Complete Hausa Novels

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 8 of 33

*NAN NA KAWO ƘARSHEN FREE PAGE*
MAI SON CIGABAN LABARIN *ZUMA A BAKI*
Ze biya naira 300 ta wannan acctn numbern. 0078174806 starling bank, shedar biya ta nan 08142105218 marasa amfani da banki kuma zasu É—auki hoton katin MTN na naira 400 su turomin ta lambar dake sama.

*YAYA ZATA KAYA A TSAKANIN ZAMAN TAKEWAR AUREN UMAR DA HUMAIRA* ?
WANDA BAN RIGA DANA BAYYANA SHIBA DOMIN SEMUN SHIGA DAGA PAID SABIDA ABIN MUHIMMI NE.
*SHIN TAYAYA HUMAIRA TAKE RABUWA DA UMAR*?
*DA ALAMU YANZU UMAR YA ZAMA MAI KUÆŠI HUMAIRA KUMA TA KAMU DA MUGUN SON SHI BAYAN SHI TUNI YAYI AUREN SHI*
*SHIN ZE MAYAR DA ITA ÆŠAKINTA? SHIN WA UMAR YA AURA? SHIN TSAKANIN HUMAIRAH UMAR NAZIR WAYA LASAWA WANI ZUMA A BAKI*?
*TAYAYA UMAR YAKE SAMUN KAN HUMAIRA HAR RABO YA SHIGA TSAKANIN SU*?
*TABBAS DAGA PAGE 1 to 8 LASA MUKU ZUMAR LABARIN NAI AMMAN RAGOWAR SEMUN SHIGA DAGA PAID GROUP DOMIN AKWAI TARIN ABUBUWAN DABAN RIGA NA BAYYANA SUBA WANNAN SALON NA DABANNE HAKA NAN TAFIYAR TA MUSAMMAN CE* 💃💃
*KUNSAN SALON LABARINA WANDA YA KARANTA LITTAFINA NA AUREN BARE! YA SANI WANDA BAI KARAN TABA KUMA YA DAURE YABI WANNAN SABON DOMIN KA TSUNDUMA CIKIN TAFKIN KOGIN DAƊIN LABARIN HUMAIRAN UMAR* 💃💃💃
MUJE ZUWA PAID GRP READERS DOMIN ABIN SEDA SHIGA LABULE💃💃💃💃💃

*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

*9&10*

Zuwa asubahi jikina ya gama tsanan ta da mugun zazzaɓin daya rufeni a daran jiya sannan kuma ga wani azababban ciwon kai daya kawon cafka wanda yasa ko gani banyi se dishi-dishi da ƙyar na rarrafa tsakar gida nayo alwala na dawo na tayar da sallah.
Abin da ya bani mamaki yadda ko kaɗan anty bata tasheni akan nai shirin makaranta ba, wanda sanin kaina ne da munyi sallar asubahi anty ke sakamu mu shirya kana muyi break fast wajan 7:00am mutafi school, zuciyata ce tabani cewar ko ɓacin ran jiyane ya hanata tashin nawa.
Mayar da kaina nai saman pillow ɗina tare da saka hannu na share hawayena baccin ne ya kuma kamani ban farka ba se wajan taran safiya jin hayaniyar jama'a a cikin gidanmu yasa na mike duk jikina babu laka sabida zazzaɓin dake jikin nawa.
Fita nai tsakar gida ina mitstsike idanuna.
Katari nayi da anty zulfa'u kanwar anty da su anty uwani suna haɗa wuta a tsakar gida gawata ƙatuwar tukunya nan gabansu cike da sanwar shinkafa da faduka.
Haka na wuce É—akin anty wanda anan ma seda mamaki ya cikani ganin yadda dangi suka cika É—akin dam ga ayiya kakata xaune taci kwalliyar su ta tsofi.
Shigowata yasa É—akin ya kacame da buÉ—a kafin naga wata kanwar baban su baba ta kamoni tai cikin uwar É—aka dani abakin gado ta zaunar dani kana ta fita waje mintuna biyu tazo ta fita dani tsakar gida banÉ—aki takaini inda naga wani bawo ancikashi da ruwan É—umi cemin tai nai wanka tana jirana a waje.
Wankan nai ba musu.
Sannan na fito waje takuma kama hannuna muka wuce É—akin anty, Anty zulfa ce ta shigo hannunta É—auke da leda baka wadda ta zazzage farar shadda mai golden É—in stone ajikinta atakaice dai seda suka taimakamin na shirya cikin wannan doguwar rigar shaddar kana anty uwani taimin É—aurin kallabi domin su duk anan cikin garin tofa suke aure ba a kauyen ba shiyasa suke da wayewar kai.
Mayafi suka bani golden da takalmi sannan na saka sarka da Æ´an kunne duk da babu madubi wajan amman nasan nai kyau ba É—an kaÉ—an ba.
Zaunar dani anty uwani tai a bakin gadon antynmu sannan ta fita mintuna goma tazo hannunta É—auke da kwano da wata jarka.
Mikomin tai ta tsaya agabana tana bani umarni akan na bude naci abin cikin kwanon.
Hannuna na sanya na bude inda nai katari da, dafaffiyar kaza wadda ba,a cire komi na jikinta ba andafata da kayan miya.
Saka hannu nai na soma ci bakina É—auke da bisimillah.
Ko kaÉ—an babu daÉ—i sema bauri amman yadda nikejin tsoron anty uwani wadda ta kasance kamar yayar anty ce domin da babanta da baban su babanmu da babansu anty uwa É—aya uba É—aya suke, itama tana nan cikin garin tofa tana aure da Æ´aÆ´anta duka acan waÉ—anda taima aure.
Yasani cin kazar ina korawa da tsumin kwakwa da dabinon data mikon na wannan jarkar.
Seda na kammala sannan na mika mata kwanon ina yamutsa bakina sabida baurin daya gamen bakin nawa.
Anty uwani ta fita haka nan su anty zulfa sun fita sun barni a É—akin ina faman tunanin abinda ke faruwa babu mai bani amsa a wannan lokacin hakan yasa na koma saman gado nai lamo ina tunanin rayuwa.
Ƙarfe goma da rabin safiya dubban mutane suka shaida ɗaurin auren UMAR MUHAMMAD SARKIN GIDA da amaryar shi AISHA YUSUF NUHU, akan kimin sadaki naira dubu hamsin wanda abokin ango yayan amarya imran shiya bada wannan kuɗi.
Bayan an kammala ɗaurin aure can na hango ango cika daji sanye cikin rigar shadda fara ƙall mai golden ɗin aiki wadda imran yay shige da ficen ganin ya ɗinko musu a safiyar yau shida humaira da kuma imran ɗin.
Bakaramin kyau umar yay ba haka ya dinga mikawa mutane hannu suna gaisawa bakin shi É—auke da matsanan cin murmushi.
Daga wajan É—aurin aure gidan su suka wuce inda zuwa wannan lokacin dangin shi na can katstsina sun zo tare da Æ´an uwan innah.
Sosai suma suke gudanar da aikace aikacen girkin Æ´an bikin.
Ɗakin inna ya wuce ya sami kakarshi iyatu zaune aifa tana ganinshi ta fashe da kuka ta rungume shi sabida ta tuna marigayi mahaifin shi seda ƙyar ya bata baki duk da shima ɗin yana cikin kewar mahaifin nashi domun wannan karamci na iyayen humairah kaɗai ya nuna masa yadda mahaifin nashi ya kasance mutum nagari domin ya shuka kairan ne shiyasa yanxu shi yake girba.
Sosai suka gaisa da Æ´an uwanshi yana kokarin fita yaji muryarta a bayan shi.
"Hammah umar ina tayaka murna".
Kozasuyi shekaru dubu basu haÉ—u ba baze manta da itaba nuratu ce É—iyar kwanwar mahaifin shi wadda ta rasu.
Da murmushi ya juyo ya dubeta nuratun daya sani ada a yanzu ta sauya wannan Æ´ar gayuce Æ´ar boko wayayya.
Sosai yay mamakin yadda ta goge.
Muryarta tace ta katse mai tunani.
"Hammah baka da zumunci tunda ka dawo kano nima na É—aga hankalina hakan yasa babana ya daukeni daga gabansu tsoho ya kaini wajan matarsa inda anan nai karatu har nai candy yanzu ina jiran result ne na faÉ—a jami'a kasan yanzu Dady ne É—an majalissarmu fa".
Zaro idanu yay tabbas baban nuratu ada daya sanshi kansila ne amman yanzu harya kai wannan mataki lallai Alhaji uba bakori yanzu ya taka ƙasa dole nuratu ta goge.
"Masha Allah sekuma a fitar da miji ba".
YafaÉ—a yana kokarin fita.
Saka hannu tai ta kunshe fuskarta.
"Hammah ka bani phone no: ɗinka zanna kira muna gaisawa Dady ma yace na karɓa masa".
TafaÉ—a tana miko mai wayarta wadda ta kasance iphone 11pro zaro idanun shi yay yana bin wayar da kallo kafin ya amsa ya saka mata numbern kana ya fita.
Da gudu ta biyoshi tsakar gidan kuma tana mai cewa.
"Hammah ga Dady ya É—aga wayar"
Ta miko mai amsa yay yana karawa a kunnen shi.
Cikin kulawa Alhaji uba ke taya umar murnar auren shi sabida yadda yasan umar sosai domin indai zezo ganin nuratu ada tofa tare da umar ze ganta haka nan kominsu tare suke shiyasa ko siyayya zema Æ´ar tashi baya ware umar domin batada magana seta hammah umar ada É—in haka ma ayanzu kusan kullum setace mai hammah umar kaza da kaza, tsananin son nuratu da dadyn keyi yasa yake son umar domin nuratu ita É—aya ce mace da Allah ya basa ragowar Æ´aÆ´an matarsa mazane su biyu kuma yarane.
Seda suka kammala wayar sannan umar ya amshi numbern dadyn kamar yadda dadyn ya umarta numbern accnt É—insa ya tura mai wanda atake anan yay mai transper dubu É—ari biyar yace yay hakuri lokaci ya kure ga tasa gudun mawar a sai kayan tea ba yawa.
Komawa cikin É—aki tayi shiko wayarsa ya saka ya kira dady yaymai godiya sannan ya fita wajan abokanshi kiran imran yay gefe tare da amsar accnt number shi yay masa transper na kudin fantin É—akin shi wanda anan humaira xata soma zama kafin aga abinda Allah zeyi.
Sannan ya wuce pos ya ciro dubu É—ari biyu.
Kai tsaye gida ya kuma dawowa kiran maryam kanwar shi yay wadda take kokarin shiryawa sannan yace ta kira mai anty maimuna kanwar inna wadda suka xo a É—azun daga katstsina, Bayan tazo ne ya damka mata kudin yace mata suje kasuwa tare da maryam su É—an haÉ—o kayan lefe koya dai suke.
Hakan ce ta kasance suka amsa maryma ta shirya suka wuce kasuwa wanda suka haÉ—o kayan lefen masu É—an dama tare da akwati guda biyu karami da babba sukayo gida.
Shiko fita ya kumayi ya damkawa wani abokinshi mai suna salim kuÉ—in kayan abinci, sannan ya koma wajan tarin abokanshi sukai sallar azahar kana sukaci abinci daga nan suka wuce gidansu amarya.
Amman shi imran bai bisu ba ya wuce ne wajan masu faitin É—aki domin a gyara muhallin amarya.
Lokacin da suka karasa gidan su humaira motar kayan gadon da baba yay rawar ganin saimata ta karaso seda suka tsagaita aka gama fitar da kayan sannan suka shiga cikin gidan gaishe gaishe sukai da dangin kafin abokanshi su bukaci ganin amarya.
Ina can ina bacci anty uwani tazo ta tashan kamar daga sama naji maganarta akaina domin ko kaÉ—an ban san budirin da ake ba.
"Humaira tashi ga angonki yazo ku gaisa da abokanshi"
Bata bani damar magana ba ta gyaran fuskata muka fita waje gaba É—aya jikina rawa yake zuciyata rawa take dajin furuncin ta ni akaima aure!!!

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.