Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 18 of 33
*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹
*29 & 30*
Cikin tsananin ɗauki na ƙarasa gareta fuskata a sake naja na tsaya a gabanta.
"A,a sakina daman ana ganinku a duniya? se yanzu kika tuna dani wallahi nayi faman nemanki amman rashin sanin gidanku yasa kikajini É—iff gani ba waya akwai tarin damuwa a zuciyata".
Nafaɗa ina mai riƙo hannunta.
Zame hannunta tai daga cikin nawa tana mai jefamin ƙazamin kallo kafin ta kwashe da wata irin dariya.
"Hmm yaro!yarone yaro man kaza komi girman jikinka idan babba yafika tofa ya fika"
Ta numfasa tana mai cigaba dayin dariyarta.
"Humairah kenan ai bani da buƙatar ki bani wani labari akan mutuwar aurenki domin ina da labarin komi akanki ba kowa bace ba ke face bazzawara marar ƴanci mai baƙin jinin da tunda Umar ya rabu da ita batada mashin shini sabida tsabar baƙin halinki"
Jikina ne yahau tsananin rawa dajin kalamin da aminiyata take jefamin amman jin maganarta a karo na biyu ya kuma hargitsamin lissafina.
"A yanzu bani da buƙatar wata alaƙa dake humaira sabida daman buƙatar maje hajji sallah to alhamdulillahi ni naje hajji har umara ma naje ta dalilinki ƙawata"
Ta kwashe mini da wata shegiyar dariya.
"Da farko sunana sakina kuma ni haifaffiyar garin kano state ce mahaifina aiki ya kawosa garin kano, amman ɗan asalin garin nasarawa lafiya ne, har Allah yasa ya auri mahaifiyata umma, anan unguwar chiranchi suka zauna har Allah yasa umma ta haifi anty hadiza daga kan anty hadiza bata kuma samun haihuwa ba har seda ta shekara takwas sannan ta haifeni ni sakina, nayi primary da secondry a wata makaranta a gadon ƙaya daga nan babanmu ya rasu wannan tasa ban cigaba dayi ba bayan nai candy ita kuwa daman anty hadiza tuni tai auren ta anan kusa da gidanmu, babarmu mace ce mai hakuri hakama anty hadiza amman nikam inada zafi ina da kishi haka nan zuciyata mai riƙo ce da bin diddigin abinda take so shekaruna ashirin da huɗu da haihuwa amman bani da saurayi bare nai tunanin yin aure sabida akwai wanda na ƙwallafa raina akansa tun ina zuwa makaranta a gadon ƙaya nake haɗuwa dashi inze tafi BUK wannan tasa bana sauraran kowani ɗa namiji, sanin inada ƙaramin jiki yasa ummana bata damuwa da rashin aurena domin inna fita kamar yar shekaru sha bakwai zakaganni sedai ta idanu inada nuna shekaruna, Akwai watarana dana fito daga gidan anty hadixa kawai senaganshi hannunsa ɗauke da wata baƙar yarinya mai girman jiki tana ta mai sangarta ze tafi makaranta a ranar dana ganshi kasa bacci nai........
Washe gari nabi ta hanyar danaga yabi anan na sami makocin sa nake tambayarsa akan labarinsa atake anan ya gayan sunansa da kuma alaƙarsa da wannan yarinya wadda naji zata zaman Garkuwa a wajansa, Mataki na farko dana fara ɗauka shine na yaga takarduna gaba ɗaya na makarantar sakandire na sake neman sakandiren da wannan yarinyar take na koma daga farko ma'ana jss one.Cikin sa'a aka haɗamu aji guda da ita, da bin diddigi da shishshigi na samu na shiga jikinta ta zamen aminiya na fuskanci yarinyar batada wata magana seta masoyina wadda dukkan maganar da zatai akansa takan tafine da dukkan zuciyata.
NAZIR
Naje sabon gari nemo ankon bikin ƙawata xan gifa mukai clashing dashi adai dai wajan gidan gala, da sauri yazo gareni yana mai min magana akan yana sona sedai kallo guda nai masa na shaida cewar ƙwararran ɗan duniyane da wannan damar na amshi numbernsa wanda najewa wannan yarinyar dashi a matsayin yayana wanda na lasa mai wata ZUMA A BAKI wadda takaisa ga bani haɗin kai wajan cikar muradina, nayi amfani da ƙawancenmu ne na cika burina akan abinda nike so haka nan naje mata da wani irin salon yaudarar ƙawa wanda bata san dashiba......
Yaudarar kuwa itace.
Najenye jikina daga halaƙa da ƴan gidansu ma'ana koda wasa ban shiga jikinta a gida ba ta yadda har mahaifanta zasu lura dani su rabamu, nima kuma ban kaita gidanmu ba bare mahaifiyata da ƴar uwata su lura da shirina nabar ƙawance na da itane a iya school daga nan kuma se ranar dana taɓa satar jiki naje gidansu ranar da nazir yazo se kuma ranar daurin aure danabi zugar jama'ar biki na faɗa gidan nasu batare dana bar wani ya ankare ba, nayi amfani da tunanina sosai kafin wanzuwar hakan sannan koda wasa ban jata jikina ba amman ita ta jani ajikinta"
Seta juyo tana kallona.
"Tunda na sanki humaira sau biyu na taɓa xuwa gidanku abotarmu a iya makaranta ta tsaya wadda yawanci iyaye basa sanin dawa ƴaƴansu suke mu'amala a makarantunsu kinga kuwa hakan ke sawa yawanci burin ƙawa ke cika akan ƙawarta musamman mai wayo irin nawa, Tun bayan da kika auri Umar na shiga halin damuwa kullum bani da buri face ganin na rabaku"
Ta kuma kallona.
"MATAKI NA BIYU Nasha matukar wuya kafin na gano maye halin umar! na fara karantar cewar bayan ke baya da wata macen dayake so aduniya inka cire mahaifiyarsa daga ke kuwa se ƴaƴan da kika haifa wanda bayan na gama amfani da uwarsu a matakin farko na cikar burina senai amfani da su wajan ƙarasa ƙudirina, wanda bayan mun haɗa baki nida nazir mun fahimci lokacin dawowar umar gida nazo akan zan miki sallamar tafiya abuja har yazo ya rike hannunki se kuma nazo nabi naxir abuja akan an saceni wanda duk nazir ne ya bincikon inda umar ke aiki da hanyar sa ta komawa gida da ƴaƴan cikin ki nai amfani har umar ya auren wanda hakan bakaramin kunci kesa ruhina ba domin bana kaunar abinda ze raɓeki bare naci albarkacin ki a wajan Umar, humaira a yanzu burina ya cika shiyasa ma na ɓata lokaci wajan warware miki zare da a bawa domin bana shakkar kisan nice matar umar mariƙiyar ƴaƴanki aminiyar ki ta bogi domin nayi amfani da daƙiƙiyar ƙwaƙwalwarki nai miki muguwar illah kuma ina miki albishir da cewa umar nawa ne for now an always dan haka sekibi wani sarkin badai nawa ba".
TafaÉ—a tana mini dariya.
"Koda wasa umar bai san na sanki ba bare yay tunanin ni ƙawarki ce haka nan inna bata sanni ba haka zalika dattijawanki suma basu sanni ba bare ai tunanin naci amana sabida haka ina da fredom na shiga duk inda naso a dangin mijina batare da anyimin kallon mai cin amana ba bare naji kunya".
TafaÉ—a tana É—an rangwaÉ—a agabana kamar wata Æ´ar duniya.
Wani irin rawa jikina ya ɗauka kamar mazari kafin nai yunƙurin........................
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*
*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹
             *31 & 32*
Ɗora tafikan hannuna biyar a saman fuskarta bata gama dawowa a hayyacinta ba na kuma wanketa da wani bahagon marin, kafin ta sosa na ƙara mata uku a jere masu ɗan karen zafi.
Da azabar ƙunar zuci na dubeta.
"Wallahi sakina sekinyi mamakin yaudara ta da kikai zan nuna miki ni ƴar kano ce cikakka ba zuwau ba kuma sena nuna miki wacece ni! cikin ilimi da nutsuwa irinta ƴaƴa masu tarbiya daga ƙarshe kuma ina mai tabbatar miki da cewa GANGAR JIKIN UMAR KIKA AURA ba zuciyarsa ba domin zuciyar umar ta AISHA HUMAIRA ce da ƴaƴanta har abada sakina bazaki mallaki umar ba matukar ina raye nai gabanki nai miki gudun wuce sa'a a fagen soyayyar umar domin ni sona yake daga zuci har baki haka zalika sone daga Allah ba boka ba malam ba kirsa bare bariki soyayyace ta asali ƴar gaske wadda turawa kewa laƙani da Pure love wadda ba algus cikinta kuma ko yanzu na mutu nagodewa Allah dayasa kika ci arzikin ƴaƴana har kika sami soyayyarsa koda haka seki bawa jakar ƙwaƙwalwarki amsar wacece aisha a zuciyar umar? bazan ji komi dan kinmin haka ba,domin sau tari daman makashinka yana tare dakai sedai kuma ta yaro kyau take bata ƙarko mu zuba"
NafaÉ—a a dake.
Tare da saurin barin wajan zuciyata na suya na nufi gidanmu.
*SAKINA*
Azabure ta dafe fuskarta da dukkan tafukan hannayenta tsananin mamakin humaira ya hanata tafiya bare ta ɗago daga dogon suman wucin gadin azabar zafin marin data afka sosai humaira ta bata mamaki yaushe humaira ta zama jan wuya haka? yaushe humaira ta zama mai dakakkiyar zuciya haka wadda harta ɗaga hannu ta zuba mata maruka biyar lallai ɗan hakin daka raina shike tsone maka idanu, jikinta sanyi ƙalau ta nufi gidansu kai tsaye kicin ta nufa batare data amsa maganar da ummanta ke mata ba, harseda ta sami ruwan ɗumi ta wanke fuskarta dashi abinka da farar fata tuni fuskar ta haye tai suntum dole seda ta haɗiyi maganin zazzaɓi sannan ta wuce ɗaki ta kwanta da shirin tafiya gidan mijinta gobe dakuma tsananin tsanar humaihar mai zafi a zuciyarta.
*Humairah*
Kamar ƴar maye haka nake tangaɗi a hanya harna isa gida kai tsaye ɗakin anty na nufa ina zunduma ihu kamar ƙaramar yarinya, da sassarfa anty da baba wanda ya dawo daga wajan sana'arsa kenan suka fito rumfar suna tambayata a ruɗe.
Ajikin anty na zube ina cigaba da kukana wanda fitarsa ce kaÉ—ai zata sakani jin sanyi acikin zuciyata.
"Ke humairah bani son sakarci, mi aka maki zakizo kina mana kuka kamar wata ƙaramar yarinya bana tunanin ko anisa zatayi wannan shirmen naki".
Naji muryar baba akaina yana faman faÉ—a.
Cikin hakan su umma da baffa suka shigo É—akin a kiÉ—ime sabida suma sunji kukan danike yi ashe.
Itako anti janyoni tai jikinta muka zauna a tsakar É—akin hakan yasa suma su baba suka zauna suna sauraran kukana.
"Anty na shiga ukuna wayyo yaya zanyi?"
NafaÉ—a cikin kuka, kusan a tare baba da baffa sukace.
"Wani abunne ya sami umar da Æ´aÆ´an a hanya?"
Girgiza kaina nai tare da share hawayena kana na dubi anty na soma bata labarin abinda ke faruwa tundaga haÉ—uwa da sakina har kawo yau hatta abubuwan danikewa ya umar seda na faÉ—a ina kuka!
Daga ƙarshe na ɗora da cewa.
"Baba ku yafeni nasan ban kyauta muku ba domin ba irin tarbiyar da kuka bani kenan ba amman sakina tayi amfani da ƙaramin tunanina ta yaudaran harta auren mijina"
NafaÉ—a ina kuka.
Gaba É—aya tausayin tane ya kamasu tabbas wannan wata jarrabata ce tare kuma da ishara Allah ya nuna musu, gaba É—ayansu domin abin da ya sami É—anka ai ya sameka.
"Karki damu humairah kanta taiwa amman kema kinyi sakaci waya gaya miki ana yarda da mutum yanzu ai mutum se Allah".
Cewar ummah wadda take share hawayenta.
Shikuwa baffa tsabar kiÉ—ima ma kasa cewa komi yayi se uban share zufar dayake famanyi.
"Kinga wannan ma ya zama izina gareko? gaba in akace ki sake yin abu babu shawarar mahaifanki kya kumayi sakarar banza uban wama ya haɗaki da ita? wato ni ina nan ina miki tarbiya wata nacan tana rushemin, amman Allah ya sakawa da umar da alkairi yanzu a wannan zamanin wani namijine zeyi abinda umar yayi wani namijin zaki dinga sheƙawa wannan iskancin ya zauna dake? to wannan matsalar da kika shiga haƙƙi biyune ya jefaki cikinta domin kinsan yanzu tun a duniya ake nuna ishara, abu na farko hakkin mijinki da kuma hakkina ni mahaifiyarki danafi kowa kusanci dake amman kika je kika haɗa kai da wata take miki zagon ƙasa, to mu bazama mu nuna wannan maganar ta faruba ki zuba musu idanu Allah ze nuna ikonsa".
Anty ta faɗa tana zubar ƙwallah domin tsananin jin tausayin ɗiyar tata.
Shikuwa babanmu tunda ya sada kansa a ƙasa bai kuma ɗagowa ba har seda su baffa sukai sallama suka wuce nasu ɓarin sannan yaja hucin takaici.
"Yanzu Aisha wannan sakarcin kikai taiwa Umari ashe? ah dole yaron nan ya dauke mana ƙafa, ashe da walakin goro a miya! ikon Allah inda ranka zaka sha kallo wato ita wannan yarinyar ku rabu da ita kanta taima amman kuma wannan ma babban darasi ne wato inzaka shekara kana bawa ɗanka tarbiya daga can zaka sami wanda yake rusa masa, to dama munata shawarar zaki koma karatu nida imirana to matsalar nifa naji tsoro kada ki kuma haɗuwa da wata ƙawar ta kuma jefaki a illah amman da naso ki fara koda fce ce kafin Allah ya kawo miki wani mijin, Allah yay miki albarka aike ba abar jin haushi bace yanzu abar tausayice tabbas alokacin akwai kuruciya da kuma wauta Allah ya saka miki Aisha shikuma umari Allah ya fitar dashi daga sarƙar wannan hatsabiya amin".
Baba ya faÉ—a yana mai kokarin fita daga cikin É—akin.
"Baba".
Nakira sunanshi.
Ya dakata yana kallona da tausaya wa.
BuÉ—e bakina nai kana nace mai........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.