Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 9 of 33
*ZUMA A BAKI*
300 Naira masu amfani da banki zasu tura ta 0078174806 starling bank.
Shaidar biya ta 08142105218.
Marasa banki kuma katin MTN na naira 400 ta numbern dake sama.
AUREN BARE COMPLT #500 anemi numbern dake sama gamai so.
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*
*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹
*11&12*
Haka na bita jikina babu ƙwari har zuwa tsakar gidanmu wanda ya cika da maƙota tare da ƴan uwanmu.
Gabana bai kuma faɗuwa ba seda naga ta miƙani cikin hannun Ya Umar wanda yake tsakiyar abokanshi fuskar nan tashi ta ƙara haskawa tai wani irin cika da annurin angon ci.
Hannu na ya damƙe da ƙarfi yana matsamin shi batare dayaji kunyar anty uwani ba yaɗan janyoni jikinshi abokin shi yaja mana hoto.
Haka yayta rungumeni ana mana hotuna wanda rabin hoton kukane harda majina a fuskana.
A fakaice yake saka hannunshi yana sharemin har aka gama kana muka shiga É—aki akai mana tare da ayiya da anty da su umma.
Fafur yaƙi yarda ai mana da abokanshi haka suka kammala gaisuwar su suka wuce waje zuwa anjima kuma azo ɗaukar amarya.
ÆŠakinmu na nufa aguje! hayewa nayi saman gado ina rafka kuka.
Cikin tsananin tashin hankali sakina ta shigo É—akinmu jikinta da kayan makaranta.
Zubewa tai saman katifar danike kwance tana hucin bala'i!
Ɗakamin duka tai a saman bayana da sauri na miƙe ina sosa wurin ina kallonta.
"Wato humaira munafunta ta kike ko? daman kinsan yaudarar ɗan uwana zakiyi yasa kika lasa mai ZUMA A BAKI! na soyayyarki daman auren ƙato zakiyi?"
Tafaɗa tana zubar da ƙwallah!
Cikin ruɗu na miƙe sosai ina kallonta nima a wannan karon na kasa daurewa kukan na saka kamar ita.
Kana cikin tattausan lafazi na dubeta.
"Haba sakina tayaya zakice bani son Nazir bayan kinsan sonsa ajininah yake?".
Nisawa nayi na daƙiƙu kafin nace.
"Wallahi! shigar sauri sukamin,sakina bansan da auren nan ba domin raina zuciyata a halin da ake ciki yanzu sunfi naki tafasa domin bana son wancan matsiyacin ko kaÉ—an".
NafaÉ—a ina hucin takaici.
"Tayaya zan musawa mahaifana dole na amshe sa a hakan duk da banji sonshi ko guda a raina".
Zabura tai tare da mikewa tana huci!
"Haka ma zakice kenan xakije ne ki bashi jikin ki kome?"
Sekuma ta zube akan gwiwo yinta ta kama nawa hannun.
"Dan Allah humairah kada ki bashi kanki ki adanawa yayana kanki kinga mu yarane bamufi shekaru 16 ba tabbas kika yarda dashi ze sakaki yoyon fitsari".
Da É—imuwa na dubeta ina zare idanuna.
"Daman ko baki ceba ni ina zan iya da wannan ƙaton tabbas ya shigeni mutuwa xanyi tabbas zanyi iya karfina domin ganin na kare kaina".
Murmushi ta sauke tare da jinjina kanta.
"Meze hana ki É—auki makami ayayin dayazo kusantarki ki masa barazana?"
Da sauri na dafata.
"A,a sakinah babu ruwana domin bana son duk ƙina dashi nai ajalinshi baki gudun rai yazo ya tarar da ajali nazo na shiga uku? tabbas bazanyi haka ba inawa mata ma masu yin hakan addu'a akan su dena domin ba ɗabi'a arziki bace ba sabida gudun tsautsayi suzo rai yay halin shi agarin son zuciya nidai ba ruwana sauya wata shawarar".
Wani shegen murmushi ta saki.
"Kai daÉ—ina dake akwai kwanya kawata to ki dinga karta mai tujara da cin zarafi aduk sanda zezo miki har Allah yasa yaji yagaji dake ya sakeki yayana ya aure ki".
Murmushin nima na sauke.
"Aikam gwara haka, akan nai masa bazarana domin wannan matsala ce gagaruma".
Sakina ranta tai jin bazanci amanar yayanta ba.
Sosai mukacigaba da hira wadda rabinta akan, yadda xan kuntata wa rayuwar aurena da ya umar take.
Se lokacin ma na tuno da wayar da nazir yabani wadda na cusata cikin kayana.
Da sauri na É—aukota sakina ta saitamin ita kiranshi mukai.
Seda sukai maganganun su da sakina sannan ta mikomin wayar.
Kukanshi na gulma ya soma reran yana cewa duk sanda yaji labarin na bawa Umar jikina tabbas ze kashe kansa ya huta.
Da irin waÉ—annan mugayen kalaman ya ribacen wanda harna manta da igiyar auren dake kaina(wa'iyazu billahi)har nai masa alkwarin tafiya da wayata gidan mijina akan muna magana dashi.
Sosai ya kasheni da kalaman soyayyar shi harya Lasa min ZUMA A BAKI wadda ta kaini ga na sallama mai zuciyata na kuma ji duk duniya babu wanda ya isa ya rabani dashi.
Naji kuma duk duniya bani da maƙiyi kamar Umar.
Seda na saka nafisa ta kawowa sakina abinci taci sannan mukai sallama ta tafi akan setazo gidana.
Waje mai mahimmanci naiwa wayar a cikin kayana.
Ina nan zaune anty zulfa tazo tana cemin sunyi jere sedai ban sami falo ba dan haka gado kawai aka saka da suf a É—akin kujerun kwa suna waje za,a mayar dasu wajan kafintan domin babu wuri.
Kauda kaina nai ina ayyana matsiyaci daman ai fitina ce zata sakashi yay auren amman meyake dashi mai kuma ya tanada daze iya rikeni yana ta karatun shi ga hidimar gidansu.
Katsemin tunanina tai.
"Humairah ki rike Umar da kyau domin zakiji daÉ—in shi sabida yarone shi mai zuciya zokije kiga lefen daya haÉ—o miki wallahi duk duniya zama da mai sonka yafi komi daÉ—i ina kyautata zaton nan gaba Allah zewa Umar É—aukaka sabida darajar kyautatawa mahaifa".
Duk abinda take faɗi bayamin daɗi sema ƙaramin wutar ƙiyayyarshi datakeyi haka nan ban motsaba harta gama ta fita.
Sema kifa kaina danai a saman kafita ina kuka wanda ya haifar min da ciwon kai mai zafi.
Ina jin ana kiɗan ƙwarya a ƙofar gida amman ban leka ba ana magariba nai sallah na koma na kwanta.
Baba ne ya aiko kirana saka mayafi nai na fita zuwa É—akinshi.
Anan na tarar dashi dasu anty zaunar dani akai agabansu nasiha baba yakemin akan zaman aure da sauransu kafin anty itama ta É—ora da tata baffama haka haka nan umma sannan su anty uwani suka É—agani wanka suka kuma sakani nai sannan aka bani rigar leshi ja na saka sosai suka shiryani nai kyau kai gaskiya Æ´an uwanmu akwai zumunci.
Mota guda É—aya aka kawo sabida kusane dan haka dagani se umma da anty uwani aka zuba cikinta.
Har aka shigar dani gidan inna kuka nike kamar babu gobe.
ÆŠakin inna aka kaini inda danginshi suka karban hannu biyu inna da kanta takaini É—akina.
Zaunar dani tai a bakin katafaren gadona, É—akin yana bada kamshin turare na musamman.
"Toni dai bana suruka dake domin ke Æ´atace Allah ya bada zaman lafiya".
TafaÉ—a da murnar ta domin yau jinta take a farin ciki yaro yay aure.
Sosai Æ´an uwanshi suka cika É—akin suna faman tayani murna har su umma suka tafi ban saniba.
Basu bar É—akin ba se wajan goman dare seda su maryam suka share É—akin suka kuma kunna turare sannan sukaimin sallama suka tafi É—akin ya rage dagani se halina
Haka nan gidan yayi tsit alamun mutan gidan sun kwanta domin garin yanayin sanyine wanda daman tun a É—akina naji suna cewa zasu jesu kwanta da wuri sabida gobe zasu wuce katsinah.
Haka na cure a wuri É—aya duk tsoro ya kamani.........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.