikin gado sannan ya dubeni cikin raunin zuciya.
"Haba Aisha yakamata ki barmin kukan nan haka indai dan na kusanceki ne yasa kike wannan kukan kiyi hakuri bazan kuma anan kusa ba nidai fatana ki daina wannan kukan sabida ze iya haifar miki da ciwon kai"
YafaÉ—a yana mai haÉ—e hannayen shi a waje É—aya alamun ban hakuri.
Amai makon na daina kukan senai ƙasa na xame jikina naja abin rufa na tura hannayena tsakanin cinyoyina na cure guri ɗaya ina cigaba da kukana wanda acikin raina matukar dadi nikeji na yadda na ɗaga masa hankali domin ni a duniya babban burina kenan naga baya cikin walwala.
Aikuwa nayi nasara domin É—unbin baccin gajiya dana wahalar daya É—iba na hidimar aure data makarantar jiya kuka na bai bari yayi shiba sema barmin É—akin dayay a sanyin safiyar nan ya fita shagon abokinshi salim ya zauna kamar yadda yake gayan daya dawo da rana.
*Haka zaman namu ya kasance nida Umari domin babu wata jituwa a tsakaninmu kullum shi yana kokarin yaga ya faranta min nikuma ina kokarin ganin na ƙunta tamai ta hanyar huɗubar Nazir wanda yake bawa sakina saƙo wajena domin koda wasa ban yarda na kula nazir da aure akaina ba domin nasan haramcin yin hakan*
Cikin watanni biyu da bikin mu yay cuku-cukun ganin ya samamin gurbi a makarantar dana baro ta jss ɗorayi da taimakon wani mutumin sa amman na tafi ss one ne kai tsaye sabida ina da kokari tare kuma da girman jiki yasa mutumin ya bashi shawarar yin hakan, sedai koda wasa bai nuna ina da aure ba, To wannan damar dana samu yasa muke yawan haɗuwa da sakina duk da ba ɓangarenmu ɗaya ba sedai abinda ya bani mamaki yadda naga sakina ta kara gogewa tai sabbin kawaye manya waɗanda suka shigo a wannan lokacin.
Dayake ba aji É—aya muke ba kuma nama fita aji yasa haÉ—uwar tamu ba koyaushe ba yawanci ma ita kan zuwa wajena da sakon wasikar yayanta wanda duk ranar da tazomin da ita tofa inta karanta min da kuka muke rabuwa.
A wannan lokacin sam Ya umari yakasa gane kaina gaba É—aya bana basa hakkinshi na aure na daina girki na daina gaisar dashi kullum yana wajan mai shayi yana siya gashi duk zafin ranshi baya min sabida tsananin son dayake min.
Watanmu biyar da aure cif ya biyamin private neco, naje wata makaranta a nan unguwar tamu na zana daga lokacin mukai sallama da sakina sedai mukanyi waya wadda har lokacin bata tako gidana ba shima a wannan lokacin baya samun zama sabida yawan fita aikin ginin sa da kuma makaranta sabida yanxu sun shiga lavel four shekarar karshe wannan dalilin yasa gaba É—aya sena wuni ban ganshiba.
Inka dubeni a yanzu na kara kyau na kara haske kirjina ya cika, shikuma ya kara duhu yay rama sabida wahalar aikin gini ga rana ga jarabata gata makaranta.
Koda wasa kuma bai yarda inna ta fahimta ba tsayin wannan lokaci muna zaman doya da manja kuma ban kuma basa hakkinsa na aure ba tundaga washe garin ranar da aka kawoni kuma shima bai takurani ba sabida yace shi wannan baya gabansa matukar zan zauna lafiya dashi to shiba son sha'awa yake min ba, duk da nasan faÉ—arshi ne kawai sabida nasha kamashi cikin dare yana lalubata, ranar karshene dana kamashi na zuba mai ciwo a kirjinshi wanda wajan yayta zubda jinin dayasa na tsorata da safe zazzabi ya rufeshi wanda yay matukar firgitani seda yaje akai mai allura sannan ya dawo gida.
A takaice yay wajan kwana uku yana jinya kafin ya warke wanda shedar cizon nawa ya fito sosai a kirjinsa abinka da farin mutum.
Tun daga nan ya tattarani ya watsar a haka azumi yazo wanda gaisuwa kawai ke hadamu in ansha ruwa nai É—akin inna nasha acan shiko daman baya shan ruwan gida sabida karatun exam É—insu ta school.
Haka mukai azumin muka gama, da sallah yay kokari wajan kawon kayan sallah da kaji haka yaywa inna da maryam sannan ya sai musu kaji suma haka ya saiwa su anty ma amman abin mamaki ban taba kajin nan ba haka ban taba kayan sallar nan ba seda suka soma wari yazo ya gani a ranar naga masifarsa seda yay kamar ze daken amman fumfurus naki tashi haka ya tattare ya fitar dasu ya dawo dakin ya sakani agaba kamar zeyi kuka.
Ko kaɗan bayajin daɗin zama da humaira amman tsabar haƙurinsa da xurfin ciki yasa bai fallasawa kowa halin da suke cikiba haka nan bai bawa mahaifiyarshi kofar luraba sabida yadda a gabanta yake nuna suna zaman lafiya.
Bayan sallah kamar da wasa na soma ciwon kai wanda baya sauka se dare ganin yanayi na yasa inna takaini asibiti gwajin farko likita ya shaida inada ciki na tsayin watanni bakwai wato tsayin watanni na a gidan mijina inna murna take tana wannan ciki bawan Allah ne wato shi baya laulayi haka ta sakoni gaba mukayo gida babu abinda nike se ƙunci koda yazo aka gaya mai yay murna sosai haka su anty sukazo dubani.
Ikon Allah cikin bamai laulayi bane domin tunda likita ya bani magani nasha ma ciwon kan ya tafi sedai an hanani aiki mai wahala wanda daman banayi.
Domin hatta wanke wanke inna ta saka maryam kemin haka nan abinci sena zaɓa.
Lokaci na gudu kwanaki na raguwa cikin amincin Allah cikina yakai watanni tara cif wanda lokacin suna gab da fita daga makaranta domin sun soma shirin exam's daga nan se tafiya service kuma da sauransu.
Hakan tasa baba yay masa magana akan na dawo gida na haihu badan son ran inna ba na haÉ—a kayana ina murna na koma gidanmu wanda koda wasa bana maganarsa ko yazo senai baccin karya.
Uwa uwace tuni anty ta gane bakin zaran wanda aranar tai min wankin babban bargon daya tsoratani har yasa inyazo nake fita shagon ya imran mugaisa amman daya takuran da magana sena hau kuka.
Wannan dalilin yasa ya ɗauke ƙafarsa a ranar wata lahadi da daddare na tashi da nakuda mai matukar wuya wadda seda na kwana na yini har ana shirin yimin aiki ma, domin harya saka hannu wajan likitan yana kuka cikin amincin ubangiji kuma segashi ana shirye shiryen shigar dani ɗakin tiyata nakudar tazo ganga ganga, inda akai ɗakin haihuwa dani banfi mintuna uku ba na haifo yarinyata mace fara jajur kamar ubanta yay kaki ya amayar.
FaÉ—in wuyar danaci ma bata bakine dayake ban karuba kuma ban fita hayyacina sosai ba yasa a ranar aka sallaman muka yo gida, tun a asibiti ya kama beby ya rike yana kallo kamar ze mayar da ita ciki sabida Allah yay masa azabar son Æ´aÆ´a kamar me.
Sosai anty da umma suka gyarani nida bebyn wadda naji wai tun a asibiti yay mata raÉ—in suna da Aisha takwara kenan.
Wanda abin yay matukar bani mamaki tare da martaba irin son dayake min.
Haka akaita hidima dani wanda ranar suna yay matukar yin rawar gani wajan haÉ—a kayan barka da duk hidimar data dace aiwa mai jego da jinjira.
Anyi taro lafiya angama lafiya yarinyata aisha (islam) kamar yadda su nafisa suka saka mata ta sami kaya sosai wajan mahaifinta da Æ´an uwansa.
Ranar danai sati biyu da haihuwa sega sakina agidanmu sosai nai murna nakaita É—akinmu.
Abinda ya fito a bakinta shine na cuceta na yaudari yayanta yana can ciwon zuciya ze kashe shi.
FaÉ—in tashin hankalin datai min ma bata bakine nidai hakuri kawai nike bata.
Haka taja jakarta ta fita tabarni da zulumi zuwanta.
Maganarta akan nazir tai tasiri a kaina domin yace wai na kaso aure na ze aureni.
Wannan kalamin nata yasa na burkice na susuce kamar wadda aka sammace sam aka kasa gane kaina ko nono na daina bawa islam ko ance na bata sena saka kuka hakan tasa yake siyo madara ana bata domin nonon senaga dama.
Haka nai arba'in na koma gidansa cikin wannan matsalar da anty bata gayawa baba ba haka ta mayar da hankali tana min addu'a.
Banfi wata guda da komawa ba mukaje tofa dangin anty tunda muka dawo na tattare islam nake mikata wajan inna intai kuka akawota na bata nono kaÉ—an na bata madara.
Watana uku da komawa daman sun gama school akai posting É—insa katsina service da taimakon baban nuratu ya sami arewa.
Shikuma ya imran taraba.
Haka muka tarkata mukai can domin inna tace tunda gidane mutafi tare, a wajan tsoho kakansa da iyatu muka sauka ɗaki guda aka bamu wanda aka saka katifa da labule se ƴan kayan tarkace,sosai tsofin suke nunan gata muna waya da sakina inna sami network islam nada wata uku da kwana goma ya kara ribata ta da ƙyar ya sami kaina muka lula.
Wanda nan ma abu kamar wasa banfi wata guda ba na soma ciwo zazzabi ciwon kai kamar zan mutu haka muka É—auki hanyar asibiti gwajin farko nan ma aka ce inada ciki na wata É—aya zokuga tashin hankali wanda seda nai barazanar zubar mai da cikin haka naita zuba masa rashin kirki kala kala batare dayace min komi ba.
Koda su iyatu sukaji sosai sukai farin ciki haka jego ya zaman biyu gana shayarwar islam domin sunce baza,a yayetaba gana rainon ciki wanda daman banawa islam komi shiyake mata, bani da matsalar komi a yanzu seta ganin na zubar da cikin jikina da kuma kashe aurena na fita nazir ya auren wanda hakan yasa na É—agawa kaina hankali na rame na fige shikuma baya da lokaci sosai sabida fita aikin daya ke da kuma rainon yarsa damma kakar tana kama mai wanda zuwa lokacin Æ´ar bata yarda dani sosai se ubanta.
Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji yanxu cikina ya tsufa sosai shima kuma ya kusa gama abinda ya kaishi haka yasa kullum tsoho zemin rubutu ya bani nasha wanda ikon Allah koda nakudar ma tazo ban jigata kamar ta farkoba.
Haka na haifi É—ana shima mai kama da babansa wanda ranar suna yaci suna Muhammadu, sunan baban ya umar kenan wanda ake cemai (aslam) babu wanda yazo daga kano sedai nuratu datazo daga cikin garin,katsina, wadda taita É—aukar yaran tana musu hotuna, sosai tai musu sayayya ta bam mamaki ni daman ban shiga sabgarta ba, haka lamarin namu ya kasance raino ya zaman biyu konace ya zame mai domun shike wa islam komi shikuma aslam iyatu tai mai haka nan rainon su ya koma kanshi shida iyatu wadda ta dau son duniya ta É—orawa aslam nikuwa daman basa gabana sema tsanar yaran data ubansu danakeji araina.
Shekararmu biyu a katsina domin seda ya kammala komi nasa harma muka É—ora watanni sannan muka dawo kano lokacin islam nada shekaru biyu ba watanni domin tana tafiya kuma tana magana wadda da daddy ta budi baki aslam yana tsaiwa sosai yaran suka shiga ran kowa domin tsabar kyansu da wayonsu hakan yasa wasu ma kece masu Æ´an biyu.
Lokacin ya umar bayada sukunin zama sabida baban nuratu yana yawan kiransa a waya yana turashi wajan wani É—an siyasa a nan cikin kano wanda ya kasance aminin sa akan ya sama masa aikin gwamnati domin takardunsa sunyi kyau baida matsala.
Wajan wata ɗaya yana faman cuku-cuku domin har abuja yaje yay sati kafin a kirasu domin duba suna cikin amincin Allah sunan *Umar muhammad sarkin gida ya fito a jerin sunayen da federal government ta ɗauka a ma'aikata na aikin ƴan sanda sedai shi yana ɓangaren sashin bincikene na fararen kaya( DSS POLICE ) wanda zasuna bincikar masu manyan laifuka ( criminal case )*
Sosai nai masa murna daya dawo yake gayan.
"Daman ya umar abinda ka karanta kenan shiyasa senai maka laifi kaimin shuru, kokuma innai abu nace ma banyi ba seka karyatani"
Dariya yay min.
"Aisha wannan aikin na jima da burin yinshi domin bawa ƙasata taimako sedai na ɓoye nemansa ne sabida aikine mai haɗari, naso mun sami aiki tare da imran to Allah baiba domin ba sashin karatunmu guda ba, kuma ni kinga baban nuratune ya sama min to abin alfarma kaima ka samu da ƙyar yasa ban zaƙe da yawa ba".
Awannan karon shuru nai mai sabida banson mu shirya.
Sosai su baba dasu inna sukai mai addu'a akan aikin nashi kafin ranar litinin ta farkon wata ya tafi training wanda seda yay sati biyu sannan suka dawo yazo yay sati biyu gida kana posting letter nasu ya fita inda ya sami aiki a garin Abuja.
Lokacin da muketa shirin tafiya abuja lokacin sakina tazomin da daddare mukai hirarmu daga nan tace min zata tafi.
Tashi nai na rakata amai makon naga ta tafi senaga tanata jana da hira akan tana missing É—ina zanyi nisa da ita, hasken motane ya haskemu a kofar gidan inna kafin naga nazir ya fito daga motar cikin sarsarfa ya karaso gareni yana kuka.
Kokarin riko hannuna yake na doke ina ja da baya.
"Nazir ni matar aure ce akull É—inka"na faÉ—a da karfin gaske amman nazir yaki daina kokarin kamoni harseda ya rikoni yana kokarin rungumeni Ya umar ya doso gidan.
Cak numfashina ya dauke na waiga banga nazir ba kuma banga sakina ba se lafiyayyun marukan danaji a kuncina suna sauka.
Gabas yamma kudu arewa babu su se ya umar dake faman huci akaina idanunshi na zubar ƙwalla.
Jana yay mukai cikin gida ya watsani a É—aki, ya rufo kofar.
"Daman abinda kike nufi kenan dani? shiyasa kika ƙi ƴaƴanki kika ƙini sabida wancan ɗan iskan da aurena akanki kike kula wani ƙato? yafaɗa yana shakoni, wallahi humaira nai nadamar haɗa zuri'a dake kuma kije na sakeki saki ɗaya!!! Hakkina dana yarana baze taɓa barinki zaman lafiyaba kije xaki fahimci wake sonki tsakani da Allah humaira kincu ceni!!"
Ya faÉ—a yana zubewa a wurin yana kuka
Bana fahimtar komi haka na É—auki mayafi na nai gidanmu.
Gurfane nake gaban baba ina kuka anty tana zagina sosai mahaifana suka nuna bani da gaskiya washe gari koda baba ya kirashi ce mai yay baya nan domin ashe tunda asubahi ya hade kayansa dana yaransa sukai tasha yana kuka haka ya isa garin abuja.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.