Complete Hausa Novels

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 33

Yauma cikin sanyin jiki na dawo daga makaranta.
Umma da anty suna zaune a tsakar gida.
Sannu nai musu tare da shigewa É—aki.
Anty ce ta É—aga baki ta kirani akan naxo naje gidan inna na siyo kubewa sabida inna ire iren kayan da take saidawa ne.
Tura bakina nai gaba alamun bazani ba.
Sannan na fito ina kuncin rai.
"Ni Allah anty bana son zuwa gidan inna".
Zaro idanu tai tana kallona.
"Sabida maƙiyinki yana gidan ko?"
"Waini humaira a ina kika koyo wannan bakin halin shin mai Umar yay miki haka kike nuna ƙinsa a ko ina bayan kuma baki fasa amsar abin hannunshi dana mahaifiyar shiba, maza kama hanya kije kuma sauran ki nuna halin wallahi babanki ya dawo na gaya masa ko yayanku"
Jin abinda ta faɗa yasa na kama hanya ina ƙunƙuni na nufi gidan inna............

*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }

NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*005*

Cikin rashin sukuni nakama hanyar gidan inna, ina tafe ina share zufar datake faman karyo mini ta saman goshina sabida zafin ranar da ake faman yi a garin.
Ƙofar gidan na tura tare da doka sallama cikin sauri-sauri sabida yadda nake gudun haɗuwa ta dashi domin yanzu ya zamame min kamar dodo.
Sanin a wannan lokacin za'a iya samun sa a gida domin naji anty tace zata haÉ—ani da yayanmu tunda naji kuwa ta faÉ—i hakan nasan cewar yau basu fita aiki ba kuma basuje makaranta ba.
Jin shiru a tsakar gidan yasa na ƙarasa ciki ina cewa.
"Innah Barka da rana inata sallama baki amsa ba ko sallah kike?"
Nafaɗi hakan ina mai Kama labulan ƙofar ta Tare da zura kaina cikin shi da sauri kuma na saki labulan ina mai matsawa baya sabida mugun ganin da idanuna yayi.
Kwance naga yaya Umar a ƙasan ledar tsakar ɗakin inna daga shi se gajeran wando irin na maza jikinshi babu riga ya ɗora hannun shi a saman cikin shi yayi wani irin lako kamar marar lafiya.
Tunda nike ban taɓa ganin jikin namiji a haka ba wannan dalilin yasa gaba ɗaya na shiga halin tsoro da furgici wanda ya baiwa ilahirin jikina damar ƙaɗawa kamar mazari, jin shurun danai alamun kamar bai san da shigowa taba yasa na mayar da ajiyar zuciya tare da salallaɓawa nabar tsakar gidan na nufi bakin ƙofa cike da saurina
Kaina sunkuye zan buɗe ƙofa naji Muryar innah kaina.
"A,a wanake gani kamar humairah?"
TafaÉ—a tana mai shigowa ciki inda nikuma nabata wuri domin ta shigo ta hanyar matsa mata.
"Ina wuni inna?"
Nafaɗa ina mai rissunar da kaina ƙasa.
"Ke kinci gidanku, Ni zaki gaisar a soro sekace ba ƙuwa maza shigo, ciki ɗan uwanki ne babu lafiya cikin shi ke mai ciwo nikam narasa irin wannan ciwon na yaro! Yanzu dai muje ki matsa mai lemun tsamin nan koze sami afuwa"
Tafaɗa tana mai shiga ciki haka na bita ina ƙunƙuni kamar bakina duka ze faso waje.
Tsaye nai a tsakar gidan.
"Nifa inna nifa aikoni akai kuma yunwa nike ji".
Na faÉ—i haka ina Mai turo bakina gaba.
"Aiko ko kafi yunwa kike ji sekin matse mai lemun nan yanzu inda kece baki da Lafiya da tuni Yana nan ya addabi kowa".
Gabana ne ya faɗi dajin furucinta uwa! Uwace ko da wasa bani son inna ta shaida ƙin da nikewa ya Umar wannan dalilin yasa nai dariya domin na batar mata da tunanin ta.
"Kai inna Nima fa bance komiba ina kofi da wuƙa, na matse Mai?" .

Nafaɗi Hakan ina mai sakin murmushin yake, da kanta ta nufi kicin ta daukomin kofi da wuƙa sannan ta miko min.
"Ungo yan ka mai ki basa Ni Kuma zan leka shagon can na siyo masa Lipton da suga adafa mai ruwan shayi sabida tun safe baici komiba".
Amsa nayi tare da nufar É—akin, na zauna daga gefen shi ina yanka lemun.
Se Lokacin yasami zarafin mikewa zaune kallo guda nai masa na kawar da fuskata.
Sabida Yadda naga idanun shi da fuskarshi sunyi wani irin jajur, Gaba É—aya jinai zaman É—akin Ya gun direni sabida Yadda Naga ya zubo mini idanunshi batare daya cemin komiba.

Ban tanka Shiba bare ya saka ranshi cewar zan masa magana, bare har akai da ƙadamin nayi mai sannu na halin dayake ciki.
Saboda huɗu bar sakina ƙawata aminiyata Wadda take cemin matar ƙato har Wasu daga cikin yan ajinmu sukaji, suke faɗa Min hakan, gefe guda Kuma tai min tayin soyayyar yayanta nazir wanda kallo guda nayi mashi naji ya sacen zuciyata duk da shekaruna Basu kai da soyayya ba amman yadda sakina ke ƙarfafamin zuciyata da kuma huramin wutar son yayan nata yasa naji kaf duniya babu kamar shi dakuma wannan damar naji kaf duniya babu makiyina kamar ya Umar,duk da yadda ike tattalina amman Ni kalaman da sakina ke zuwar min dasu a matsayin na yayanta da kuma kushe ya Umar datake min yasa naji nafison nazir akan Umar sau dubun dubata.
"Nurinah bazaki min sannu ba kina ganin halin dani ke ciki?"
Naji Muryar shi Acikin dodon kunne nah, wadda take adashe kamar Mai cutar murah.
Wani Irin tafasa naji zuciyata nayi min komi ze min a yanzu bana Ganin farin shi ganin farar Fatar jikinshi nike kamar baƙin tukunya.
"A'ishah! Wai mike damun rayuwarki kwata kwata nakasa gane miki nifa senace tun da kika soma girma kika shiga secondary Naga kin Soma sauya mini ko ƙawaye kikai masu zuga mini ke?"
Ya fadi hakan Daga gani cikin kokari yake Maganar saboda yadda naji yana mayar da numfashi akai akai.
"Nifa ya Umar Babu Mai zugani kawai zuciyata ce naji bata sonka inda Zaka taimaki rayuwata daka rabu dani daka janye maganar aurenmu dakai, saboda koka auren baka da zuciyata yaya kaje ka cewa su baba su tsinke wannan alkawarin na aure da suka É—aura a tsakanin mu abaka nafisa ko sadiya".
Tunda nafaɗi Maganar Naga ya sauke kansa ƙasa gaba ɗaya jikinshi rawa yake haka nan naga jijiyar dake kanshi ta miƙe tai ruɗu ruɗu tana faman harbawa rintse idanunshi yayi yana taunar lips ɗin shi na ƙasa alamun ɓacin rai sun bayyana ƙarara a saman beautiful innocent face ɗinshi.
Ci-gaba nai da matse lemun amman jikina rawa yake saboda tsoron shi danaji kada, ya makeni ga gida babu kowa domin Maryama tasha gayamin irin horan dayake mata intai masa laifi.
Ina kammalawa nace mai.
"Yaya ga lemun".
Wata wawar damƙa yakai ma tsintsiyar hannuna dayasa nai wata irin ƙara! Mai fitar amo!
Rintse idanunshi yayi yana jin zuciyar shi Kamar gaushin wuta Yau inda shike da iko da zuciyarsa daya fatattaki soyayyar ta ya huta duk Irin yadda manyan 'Yammata 'ya'yan manyan mutane ke Mai tayin soyayyar su a school da wurin aiki baita ɓa kallonsu da zummar soba se Ita amman shine har zata dubi ƙwayar idanunshi take gaya mai wannan mummunar kalamin.
Gaba ɗaya ta rai rayoni yay zuwa jikinshi saman ƙirjinshi Mai cike da yalwar gargasa wadda bai saka mata mata komai domin rufe taba, Rungumeni yayi tsaf ina jin yadda zuciyarshi ke harbawa da sauri da sauri kafin naji shashsheƙar kukan shi cikin dodon kunnenah.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.