Complete Hausa Novels

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 20 of 33

TOFA!
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *37 & 38*

NafaÉ—a ina mai sakin kuka tamkar raina ze fita sabida wani irin azabar ciwo da yatsan nawa yakemin da sauri anisa ta fita tsakar gida mintuna kaÉ—an se gasu sun shigo tare da anty cikin É—imuwa anty ta dubeni.
"Tashi humairah muga yatsan naki meke damunki?".
Da ƙyar na sami damar yunƙurawa na tashi daga kwanciyar danake ɗin, na saka matashi na gyara zamana, hannu ta saka ta ɗago yatsan nawa dayay jajir kamar ze fice sabida azaba
"Subuhanallahi yaya akai kikai wannan rauni haka kamar wadda bata kallon gabanta?"
TafaÉ—a tana mai kallon yatsan nawa.
Rintse idanuna nai sabida zafin dana keji sosai ga zazzaɓin dayake damuna.
"Wallahi anty jiya naisa a bakin ƙofa bamma zaton ze zaman haka ba, wallahi bakiji yadda yakemin zafi ba kamar ze fitar min da yatsana".
NafaÉ—a ina mai rintse idanuna kaÉ—an.
"To Allah ya sawwaƙe ya kuma kare gaba Allah ma yasa yau babu makarantar yaran da sedai ki fashi bara a kawo miki abincinki nan inyaso seki sha ko panadol ne insha ALLAHU zakiji afuwa".
Fita tai anisa ma tai mini sannu tabi bayanta.
Can kuma segata dauke da kwanukan abincin karyawa ta diren agabana, Godiya nai mata sannan na sauko ina É—ingisa kafar a hankali nake tafiya harna nufi gaban kayana na zaro zani na É—aura sannan na matsi maclean na É—auki brush na nufi tsakar gida.
Wanko bakina nayi tare da fuskata na koma ɗaki agaban a bincin, na zauna na saka hannuna na buɗe kwanukan tuwone ɗumame da miyar kuɓewa jan murfin nai na rufe sabida tsanar danaiwa tuwo ko kaɗan bana ƙaunarsa jan jikina nai na koma saman gado na ƙudunduna abina ban wani jimaba bacci mai nauyi ya kuma fusgata.
*********
A wani haɗaɗɗan gidan cin abinci yayi parking seda ya gyara dai dai ton motar tasa,Sannan ya kasheta ya fita waje yana mai shaƙar iskar dake kaɗowa daga sararin samaniya, taka ƙafafunshi yayi ya karasa shiga cikin wajan.
Direct wajan order ya nufa yaje yay order abinda yake buƙatar suci shida yaran nasa sannan ya nufi wajan biyan kuɗi akai amfani da Atm card ɗinsa wajan biyan kuɗin.
Hannunshi É—auke da manyan ledoji masu tambarin wajan cin abincin guda biyu ya nufi gaban motar shi ya bude gidan baya ya zuba ledojin sannan ya zagaya wajan driver ya shiga yaja motar ya nufi hanyar gidansa.
Tafiya yake cikin nutsuwa yana lissafa lamuran rayuwa waÉ—anda suke faruwa ga bawa.
Yau zakaga safiya tayi anjima zakaga azahar tayi daga nan se yamma se dare gaba ɗaya rayuwar gudu take wadda wasu daga cikin bayi basa gane yadda rayuwar take sema wata algaita da shaiɗan da muƙarraban sa ke buga musu.
Lumshe idanuwan sa yayi tare da furzar da sassayan iskar cikin bakinsa yana mai hasaso lamarin duniya yadda yake tafiya, Komi na rayuwa akwai geji tare kuma da iyaka wallahi a wannan aikin nashi yaga abubuwa da dama waÉ—anda suka basa tsoro ainun.
Babban abinda yake daÉ—a daure masa kansa shine yadda a yanzu wai mutum yazama abokin tsoron É—an uwansa mutum a yanzu, In bakai taka tsan tsan da rayuwarkaba sekaji ance babu kai, yanzu wasa ake da rayuwar mutum kamar ba a bakin komi ba, babban abin da ya kuma É—aure masa kansa shine.
Case É—in wannan mutumin wanda ake xargi yana garkuwa da mutane, shi baban yaran da aka É—auke abin da yake faÉ—a masa last week dayaje office É—insu shine.
Business yake na kayayyakin masarufi yana zaune a shagonsu na kasuwa kawai sega wannan mutumin yazo yace mai zeyi siyayya ta kimanin maƙudan kuɗaɗe, waɗanda suke da daraja.
Bayan sunyi cinikin ya amshi accnt numbern sa ya tura masa da waÉ—an nan kuÉ—aÉ—en.
Bayan sati É—aya still ya kuma zuwa yay masa siyayya wadda tafi ta farko kuÉ—i sedai a wannan karon bai basa kuÉ—in duka ba seya bashi rabi seyace masa ze masa ciko Da zarar wasu kuÉ—i sun shigo masa.
Ranar da mutumin ya kirasa akan cewar ze kawo masa kuÉ—in se akai akasi yana gida baya shago amman seya ce mai ya tura mai ta accnt,A lokacinne mutumin yace wai accnt nasa ya sami matsala in ba damuwa yay masa kwatancen gidansa ya kawo masa mana.
Cikin yadda yay masa kwatancen gidan nasa da daddare yazo masa da kudin bayan sunyi waya ya shaida mai yana kofar gidan.
Fita yayi ya amso kudin kana sukai sallama.
Tafiyar mutumin da kwana ɗaya aka shiga gidansa aka ɗaukewa matarsa manyan sarƙoƙi na gwall sannan akai gaba da ƴarsa mace da kuma yaronsa namiji.
ÆŠimuwa tashin hankali sun shiga, sedai abinda ze baka mamaki yadda aka kira wayar uban nasu akan cewar seya bada kuÉ—aÉ—e masu kauri sannan za,a sakar mai yaran nashi wannan dalilin yasa mahaifin yaran ya garzayo office É—insu ya bada report wanda nan da nan suka baza jami'ansu akan suyi bincike akan al'amarin wanda suka dauki wajan sati uku suna faman abu guda.
Wanda cikin hukuncin Allah suna ta samin nasara akai.
Wannan aikin ne ze kaishi kano nan da kwanaki guda, domin ya ƙara bincikar sauran waɗanda abin ya shafa kamar yadda jadawalin aikinshi ya basa dama.
Da wannan tunanin ya ƙarasa gida jikinsa a mugun mace.
Baya kaunar abinda xe saka ya tafi yabar yaran nan nasa a gida batare da wani ba.
Amman ya barwa Allah ikonshi domin shine mai tsare kowa.
Parking ya gyara a bakin gate ɗinshi sannan ya kashe motar,Ya shiga gidan kofar falon ya tura babu kowa a falon se Ƙarar tv.
Gaban tv'n yaje ya kashe sannan ya zube ledojin daya shigo dasu a falon ya nufi kofar dakinshi, alwala ya É—auro a toilet sannan ya fito falon still baiga kowa ba.
Baiko dubi dakin sakina ba ya nufi É—akin yaran nashi.
Hannu ya saka ya murÉ—a handle É—in kofar tare dayin sallama.
Islam na zaune saman sopa tana duba littafin azkar a hannunta, wanda ya zauna ya koya mata, shikuwa aslam yana raɓe a gefenta yana kallon yadda take karatun nata.
Gabansu ya karasa ya zauna a gefen, su ya É—aga aslam yana mai cewa.
"My boy bazaka kula daddyn naka ba?"
Dariya yaron nasa yayi yana mai kwantar da kansa a jikin mahaifin nasa.
Itako islam batai magana ba har ta kammala azkar É—in nata ta shafa sannan ta mike.
"Daddy sannu da dawowa"
Abinda ta faÉ—a mai kenan taja jikinta tabar mai É—akin.
Murmushi kurum yayi ya bi bayanta aslam a hannunshi.
Tana xaune a kasan carpet tai tagumi.
Cikin damuwa ya zauna a gabanta ya saka hannu ya cire mata tagumin nata.
"Bebyn daddy waya taɓamin kene?"
Ya faÉ—a yana tsareta da idanunshi.
Tura baki tai gaba tana kokarin yimai kuka!.
"Daddy bakai ne katafi kabarmu ba,inata kiranka kaimin banza".
Seta saka mai kuka! wanda hakan ya kumayi dai-dai da zuwan sakina falon wadda taci ado na burgewa.
Da sassarfa ta karaso gaban islam tawani kamota cike da kirsa.
"Ambebi na, waya taɓamin ke kike kuka tunda kika shigo nike maki magana kinmin shuru, ko daddy ne?"
Gaba ɗaya ido suka zuba mata daga islam ɗin har aslam ɗin suna kallonta wanda hakan ya bawa umar damar fahimtar wani ɓoyayyan al'amari a tare dasu ɗin.
Cikin rashin sabo da hakan, islam ta janye jikinta.
Kallo tabi mahaifinta dashi cikin kuka tace mai.
"Daddy dan Allah ka kaimu wajan maman kano, dan Allah daddy bama jin daÉ—in zama babu ita anan gidan...........
#AUTAR MANYA
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.