Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 33
Sosai na haÉ—e raina tamau na kame jikina waje É—aya kaina sunkuye haka nazo gab da su zan gifta araina nake ayyana da ranar Allah amman bazasu huta ba.
Sautin dariya naji daga bayana kafin naji fitar sautin É—aya daga cikin samarin wajan.
"Waini kam B.smoll wannan ba tagidan su ƙwaro bace?"
Ina jin wanda aka kirawo da b.smool É—in yace.
"Sosai ma ai yayar ƙwaro ce ƴar gidan yayan babansa ce shegiya mai baƙar fuska se uban girman kai kullum haka zaka ganta kamar ta faɗi, ita bata yarda ba ƴar boko, se tsabar baƙin jini duk ƙannenta sunata ɗagawa amman ita har yau babu wanda ya taya"
Banji abinda ɗayan ke cewa ba na ƙarasa gaban gidanmu.
Dab da zan shiga xauren mu naji hayaniyar su na tashi.
"Se OGA CIKA DAJI"
Haka naji majalissar tasu ta kaure da faÉ—i wanda sautin muryarsu tayi dai dai da sautin bugun zuciyata...............
SANNU SANNU..................✊
*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }
NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*002*
Da gudu na ƙarasa shiga zauren gidan namu sabida yadda numfashina yake ƙoƙarin ɗaukewa.
Cikin sauri na faɗa tsakar gida kamar wadda aka jefa ina shiga nai ɗakinmu tare da banko ƙofar na zauna turus a bakin gado ina mayar da numfashina dake barazanar ɗaukewa hawayen da suka sami zarafin zubo min a yanzu sunake saka hannu ina gogewa.
Cikin dakakkiyar muryarshi mai cike da amo!
Yake doko sallama tsakar gidan namu kafin naji sautin takalman dake nuna min alamun bashi kaÉ—ai yashigo gidan ba.
Cikin murna da farin ciki anty dake cikin É—akinta take amsa mai sallamar kafin naji muryarta a tsakar gidan tana cewa.
"A,a lale maraba da mai gidana da kishiyata yau kace manyan baƙi gareni ku shigo mana UMAR"
Anty ta faÉ—a tana mai nufar É—akinta da sauri domin shin fiÉ—a musu tabarma.
Jin kalamin anty yasani tashi kamar an mintsi nan na nufi gaban taga ina lekensu domin tsananin tsoro baze barni na leƙasu ba.
Gabana ne yay muguwar faÉ—uwa sakamakon idanu biyu da mukai da SANYIN IDANIYATA.
Hawaye ne ke ƙara zubomin a saman fuskata kafe islam nai da idanu ina kallonta yarinya mai shekaru biyu a duniya amman inka du beta seka ce ƴar shekaru uku, kafin na mayar su kan aslam ɗan uwanta wanda yake riƙe da hannun babansa dake sunkuye yana tube takalman shi ze shiga ɗakin anty.
Zuciyata ce tai rauni gaba É—aya komi ya tsayamin cak hatta yunwar dana zo da ita ta gushe bakina ya bushe babu abinda nake muradi kamar in ganni gaban Æ´aÆ´ana da Allah ya bani amman kash hakan nasan baze yuwu ba domin na riga nabar kari tun ranar tubani.
Tabbas Nazir ya cuceni ya lasa mini ZUMA A BAKI wadda har abada bazan daina la'antar shiba, ya rabani da farin cikin rayuwata wanda har abada bana zaton zan sami farin ciki in bana tare dasu.
Tabbas na tafka babban kuskure acikin rayuwata UMAR ya lasan ZUMA A BAKI na soyayyarshi Nikuma na mayar masa da tawa ZUMA A BAKI'n ta yaudarar mu ta mata tabbas nasan har abada umar baze manta dani ba har abada umar baze taɓa dawo da soyayyata rayuwar shiba.
Na cuci kaina gashi har wasu mazan na min kallon mai baƙin jini sabida ƙaddarar data faɗawa Aurena.
Tsaye nayi a wurin kamar wadda aka dasa inajin yau koze daken bazan fasa tin kararshi akan ya bani Æ´aÆ´ana naji É—umin suba.
Yafi mintuna goma a ɗakin anty kansa sunkuye a ƙasa yana kallon ledar dake tsakar ɗakin.
"Amman dai zaka bar mana su islam su É—an kwana biyu kafin ka koma ko?"
Anty ta faÉ—a mai tana mai É—ora aslam saman cinyarta.
Rintse idanun shi yay yana mai fesar da hucin dake fasowa daga maƙoshin sa sam baya ƙaunar nesa da yaranshi haka nan baya son wata alaƙa da kuma shiga tsakanin shi da Aisha wannan dalilin yasa a kullum yake nesanta kanshi gareta.
Zuwanshi ma nayau ya samo asaline da yadda inna ta uzzira mai akan seya kawosu bada ban hakaba da baya tunanin ze kawo Æ´aÆ´ansa gidan anan kusa.
"Umar bakaji nane?"
Anty tai maganar tana kallon shi cike da tausayawa.
Ɗago da jar fuskar shi yay mai kama data turawa sabida yadda Allah yay mashi azabar kyau da jar fata kana ya zuba mata manyan idanunshi waɗanda atake anan launinsu yay mugun sauyawa cije ƙasan laɓɓansa yay tare da cewa.
"Ai suna makaranta amman in akai hutu zan kawo su".
Yafaɗawa anty hakane sabida jin daɗinta amman a ƙasan zuciyar shi bayajin hakan zata faru.
Tashi yayi tsaye tare da zaro damin kuÉ—i a cikin aljihun wandon jeans É—inshi ya dire gaban anty.
"Gashi anty a saima yara wani abun ni zan koma agaida su baffa se watarana"
Sunkuyar da kai anty tai kasa tana mai kallon uban kudin dake gabanta.
"Haba Umar wannan kuÉ—i ai yayi yawa dan Allah ka dauke kana fama da nauyin iyali ai baka bada wannan kuÉ—i hakaba".
Shi dariyama kalamin nata ya bashi amman seya basar.
Tare da sunkuyawa ya É—auki aslam daman islam batada yarda shiyasa bata ko nufi inda anty take ba
"Anty mun gudu a gaida sauran".
Yafaɗa yana mai saɓar ƴaƴanshi yabar ɗakin cikin sauri.
Kasa magana anty tai tana bin kudin da kallo lallai arziki nufin Allah humaira ta cuci kanta da tuni itake da wannan daular.
Ganin fitowar su yasani komawa da sauri na É—auki gyale na rufa akaina nabi bayanshi.
Seda na haÉ—a da gudu sabida daman can ya umar yana da mugun sauri, koda na fita yama bar kofar gidanmu yana tsaye agaban dandazon matasan É—azu yana raba musu kuÉ—i suna fama ihu suna masa godiya.
Ina laɓe yagama musu rabon kuɗin ya nufi kwanar gidansu.
Da sauri na gyara mayafina na nufi inda naga yayi baki É—aya jikina rawa ike idanuna ko gani basayi.
Koda nazo zan gifta wannan majalissar ta É—azu senaji wani daga cikinsu yana cewa.
"Kunga Æ´ar wahala kun san wata kebi haka?"
ÆŠiff naji sunyi se sautin saurina dana muryar wannan matashin danaji yana kora musu bayani kamar haka.
"tsohuwar matar CIKA DAJI cefa ta rabu dashi yanzu kuma taga yayi kuɗi take faman binsa kamar zata tashi sama ai ƴar wahala kenan ta ɗorawa kanta girman kai shiyasa tunda ta fito babu mashin shini se faman zaryar koyarwa a ƴar ƙaramar private shiko oga ai yacigaba kuduba fa motar dayake hawa yanzu?"
Dariya suka kwashe da ita banji sauran ba nidai na nufi inda zuciyata take muradin zuwa.
Yana ƙorarin shiga gidan inna domin harya tura madai dai cin gate ɗin gidan nai saurin ɗora ƙafata kan dakalin gidan cikin rawar murya data zuciya na furta.
"Yaya dan Allah ka bani su nima suji ɗumina irin na mahaifiya ka tuna nima ina da haƙƙi akan ƴaƴana nifa na haife su kaiwa girman Allah kabani yarana"
NafaÉ—a muryata tana rawa ina kokarin mika hannuna wajan islam domin a yanxu ita nafi mai tar so fiye da komai....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.