Complete Hausa Novels

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 27 of 33

*ina mata ƴan ƙwalisa? shin kokunsan ƙamshi da gyara shine mace? to matso na baki bayani shahararriyar mai haɗa turarukan mata da kuma kayan gyaran jikin mata wato maman noor yanxu ma ta kara xuwar muku da xafafan kayan ƙamshi dana gyara jiki domin kara kankaro miki da martabarki wajan oga ga kayan nata kamar haka*👇🏼

Turaren wutane
Humrh
Kulacham
Turaren wanka
Turaren Kaya

Gyaran jiki
Na amare
Da masu jego

Da magungun nan mata
Irin su kaza
Tantabara
Tsumi
Gumbar
Zuma
Sauran bayani dai in mutum yamin magana na masa
*gamai neman karin bayani seya kira*👇🏼
Ummu noor
08067807620
09057713999

*ZUMA A BAKI* _Is not for free book domin neman ƙarin bayani seki tuntubi wannan numbern 08142105218_

*Albishirin ku masu son karanta ƙayatattun labaran soyayya masu narkar da zuciya gami da ilimantarwa da faɗakarwa to gada ma ta samu ki nemi waɗannan zafafan littatan waɗanda aka baje soyayya mai tsayawa a zuƙatan makaranta cikinsu*👇🏼

*AUREN BARE*
*H A S K E*
*KOBA SO*
*DA IZZATA*
*ÆŠAN MAJALISSA*

_Nemi wannan numbern 08142105218 duk É—aya akan farashin naira 300 ne amman idan siya zaki gaba É—aya xaki biya naira 1000 É—aya ne_
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *53 & 54*

A matuƙar firgice na dubeta tare da cewa.
"Anty zamu wuce kuma?".
Kallona tai cikin É—an zafin rai kaÉ—an.
"Eh! zaku wuce mana ko bazaki ba naje na shaidawa ubanki?".
Idanuna cike da tarin takaici nace mata.
"A,a ni bazanwa baba gardama ba amman dai nikam bangama shirina ba ko dolene seya tafi dani?".
NafaÉ—a idanuna na zubar da hawaye mai yawa.
"Fatima ku bani waje sannan ku turomin uwani".
TafaÉ—awa su fatiman anty zulfa cike da bada umarni.
Fita sukai daga É—akin inda yarage dagani se ita sekuma sautin kuka na dake fita.
Sallamar anty uwanice tasa naÉ—an tsagaita da kukan danake yi.
"Uwani gata nan seta kuma gaya miki uban daya sakata kuka wallahi na soma gajiya da halin humaira sabida haka zan zuba miki idanu ai bake kaÉ—ai ke gareni ba haba sekace wata yarinya".
Anty ta faÉ—a cike da tarin takaicina.
Zama anty uwani tai fuskarta a É—aure.
"Kiyi haƙuri anty ki zauna ai magana ai bakya yi fushi da itaba rabuwar farin ciki akeso kuyi bata ɓacin rai ba".
Cewar anty uwani.
"Haba uwani wallahi na rasa irin taurin kai na yarinyar nan abin da nakeso ta gane a yanzu kotai wani auren wallahi bazata sami kwanciyar hankali kamar na gidan umar ba, ki duba rashin kirkin data dinga shuka mai lokacin suna tare ai koda zugar ƙawa itama da ɓurɓushin halinta na taurin kan tsiya, amman yaron nan duk ya mantasu ya kuma kawo kansa akaro nabiyu to kodan ki koma gaban ƴaƴanki bazaki farin ciki ba, munafukar Allah ai duk bakinku guda da umar din amman anan kita nuna bakya sonsa wallahi uwani nagama da humaira nagama ganota kukan munafurci take domin gaba ɗayansu babu mai gaskiya daga ita harshi ɗin kowa ya afu da ɗan uwansa".
TafaÉ—a tana mai kuma zama a gefe na.
"Nifa anty wallahi bana sonshi........"
Bugemin baki tai wanda har seda tajimin ciwo.
"Idan kika kuma cewa bakya son umar wallahi senai miki baki!!! dan ubanki ke wace irin yarinya cene? zuwa xaki ki kuma kaso auren ki dawomin?.to wallahi kika kuma kasowa sedai ki nemi wata uwar badai niba wallahi kinji na rantse tun dake shasha shace".
TafaÉ—a a matukar fusace tare kuma da bar mana É—akin.
"Kingani ko?.yanzu hankalinki ya kwanta kin ɓatawa mahaifiyarki rai ko?".
Anty uwani ta faÉ—an haka.
Kuka na rushe dashi ina mai dafota.
"Anty uwani umar ya rainamin hankali Anty bani nacewa umar ina son kome ba amman sabida ya rainani yana ganina a arha shine yaje ya haɗa karya wajan baba har aka mayar da auren batare daya nemi jin ra'ayina ba sukuma su baba sabida sun ganni a motarsa suka amince sabida yay min ƙofar rago kwanakin baya, Anty uwani wallahi bada ban ƴaƴana ba sedai duk wadda za,a ayi amman da bazan koma mai ba kuma.wallahi kona koma yanzun ma seyay biko yay duk abin da bai ba ada sannan zega fuskata".
NafaÉ—a cikin kuka!.
"To nidai dan Allah humaira ki nutsu ko iyayenki suma hankalinsu ya kwanta sannan dan Allah kada ki ɗagawa waccan baƙar gadarar ƙafa dai dai dana minti ɗaya idan tai miki ki mata ki nuna mata nan ɗin kece dashi domin gidankine dana yaranki, Amman umar kam ki sassauta mai domin a farko baiji daɗinki ba dan Allah wannan karon ki buɗe ƙafa yadda ya kamata karki mai rowa domin mu zuri'armu basu gaji rowa ba kula kirsa tarairaya tsafta kula da ibada duk ki rike insha Allah da sannu ALLLAH ze kawo mana karshen komi".

Tura bakina mai kamar ƙaramar yarinya.
"Nifa ba yau zan koma ba yabarni nagama shirina na taho daga baya".
Da kallo ta bini.
"ki tashi malama ki tattara kayanki karnaji karna gani ehe!".
Ganin fuskarta babu saukine yasa na tashi gaban sif ɗina ta kaya naje na soma haɗawa cikin gajiya na kammala su acikin wata ƙatuwar trolly se lokacin ta fita daga ɗakin ganin da sauran time yasa naje nai wanka na ɗauro alwala nai sallar la'asar tare da yin azkar.
Dayake garin akwai É—an sanyi yasa na shafa mai tare da zira riga da skirt na karen muski jajaye masu kauri.
Sena É—ora bakin mayafina kato akai kana na fita É—akin anty.
Bamma sameta ba tana can É—akin baba dan haka can É—in na bita lokacin wajan biyar da minti goma, gaisar da baba nai anan ya soma yimin nasiha mai ratsa jiki kamar haka:.
"Humairah kibi mijinki sauda ƙafa kiyi koyi da mahaifiyarki gata nan wallahi bata taɓa saɓamin ba, bare nai tunanin ƙara mata abokiyar zama ko saki! sannan ki tafi gidan mijinki da zuciya ɗaya karki yarda zuciya ta ɗebeki ki rama sharri da sharri ki zama mai yafiya sannan ki zama mai rama sharri da alkairi, Kinsani na sani duka mun sani ƙawarki ta cutar dake amman ki ƙaddara hakan a matsayin kaddarar Allah wadda ya tsara tun fil azal daman can dole seta dalilinki zata auri mijinki seki lissafa haduwarku da ita wadda ta kasance ta sila wadda daman can ALLAH ya ƙaddara........
Kome kikaga ya sami bawa tofa akwai sila da kuma ƙaddarar faruwa wadda baka taɓa sauyata, idan mukace duk abinda akai mana na sharri zamu rama da sharri tofa da duniyar tamu ta tarwatse tuni, sabida haka kiyi koyi da hakuri halin Annabi muhammadu (s.a.w) Wanda ansha haɗa masa makircin dayafi namu amman yay hakuri kuma ya nufi waɗanda suka haɗa masan da alkairi daga ƙarshe meya faru? su sun taɓe shikuma Allah ya ɗaga darajarsa ya kuma ƙara tsare shi daga dukkan halaka,sabida haka humaira ni a matsayina na mahaifi gareki ina mai horarki dayin hakuri dayin yafiya da kuma kawar da kai domin kawar da kai ɗabi'ace ta manyan mutane dan Allah kada ki tafi gidan umar da niyyar ɗaukar fansa ki tafi da niyyar neman aljannarki insha Allah ubangiji ze mi luɗifi da'imi duniya da lahira kinji ƴar albarka".
YafaÉ—an muryarshi na rawa.
Kuka na saka na wannan nasihar ta mahaifina domin ta ratsani ta shiga jikina ada na ƙullaci sakina araina na nuna cewar nima zan rama dukkan abinda taimin.
Amman yanzu kam bana jin zan iya mayar da sharri da sharri sedai na mayar da alkairi ga sharri sannan kuma bazan taɓa zuwa da zummar ɗaukar fansaba zanje da zummar neman lahirata nasan Allah yana bayan mai gaskiya kuma insha Allah gaskiya zatai halinta.
Amman dai babu zancen wani aminci ko shigewa jikinta sedai araina babu ƙullinta Cikinshi.
Tunanin danake yine ya tsaya cak lokacin danaji sassanyan ƙamshin turaren dayake kunno kai cikin ɗakin.
"Assalamu Alaikum".
Naji sautin muryarshi acikin kunnuwa na.
Da sauri nai ƙasa da kaina tare da rintse su sabida haushinsa danakeji yasa bana son ko kallonshi.
"Amin wa'alai kassalam".
"A,a umar harka fitoma ashe? lale maraba sannu kaji É—an albarka".
Kansa a sunkuye kamar munafuki naji yana gaisar dasu baba.
Niko bai sami arzikin kallo ba bare na gaisar shi sema cigaba da tunani danai.
"Umar ga humaira nan na baka amanarta a matsayina na mahaifin ta bazance maka komai ba game da ƙarancin shekarunta domin har yau bata haɗa ashirin a duniya ba sabida haka wani abun sekai mata uzuri, sannan intai ba dai dai ba ka dauki mataki bata da uwa ba ta da uba acan ɗin bata da kowa se Allahn daya halicceta sekuma kai dan Haka ina mai jaddada amanarta gareka umari Allah ya baku zaman lafiya da'imi".
A ƙasan laɓɓan sa ya amsa da amin amman can cikin xuciyarshi yana mamakin halinta har yau baxata sauya ba, ai ko banza ta gaisar dashi amman ko arzikin kallo baima samu ba tome take nufine?...........

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.