Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 26 of 33
AISHA.
Da zazzaɓi na kwana na takaicin yankan kaunar da umari yay mini wallahi nasan daman da gayya ya dauken a motar tasa shiyasa naga yanatamin dariya.
Da zazzafan ciwon kai na kwana haka nan dashi na tashi har su anty xulfa sukazo ban fita ba tun bayan sallar asubahi ina ɗaki ina ƙunci,
Lokacin da anisa tazomin da albishir É—in É—aura aurena wallahi seda na zageta dan takaici.
Karfe biyu anty zulfa tashigo dakin da faÉ—a da masifa ta sakani gaba naci abinci sannan ta soma shafamin dilka ajikina.
"Duk anty ta gayamin abinda ya faru to yanxu dai ki sani bake kaÉ—ai gareshi ba a wannan karon inason ki nunawa ita kawar nan taki cewar kema mace ce mai cikakken iko kada ki É—ag mata kafa cikin ruwan sanyi kici durun uwarta! yadda ya kamata daman shi ai karshen cin amana tabewa, shikuwa umar wannan karon shima nuna masa ke mace ce mai aji! kada ki yarda yaga lagonki jawa É—an banza linzami a É—aki karki fito falo da kunci sabida makiya karsu gani su maki dariya sannan waÉ—an nan magun gunan sadidan ne kisha sosai kayan fruit ne aka haÉ—esu da garin madara aka dama da zuma kisha insha Allah zaki sami ni'ima sadidan ajikinki domin seda ita zaki gigita MAZAN"!.
Nidai bance mata komaiba sedai nima a wannan karon na ɗaura ɗammarar gyara ɓarnar danai ada can baya..........
*******
UMAR.
Gamai buƙatar karanta littafina sabo wanda zezo a farkon sabuwar wannan shekara mai zuwa ze biya
*BAƘAR FATA*
(Romantic story)
Norma grp#300
VIP#500
Sp#1000
Complt#1000
Accnt#0078174806 starling bank then show me your evidance of payment ina maraba da masoyana Æ™ashin bayan nasarata one loveâ¤ï¸ðŸ’¯
💃💃💃💃💃💃💯
*INA MARABA DA MASOYANA ONE LOVE*💯💯â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸ðŸ’ƒ
*ZUMA A BAKI* _Is not for free book domin neman ƙarin bayani seki tuntubi wannan numbern 08142105218_
*Albishirin ku masu son karanta Æ™ayatattun labaran soyayya masu narkar da zuciya gami da ilimantarwa da faÉ—akarwa to gada ma ta samu ki nemi waÉ—annan zafafan littatan waÉ—anda aka baje soyayya mai tsayawa a zuÆ™atan makaranta cikinsu*👇ðŸ¼
*AUREN BARE*
*H A S K E*
*KOBA SO*
*DA IZZATA*
*ÆŠAN MAJALISSA*
_Nemi wannan numbern 08142105218 duk É—aya akan farashin naira 300 ne amman idan siya zaki gaba É—aya xaki biya naira 1000 É—aya ne_
*SANARWA TA MUSAMMAN*
*ina mata Æ´an Æ™walisa? shin kokunsan Æ™amshi da gyara shine mace? to matso na baki bayani shahararriyar mai haÉ—a turarukan mata da kuma kayan gyaran jikin mata wato Ummu noor yanxu ma ta kara xuwar muku da xafafan kayan Æ™amshi dana gyara jiki domin kara kankaro miki da martabarki wajan oga ga kayan nata kamar haka*👇ðŸ¼
Turaren wutane
Humrh
Kulacham
Turaren wanka
Turaren Kaya
Gyaran jiki
Na amare
Da masu jego
Da magungun nan mata
Irin su kaza
Tantabara
Tsumi
Gumbar
Zuma
Sauran bayani dai in mutum yamin magana na masa
*gamai neman karin bayani seya kira*👇ðŸ¼
Ummu noor
08067807620
09057713999
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*
*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹
             *51 & 52*
_AFUWAN YAU NAÆŠAN TASHI DA RASHIN JIN DAÆŠIN YANAYIN NE....._
UMAR.
Da wani irin gudu ya shiga cikin Gidan Habu ɗan ƙwai duk da tarin matasan daya gani shaƙe acikin harabar gidan waɗanda kallo ɗaya yay musu yagane abokan hulɗar ɗan ƙwaine sabida yadda yaga sunata faman bankar ƙwayoyin shaye shaye acikinsu.
Wani ne ya hura usir nan da nan wasu ƙattin maza suka takewa umar baya suna cewa....
"Kai! kai!! kada ka shiga kofar nan wallahi ka shiga a ajalinka"
Sarai yana jinsu amman baiko kulasu ba haka ya ƙarawa mansa gudu harseda yakai kofar farko wadda yasa karfi ya doketa akuma dai dai wannan lokacin, yaji ƙarar sautin koke koke! idanunsa ya bude tar akan yaran Alhaji wada mai wake waɗanda ake faman nima fiye da sati uku, tare dawasu yaran waɗanda suma yake kyautata zaton suma ɗin satosun akai domin garkuwa, da sauri kuma ya saita ƴar na'urar vedio camarar dake hannunshi wadda sam bazaka taɓa cewa akwaita ba sabida ƙanƙantar ta cikin mintunan da bazasu gaza ashirin ba ya gama aikinsa ganin waɗannan matasan sun kusan shigowa ɗakin dayake yasa yay saurin bara shure shure kamar wanda baya cikin hayyacinshi a matukar firgice suka shigo ɗakin suna faman nishi sabida akwai tazara mai yawa a tsakanin harabar gidan da ɗakin wanda seda sukasha gudu kafin su shigo nan ɗin wanda wannan damar daya samune yasa ya gama abinda yake batare da sunci mai ba.
"Kai waya baka izinin shigomin gida?"
Habu É—an kwai wanda keta faman nishi yake faÉ—awa umar cikin muzurai.
Dariya umar ya kwashe da ita yana faman soshe-soshen karya kafin ya kaiwa bangon É—akin mari yana mai cewa.
"Hararata kake dan ubanka hararata kake".
Yana cigaba da kaiwa bangon naushi.
"Dallah ku kamashi kuje ku wurgamin shi waje ta yadda baze ƙara gigin zuwa inda nakeba".
Habu ya dubi matasan yana basu umarni kafin kuma ya dubi umar yana mai janyo hannumshi.
"Ƙaton banza ƙaton wofi kaci sa'a kana da taɓin hankali wallahi yau dase dai uwarka ta haifi wani waya gaya maka ana wasa da dodo?".
Maza ku fitar min dashi kafin zuciyata ta sauya tunani akansa.
Umar yana dariyar rainin wayo kamar bai san abinda suke ba yanaji yana gani suka kamasa suka fita dashi yanata dariyarsa.
Cikin amincin Allah suka wurgoshi kofar gida gudun kada su ankare yasa yana tafe yana tsalle tsalle harya karasa hanya kana ya sami napep ya nufi masaukinshi.
Gaba É—aya jikinsa yana masa ciwo.
Tabbas yasan aikinsu mai haÉ—arine amman darajar ceton rai Allah ze karesu.
Ya sauka ya bawa mai napep É—in kudinshi sannan ya nufi cikin hotel É—in.
Cikin kuzari ya kammala kintsa kansa cikin coffee'n jallabiya mai yankan hannu sallar la'asar yay sannan ya nufi wajan frij ya dauko moult mai sanyi ya zauna akan sopa yana sha seda ya kammala sannan ya É—auko laptop É—inshi.
Ya shiga tura manyan bayanan daya samu akan habu ɗan ƙwai.
Sosai bayanan suka girgiza ogansa aikuwa nan da nan ya kira umar awaya cikin girmamawa suka gaisa.
"Mr sarkin gida! naga sakonka amman abin fa yayi mugun É—auremin kai kuma nai matukar baka numbern yabo sabida haka yanzu zanyi report na case É—in zuwa kano idan yaso se a tura musu jami'anmu na can É—in to amman wani hanzari ba gudu ba yana da kyau ayau komi dare ka fita daga kano katawo abuja domin anan É—in zakafi samin safe sabida ina gudun kada kuma su soma bin diddiginka".
Gashin kansa ya hautsina da ɗan ƙarfi! yana mai furzo da huci daga cikin bakinsa.
Lip's É—insa masu azabar ja kamar an sakama janbaki ya shiga tsotsa.
"Oga babu damuwa fa a ko ina nake Allah yana tare dani".
YafaÉ—a cikin rashin sukuni.
"Yes a ko'ina kake akwai ALLAH amman bada ga ni bane daga can saman mune ma'ana hedquater ita ta bada damar ayau ka tattara komi ka komo kodai ka manta daman iya yau wa'adin aikin naka ya kare?".
Lumshe idanunshi yay sam ya manta sabida matsalar humaira.
"Ayyah! wallahi na manta amman babu komi insha Allahu zanzo komi dare".
YafaÉ—a ransa badan yaso ba.
"Okey yanzu sekaje airport sabida akwai jirgin daze tashi daga 6:00pm kano to abuja babu matsala insha Allah tuni angama maka komai".
Murmushi ya sauke mai sauti daman wannan ƙa'idar aikin sune in za'a turaka waje tofa komi naka yana ƙarƙashin kulawarsu.
"Oga kasanfa wancan zuwan da mota na naxo sannan kuma zan tafi da madam ne".
Cikin kulawa yace mai.
"Babu matsala koma dai da wayene karka damu zancen mota kuma ka barta wajan wanda ka yarda dashi insha Allah gobe zan tura driver na ya zo maka da ita".
Godiya yay masa sabida irin mutuncin da ogan nasu kemai lallai daman so gamon jinine wani haka kawai zakaji daga haɗuwarku dashi Allah ya ɗoraka akanshi yana sonk yana kyautata maka, domin gaskiya shikam tunda ya soma aiki wajan suke tare da ogan nasa amman bazece ga ranar daya taɓa bata mai ba sema tarin llkairin dake yimasa.
Duk wannan tunanin zucin yana yinsane bayan sun kammala wayar dasuke da ogan nasa.
Still wayar ya kuma dauka ya soma kiran baba cike da alkunya.
Cikin farin ciki baba ya dauki wayar gaisawa sukai baba ya kuma yi masa fatan alkairi..
"Baba daman wajan aikinmune suka ɓuƙaceni yau sabida haka karfe shidan yamma ma zan wuce ko ita ta gama kintsawa?".
YafaÉ—i hakanne domin a kashe magana domin idan innah ya gayawa zata iya cewa ya bari daga baya shikuwa yanzu yadda ya gaggaji É—innan baze iya dawowa kano nan kusa ba.
Hakama ita kanta humairan yaje mata da maganar yasan halin taurin kanta ƙi zatai ƙarshe ma arabu baram baram.
"To masha Allahu amman kasan yadda abin yazo a bazata ko shiri bamu gabatar ba gakuma hidimar bikin sadiya, sabida haka kaɗan ɗaga mana ƙafa mugama na sadiyar inyaso itan ta tare daga baya tunda bazzawara ce".
Baba yakai maganar zuciyarsa É—aya.
"Haba baba yau koda bani na auri Aisha ba ai baba ni mai yi mata kayan É—akine bare kuma daga hannuna ta fito nine ma zan bada hakurin rashin lefe wanda insha Allah daga baya zanyi mata, amman indai dan kayan gadone wallahi kubari akwaisu wadatattu agidana, sannan itama sadiyan baba nabarine bikin yazo amman wallahi na dauke muku".
Yafaɗa muryarsa can ƙasa kamar koda yaushe.
"A,a umari dame zakaji da hidimar aiko mana da kayan abincin da kakeyi duk wata koko da hidimar karatun anisa dana abba daka dauke mana banda gyara mana gida dakayi sannan kuma kazo kace ka É—auke masu nauyin kayan É—aki inaga hakan kamar bamuyi dai dai ba".
Rintse idanunsa yay har sanda baba ya kammala maganarsa.
"Ya salam baba dame zan biyaka? wallahi babu baba tunda ka dauki AISHA ka bani alokacin da bani dashi baka duba wannan ba, ka dauki mahaifiyata ka rike tare dani da kanwata baka taɓa gazawa ba haka muka taso kamar jini ɗaya! baba wallahi bani da arzikin dazan rama abinda kaimin daga karshe Aisha ta bani abinda har abada bani da kamarshi ma'ana ƴaƴana baba duk duniya kun gama min komai sema hakurin dazan kuma baka na sakin Aisha danai acikin ganganci da fushi wanda insha Allahu bazan kuma ba har abada".
YafaÉ—a cike da alkunya.
Daga ɓangaren baba murmushi ya saki.
"Nagode umari kaji Allah yajiƙan muhammadu mutumin arziki nima har abada bazan manta da mahaifinka ba kuma zuri'ata bazasu manta da alkairin muhammadu gareniba humaira kanwarkace matarka uwar yayanka fatana Allah ya baku zaman lafiya mai dorewa sabida haka bara na sanar da mahaifiyarta ta sakata ta kintsa kayanta daka fito seku wuce kaji".
Wata sahihiyar nutsuwace ta ziyarceshi.
"Nagode! baba Allah ubangiji ya kara maka girma nagode! nagode!!".
YafaÉ—a yana mai katse wayar.
FaÉ—awa saman katifar dake É—akin yay yana mai shafo saman kirjinsa a fili ya furta.
"Yaushe rabon ƙauna.........."
kafin ya mike ya nufi bathroom domin yay wankan tafiya.
AISHA
Cikin sauri anty ta shigo ɗakinmu ina zaune a tsakiyar su fatima ƴaƴan anty zulfa muna ɗan taɓa hira.
Sanye nake cikin doguwar rigar atamfa sabuwa dal, fatima taimin É—aurin ture kaga tsiya.
ÆŠayan hannuna kuwa jan lalli irin na sajan nafisa ke sakamin.
"Humaira ki som haÉ—a kayanki inji babanku anjima kaÉ—an umari zezo ku wuce.............
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.