Complete Hausa Novels

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 6 of 33

*Littafin naira 300, Ne gamasu amfani da banki zasu tura ta nan 0078174806 starling bank sesu turo shaidar biyansu ta nan 08142105218, Marasa banki kuma zasu É—auki hoton katin waya na MTN na naira 400, su turomin ta nan 08142105218*

*Masu son AUREN BARE*
Book 1
Book 2
Complt document.
Naira 500.
Ta nan.0078174806 starling bank shaidar biya,08142105218,
Masu son littattafaina dana gama gaba É—aya na kuÉ—i har Auren bare sukuma naira 1000 ne.

*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }

NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*007*

Buɗe kyawawan idanun shi yake sannu a hankali waɗanda suka cika da wani irin ruwa wanda ya baiwa ƙwayar idanun tashi damar haɗewa da wani irin ja kamar gaushin wuta.
Jajayen laɓɓan shi yake motsawa a hankali a hankali wanda baka sanin abin da yake faɗi kafin ya sami damar mikewa a hankali yana rintse idanunshi ledar drip ɗin da aka maƙala mai yake bi da kallo atake anan tunanin abin da ya kawoshi asibiti ya soma zuwar mashi daki daki acikin ƙwaƙwalwar shi.
"Sannu yanzu maike maka ciwo?"
Tambayar da nurse É—in gabanshi tai mai kenan tana mai saka hannu tana cire mai ledar drip É—in.
Rintse idanunshi yayi tare da buÉ—esu akanta yana mai zuba mata manyan idanunshi.
Batare daya tanka taba ya komar da kansa saman pillow ya kwantar yana mai cije ƙasan laɓɓanshi na ƙasa.
Tattare kayan aikin ta tai kana tabar bakin gadon nashi bayan ta tabbatar da komi normal ba wata matsala.
Maganar su inna ce ta kuma dawo dashi daga duniyar tunanin daya faÉ—a na dangane da lamarin shi.
"Sannu yaro yanzu ina ke maka ciwo?"
Cewar inna tana mai dafa saman kanshi baki ɗaya hankalinta yana kanshi, kafin su anty suma suyi mashi sannun yana jinjina kai alamun da sauƙi.
Miƙawa baba hannu yay sukai musaba ba.
"Yanzu dai an mai allura tare da karin ruwa amman dai gaskiya in kuna son yaron ku ya rabu da wannan ciwon sekun mai aure".
Dr yafaÉ—a yana mai daukar biro da takarda ya soma rubutu ajikinta.
Kafin ya É—ago ya mikowa baba takardar.
Amsa baba yayi yana mai sakin murmushi.
"Babu komai likita indai dan wannan ne babu matsala akwai yarinyata da nai mai alkawari in yaso se a É—aura auren kawai".
Murmushi dr yayi.
"Amman kwa dattijo daka kyauta sabida yana cikin bad condition akan lamarin kuma har ga Allah, in bakuyi kokarin yi mai aure ba komai na iya faruwa sabida yadda halittar shi keda ƙarfi irin hakan ne kan saka mutum yay zina da dai sauran su".
Murmushi baba yay irin na manya.
"karka damu likita nafa gamsu sekai kamar baka gayamin ba".
Dariya baba ya baiwa dr dan haka seda yaÉ—an dara kana sukai sallama baba ya fita imran ya baiwa takardar maganin shikuma yaje phamarcy ya siyo sannan suka karasa cikin ward É—in.
Zaune yake yay matashi da pillow dagashi se, jallabiyar da inna ta zira mai lokacin da zasu tawo asibitin duk su inna sun zagaye shi suna masa sannu ganin baba yasa yaÉ—an muskuta kaÉ—an yana gaisar dashi.
Fuskar baba wasai babu alamun damuwa yake amsa mai gaisuwar tashi.
Domin yana tunanin inma wata matsala ce yanzu tazo karshe tunda yaji komi.
"Madallah Umari jikin da sauki kai imirana jeka samo mana shatar tasi mutafi gida yau dai ciwo ya ƙare".
Cewar baba.
Gaba É—aya su anty basu fahimci mai yake nufi ba, haka imran ya fita yaje ya samo tasi.
Da taimakon imran Umar ya sami damar fita har zuwa bakin gate inda motar take shida imran a gaba su anty da inna da umma a baya baba kuma yahau adai daita yace ze tadda su agida.
Har lokacin da suka koma gida akwai matasa a kofar gidan inna suna jiran isowar CIKA DAJI sabida shiÉ—in na mutane musamman matasan anguwar da suke yinshi.
Faka motar yay dai dai da sanda matasan kofar gidan suka saka ihu suna murnar dawowar shi.
Fitowa yay daga motar yana É—an yamutsa fuskar shi kasancewar shi bamai yawan magana ba amman akwai murmushi.
Se lokacin na sami damar karewa UMAR CIKA DAJI kallon tsaf.
Dogone mai jiki yana da suffar ƙarfafan maza farine mai sirki daja sumar kanshi irin ta fulanin usul ce haka nan yana da manyan lumsassun idanu masu kama dana maijin bacci.
Yana da doguwar fuska mai cike da tsantsar kyau wadda take zagaye da saje mai haɗe da gemu, fararen haƙoran shi masu kama da ƙanƙara yake buɗewa yana gaisawa da ƴan samarin anguwar da suka zo yimai ya jiki.
Har su anty suka isa gida yana faman gaishe gaishe da jama'a kafin ya samu ya zame da ƙyar gida ya shiga ya faɗa bayi yay wanka sannan ya fito yazo ɗakin inna ya zauna shayi ta haɗo mai mai lemun tsami.
Ta aje masa tana daÉ—a yi mai sannu da jikin?.
ÆŠaukar kofin yayi yana kaiwa cikin bakinshi zafin shayin na ratsa shi yana jin sauki acikin jikinshi.
Seda akai kiran sallar magariba sannan ya kammala ya tashi ya nufi masallaci.

Nikuwa fita mukai da sakina a wani layi muka tsaya nida ita da nazir, kana muka sami dan dakali muka zauna muka soma hira.
Nazir irin muta nan nan ne masu iyayin tsiya magana kaÉ—an seya sakomin turanci.
Sannan na fuskanci yana son ya taɓamin hannuna koya ɗan dukeni a cinyata amai makon naga sakina tai masa magana a,a sema kara gudun hirar mu naga tanayi.
Sosai nima na saki jiki muke hirar mu dashi.
Kafin naji yace.
"Ungo my bb"
Ya mikon kwalin waya daga hannun shi dayake Bb yake cemin ma'ana black beauty.
Jikina yana rawa nai kasa da hannuna naki amsa.
Amman seya kamo hannuna yana shafawa harya samu damar sakan wayan acikin shi.
Kafin ya kuma shafo gargasar hannuna cikin tafiyar tsutsa yana lashe baki.
"Ki amsa dan Allah sabida da ita xanna jin É—umin ki".
YafaÉ—a yana kokarin kamo hannuna ya É—ora a saman cinyar shi.
Lokacin idanuna yay tozali da yadda saman rigarshi ya tashi.
Da sauri na mike ganin sakina bata wurin tai gaba tana dariya tana cewa.
"Bara nabarku ku bawa shuka ruwa ina zuwa my yaya".
Cikin zafin nama shima ya mike tsayen yana kamoni.
Da sauri na fisge kamar zanyi kuka! nace mai.
"Yayan sakina maye haka wannan ba É—abi a mai kyau bace, sannan kuma gaskiya bazan amshi wayarka ba sabida gudun matsala a shekaruna ban can canci rike wayaba".
Amai makon naga ya amshi wayar senaga ya É—ora hannu a saman kirjin shi yana tari.
"Wayyo Bb in baki amsa ba zan mutu wayyo zuciyata".
Da sauri naga yana tarin kamar ze sumar min.
Cikin azama na matse wayar ajikina ina ƙifta idanuna.
"Zan amsa kai hakuri"
NafaÉ—a a sokon ce.
Amai makon naga ya ware senaga ya saki wata makirar dariya tare da manna min kiss a saman goshina.
"Wow thanks my bb ashe ana sona".
YafaÉ—a yana dariya.
Nima dariyar na saki kafin kuma nai gum da bakina ina saka hannuna ina toshe bakina.
Kamar kuma an ce na waiga aikuwa idanuna ne sukai tozali da Ya Umar da Ya imran suna tun karo layin wanda daga gani kamar daga masallaci suke.
Kirjina ne ya bada sautin Dum! dum!! da sauri na matse wayar a kirjina kafata na rawa na..................

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.