Complete Hausa Novels

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 19 of 33

#AUTAR MANYA

*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *33 & 34*

"Baba inada buƙatar makaranta nima dan Allah baba ka tausayamin ka mayar dani makaranta wannan kaɗai ze saka naji sassaucin zafin dake zuciyata".
Nakai maganar ina mai fashe mai da kuka!
Dakatawa baba yayi da fitar nashi kana ya dawo gabana ya gurfana hannuna ya kamo yana mai lallashina.
"Haba Aishatu na! maye na kukan aini yanzu na zubda makaman yaƙina akanki,Bara ɗan uwanki yazo inaganin zan sama miki gurbin karatu kima daina zubda hawayenki akan wannan".
Babana ya faÉ—a min hakan cikin tattausan lafazi.
Anty ce ta, tari numfashin, baba tana mai cewa.
"Amman babansu da kawai ta fitar da mijinta tayi aure inaganin hakan zefi mata ƙima, domin yanzu haka daga gidan Haladu ƙanin umma take kuma naji umma na maganar bazzawari hajiya zata haɗata dashi ai sekaji ta bakinta kafin maganar karatun ta miƙe ko?".
Anty takai maganar tana mai kallon babammu wanda yay tsam da ransa alamun ya É—an shiga tunani ne na daban.
"To'to babu damuwa amman dai duk da haka ina son tacigaba da karatun nata yanzu ke Aisha yaya kukayi da hajiya hadizan?".
Baba ya jefamin tambayar yana kallona.
Hawayena na share domin ni tuni nama manta danaje gidan mai makarantarmu.
"Baba wai ɗan uwanta ne keson ƙarin aure matarsa ɗaya da yara takwas, amman ba gida guda ze haɗamu ba kowa da gidanshi, nan da sati ɗayama zezo mu gaisa".
Nakai maganar kaina a ƙasa.
Dafe haɓa anty tai tana mai sauraron abinda baba ze faɗi aikuwa baba se cewa yayi.
"To madallah Allah ya zartar da abinda yafi zame miki alkairi a wannan karon dama zamu baki domin ki fitar da mijin da kike so sabida haka duk wanda kika ɗauka kika kawo mana matukar muka bincika mukaga halinsa na garine zamu bakishi sabida nina fahimci a karon farko ma, Umar ba ƙinshi kikai ba tsabar zugace da hassadar waccan shaiɗaniyar ƙawar taki ya saka kikaita ƙulla masa tsiya salo-salo to yaya zamuyi da hukuncin Allah fatanmu Allah yay miki zaɓin alkairi amin".
Baba yafaÉ—a yana mai tashi tsaye ya kama hanyar fita anty tana mai masa adawo lafiya tare da amsa masa da amin.
Sosai anty ta zaunar dani tana min nasiha tare da bani manyan misalai akan yanayin rayuwa wanda nai matuƙar tsorata dasu tabbas nina shaida yarinya ce ni amman ƙaddarar auren wuri da haihuwa yasa na sami ƙarin girma ajikina da hankalina wanda ya zarta na shekaruna.
Bamu muka tashi daga rumfar anty ba seda akai kiran sallar magariba bakin rariya naje nayo alwala na shige É—akinmu na shinfiÉ—a abun sallah na som gabatar da sallar magariba ina idarwa nai bangaren umma kallo.
Anan muka shantake har Anty tagama tuwon dare ta zubo mana namu mukaci daga nan mukai sallar isha'i kowa ya kama gabansa domin ya kwanta ya hutawa ransa.
Dare mahutar bawa amman a gareni hakan ya gagara domin gaba ɗaya nakasa rintsawa idanuna ya fushe sam nakasa yin bacci se faman nanata maganganun sakina nake acikin ƙwaƙwalwata.
Wannan rayuwa wato gaba É—ayanta abar darasice ga bawa yakamata tun da sauran damarmu mu dinga gyara halai yarmu kafin mutuwa tazo ta riskemu wannan itace ranar nadama ga bawa.
Wai yanzu ace zalinci cin amana zamba cikin aminci handama da baba kere sune suka yawaita ga al'umarmu? makashin ka yana tare dakai kana tare da mutum amman shi zagon ƙasa yake maka shin mai Umar yake dashine da har sakina zataimin wannan ƙullalliyar akanshi?
Lumshe ƙananun idanuna nayi ina hasko yadda umar yake a zahiri.
Umar dogon namijine mai suffar ƙarfafan maza farine tas mai dogon hanci da manyan idanu yana da mugun haƙuri tare da kawaici da rashin magana,Amma akwai zuciya idan ranshi ya ɓaci, Lumshe idanuna na kumayi ina Mai juyawa na rungume filon dake gabana tuno tsadaddiyar soyayyarshi wadda kansa naji kamar mu kaɗaine ke rayuwa a duniyar in yana gwadamin ita, yasan salon narkar da zuciyar mace haka nan yasan laƙanin mantar dake a duniyar da kike koke wacece wajan taurin kai matukar umar ya soma rikitaki da salonsa tofa bazaki kaucewa biye masa ba.
Wani azababban fitsarine ya kamani acikin wannan dare gani Mai mugun tsoro tashin anisa na soma amman taimin shuru,ganin ya soma zubomin a pant É—ina yasa na mike da sauri tare da fita ina tsaki.
Duk tunaninshi dana yaranshi dana matarshi ya hanani sukuni har yasa na raba dare idanuna bude.
Addu'a nai kana na shiga bayi na kama ruwan na fito nai alwala na nufi hanyar ɗaki adai dai dokin kofar ɗakinmu naɗan doki bakin kofar da ƙafata wadda naɗanji zafi kaɗan amman sena maze na shige ɗaki bayan na kaɗe shinfiɗata na kwanta abina.
Yatsana ne babba na ƙafa ya cigaba da zafi kamar an watsa barkono addu'a nai a wajan na shafa a wannan karon naji dama sannan bacci ya kwasheni wanda ban farkaba seda akai asubahi koda na tashi still yatsan nawa ya ɗan kumfura haka nayo alwala nazo nai sallah bayan nai azkar na koma bacci wanda rabi azabar yatsan ce fall a jikina wadda harta zuban zazzaɓi mai zafi.
***********
Da wajan karfe bakwai ta isa tasha wanda kusan bakwai da rabi motarsu ta tashi zuwa garin na abuja,Tunda tahau motar ta kifa kanta a saman jakarta tana tunanin matakin dazata dauka akan humaira haka har suka isa garin abuja bata wani yanke tartibin abinda zata mata É—in ba.
Taxi ta tara ta shigar da kayanta sannan ta masa kwatancen inda zataje tafiyar mintuna kaɗan ta kaita unguwar tasu kuɗinshi ta bashi sannan ta saukar da kayanta tare da nufar cikin gidan ta kama kofar gate ta bude da ƙyar ta shigar da jakarta cikin falon tana uban nishin azabar gajiya data zafin ciwon kan marin jiya dayaki sakinta har yau.
Gumi ta yarfe na wahala tana mai kallonshi a fakaice kafin ta karasa saman kujerar dayake zaune da sassarfa ta isa gareshi..........

#AUTAR MANYA
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *35 & 36*

Zaune yake dagashi se dogon farin wandon yadin kufta system ce a saman cinyarshi yana dannawa sabida wani aiki dayake gudanarwa acikinta.
Idanunshi manne da farin gilashi wanda ya zauna das a fuskar tashi abin sha'awa.
Cikin wani irin yauƙi da gwalli sakina ta ƙarasa gabanshi tare da saka hannu ta janye system ɗin dayake aiki da ita ta, kana ta mayar da jikinta ta zauna a saman cinyarshi hannunta ta ɗora a saman sajenshi taɗanja kaɗan tana wani irin ƙifta idanunta.
"Beby nai missing naka amman shine ka tawomin da yarana babu ko sallamar kirki ko?"
TafaÉ—i maganar cike da salon jan hankali.
Murmushi ya sauke kaɗan domin a iya wannan lokacin yagama karantar cutar mai da yara da takeyi a bayan idanunshi, amman danya ɓatar mata da tunaninta yasa yace mata.
"Dafatan kin dawo lafiya?"
Ya kauda wannan maganar datake soko masa.
"Lafiya kalau na dawo se É—unbin kewar Æ´aÆ´ana"
TafaÉ—a da wata irin siga.
Shikam dariyama ta basa a wannan karon.
"Ƴaƴanki ko? kima daina damuwa dasu fa kin manta uwar data haifesu ma tana can tana rayuwarta babu su bare ke?"
YafaÉ—i maganar da siga biyu.
Jikinta ne yay sanyi a wannan karon tai danasanin jefa mai tambayar ma gaba É—aya.
"Nida ita akwai bam-banci domin ni ina sonka".
TafaÉ—a a zuciye.
"Ita kuma ƙina take? look sakina idan kinsan cin zarafina zakiyi daga zuwanki zaki koma inda kika fito yanzu".
Yafaɗa cikin ɓacin rai matuƙa.
Wanda yasa hatta idanunshi seda ya soma fitar da jar kala.
Numfashi taja a galabaice dajin wannan baƙin furucin nashi.
"Umar mai kake nufi akan waccan marar mutunci kake gayamin waɗan nan maganganun? kalla fuskana akan naje gidansu gaisar da mahaifanta dan kawai mamanta tace ni matarka ce jiba yadda ta miƙe ta zubamin maruka har biyar jere"
TafaÉ—a tana mai nuna mai fuskarta data kuma yin ja abinka da farar fata.
Zaro idanunshi yay waje cike da mamaki.
"Toke waya baki ikon zuwar musu gida da izinin waye?"
Rau rau tai da idanunta.
"Tsautsayine ya kaini ba wani abun ba".
"Yayi miki kyau amman bana tunanin Aisha zata mareki akan kawai dan kince ke matata ce gaskiya domin wannan kalmar bazata saka ta mareki ba? sakina sau tari kina yin abun da nake kallonki dasu kada fa ki manta ina aikine da shashin bincike ne na masu manyan laifuka wallahi! wanda ya fiki rashin gaskiya ma tashi É—aya nake ganoshi bare ke! ke kina cin alfarmar aurena ne amman bada ban haka ba da tuni na watsaki waje, Sabida haka ki taka a hankali kisan da wa kike zaune ba sakarai bane sedai kawaici irin na fulanin usul".
Yakai maganar yana mai tashi yabar mata wajan ya nufi bedroom É—insa zama yayi a gefen gado gaba É—aya abin duniya yay masa zafi.
Ya soma gajiya da halin sakina wanda kawai kallonta yake dasu bawai baya sane bane musamman akan yaransa wallahi kawai yana mata kawaici ne akansu.
Wayarsa dake yashe a bakin gadon ya É—auka ya shiga contact É—insa lambar ogansa ya shiga kira bugu É—aya ya É—auka gaisawa suka shigayi, sannan suka É—ora akan bayanin binciken da aka sakashi ya gudanar akan wani mutum wanda ake zargi daya saci yara guda biyu yayi garkuwa dasu, sosai suka zanta akan maganar yanzu haka an samu nasarar gano inda mutumin yake zaune sabida haka dole ogan nasa yace mai zasu turashi kano sabida akwai waÉ—anda aka gano suna tare da mutumin sedai su suna zaune ne anan kano bayan sun gama maganar sallama sukai sannan ya kashe wayar yana mai dafe kansa dake barazanar tarwatse masa.
Sam bai shirya tunkarar kano a wannan lokacinba, sabida yaransa suna tsaka da karatune shikuma baya son abinda ze nesanta shi da yaranshi musamman a wannan lokacin da sakina take gallaza musu duk da bai nuna mata yasan komi ba, amman abin yana mugun taɓa masa ransa amman ta kusan tuƙeshi takaishi bango domin shi ɗabi'arshi ce kawaici zai taraka in kana masa abu amman da zarar ka kaishi bango tofa komi ma ze iya faruwa.
Tsaki yaja mai ƙarfi sannan ya miƙe tawul ya dauro a west ɗinshi kana ya faɗa toilet ya sakarma kanshi ruwa,ya jima yana cuɗe jikinshi da lallausan soson dake hannunshi,sannan ya kammala wankan nashi ya fito a centern ɗakin ya tsaya ya goge ruwan jikinshi gaban jerin kayansa ya tsaya ya ɗauki yadin kufta ruwan madara mai ɗinkin riga har ƙasa se wando sakawa yay kana ya feshe kansa da turare mai ƙamshi gyara sajen fuskarshi yayi sosai sannan ya ɗauki makullin motarshi ya fita makarantar su islam.
A hanya nuratu ta kirashi tsiya take mai akan rashin zumuncin sa wai ya manta da ita kwana biyu baya nimanta murmushi yayi yana mai bata hakuri akan yanayin aikinsa ne ya kawo hakan.
Koda ya ƙarasa makarantar seda ya jira su aka tashi sannan ya kamo hanya suka yo gida tun a mota daya ce musu mommy ta dawo yaga islam ta haɗe ranta saɓanin ada daya daukosu sunata murnar ganinshi, Amman tunda yace musu mommy ta dawo sukaja bakinsu suka tsuke harya ƙarasa gida basu tanka masa ba, abakin gate ɗinsa ya tsayar da motar tare da bude musu kofar kallon islam yayi gaba ɗaya yarinyar ta kom kamannin mahaifiyarta sak,inka cire farar fatarshi data ɗauko shiyasa tafi aslam kyau nesa ba kusaba sabida ita ta haɗe da kamannin humaira da kuma manyan idanun mahaifinta ne,
"My happiness zanje nai mana take away na dinner kuje gida maza ki kula da ƙaninki kafin na dawo".
Tura baki tai gaba tamkar yadda humaira ke masa inzatai rigima sannan tace mai.
"Mudai daddy kaje damu zamu bika can É—in"
TafaÉ—a tana mai kafesa da manyan idanunta.
murmushi ya sauke mata yana mai lakato kumatunta yana maijin soyayyar ta acikin ransa fiye da komi na rayuwarsa.
"Sorry my love jeki cire uniform ɗinki kicirewa ƙaninki ku zauna a ɗakinku kujirani ina zuwa"
YafaÉ—i maganar cikin tausayin kansa dana yaran nasa.
Babu damar musu haka taja aslam tana ƙunci kamar zata kurma ihu! suka nufi gidan.
Ya jima yana kallonsu don seda suka ƙulewa ganinshi sannan yaja motar ya nufi inda ze amso musu abincin dare.
Yana tafe yana tunanin su aransa tare da fargabar abinda zeje ya dawo akan su.
Cikin sanÉ—a kamar munafukai sukai sallama a falon hannun islam rike dana aslam.
Tana zaune ta haÉ—e kai da gwiwa tana nanata cin zarafin da umar yay mata a É—azun wanda shiya hanata tashi daga wajan bare ma ta kintsa kayan ta datazo dasu.
Cikin rawar jiki suka zube a gabanta.
"Mommy barka da yamma"
Islam ta faÉ—a sabida itace mai baki aslam kam bayada wani wayon kirki bare bakin magana sosai.
Wata uwar harara ta maka musu cike da tsanarsu.
"Dan ubanki inda banyi yammar ba zaki ganni anan wato baku so na dawo gidan ubanku bako? shegiya mai fuska kamar anyi ɓarin kayan miya a injin markaɗe kutashi kubani waje ƴaƴan jaraba" ta saka ƙafa ta haure islam tai baya amman tsabar tsoronta bai bar islam tai kuka ba da sauri taja ƙaninta suka bar falon ɗakinsu suka nufa kuka! yarinyar ta saka a ƙasan tiles tana mai sosa wajan data duketan.
Cikin kuka aslam ya matso gabanta ya saka hannu ya share mata hawayen.
"Yaya ki bar kuka! dan gayawa daddy"
YafaÉ—a da gwaranci sabida baya iya magana sosai.
Cikin son kanin nata ta janyoshi jikinta tana share mai hawayen dayake.
"Aslam É—ina kada ka gayawa dady kaga mommy tace in muka gaya masa zata yanka mu mudaina ganin daddy da inno da maman kano wadda na kwana a wajanta".
TafaÉ—a tana mai tashi tsaye ta wanko fuskarta suka cire kayansu tsuru sukai a É—akin suna jiran ubansu ya dawo domin tsoron fita suke waje.
*********
"Yaya humaira ki tashi ga abin karyawarki inji anty"
Naji muryar anisa kanwata akaina tana min magana.
ÆŠago da jajayen idanuna nai na sauke akanta.
"Anisa kiramin anty ƙafata kamar zata cire wayyo yatsana...........

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.