Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 25 of 33
Gamai buƙatar karanta littafina sabo wanda zezo a farkon sabuwar wannan shekara mai zuwa ze biya
*BAƘAR FATA*
(Romantic story)
Norma grp#300
VIP#500
Sp#1000
Complt#1000
Accnt#0078174806 starling bank then show me your evidance of payment ina maraba da masoyana Æ™ashin bayan nasarata one loveâ¤ï¸ðŸ’¯
*GABA ÆŠAYA SADAUKAR WANE GA*
*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹
             *49 & 50*
Cikin sakin fuska baba ya dubi umar yace masa.
"Barkan kadai Umar, dafatan kana lafiya yaya iyalin naka?".
Murmushi ya sauke yana mai saka hannunshi ya shafo sumar dake saman kansa.
"Lafiya lau nima nazo wani É—an aikine kanon dafatan kuna cikin koshin lafiya?".
"Alhamdulillahi umari ashe kaida humaira ne, shiyasa naga tai gida aguje ja'irar yarinya".
Cewar baffa ƙananin baba yana dariya.
Cikin tausasan kalamai yacewa baba daman magana ce dashi in babu damuwa ze dawo nan da magari ba.
"A,a umari haba sekace bako muje shagon zaure mana muyi maganar tunda naga da sauran lokaci kafin ayi magaribar".
Bai misaltawa baba ba haka suka rankaya sukayi cikin gidan a shagon soro baba ya gyara mai wajan zama kana ya zauna.
Cikin nutsuwa ya kalli baffa domin baze iya duban baba da maganar ba sabida kunya wadda tunda ya saketa bai taɓa waiwayarta da sunan biko ba se yanzu.
"Baffa daman mungama magana da Aisha akan cewar ita tafi son ta koma sabida Æ´aÆ´anta shine nazo na baku hakuri baba ataimaka Aisha ta koma wajan yaranta".
Tsit! shagon yayi kafin baffa yace mai.
"To Alhamdulillahi Umar daman mu a kullum gyara mukeso ba ɓarna ba sabida haka tunda har ita humairan da kanta tace taji tagani zata koma ai babu wani abu semuyi muku fatan alheri Allah ya saɓa hali".
Da amin baba ya amsa.
Anan suka gama maganar da zasuyi kuma atake anan baffa ya amshi wakilcin humaira akaro na biyu shikuma baba ya amshi na umar sadaki ya bayar bayan haka suka bar maganar akan gobe za,a daura aure.
To bayan kammala wannan gidan imran ya wuce ya sami kanwarsa maryam É—auke da tsohon ciki ko ruwa ma bai tsaya yasha agidan ba yayi gidan inna sabida imran É—in baya nan yana wajan aikinsa wanda bayan kammala karatunshi shima ya sami aikin banki anan wani sabon banki shiyasa haduwar tasu take wuya sabida yanayin aikin kowa sedai duk wata tattaunawa suna yinta a waya.
Innah tana tsakar gida tana faman gyara zogalan ,dazatai miya sallama yayi ya shigo tare da neman guri ya zauna a gefenta yana gaisarta.
kada ran kada han ta amsa mai domin ya bata haushi jiya akan abinda yay ma humaira a waya.
Bayan wajan yay shuru kamar babu kowa inna ce ta dubeshi.
"Umar umarni nake baka akan kaje ka dawo da uwar yaranka wallahi a wannan karon bazan ɗaga maka ƙafaba nagama magana ta".
Tafaɗa ranta a ɓace.
"Inna yanzuma daga gidansu nake kuma insha Allahu gobe zata zama matata akaro na biyu".
Jiyowa tai ta dubeshi.
"Kai dan Allah umari da gaske kake?".
Cikin tsantsar mamakin soyayyar da innah kewa aurenshi da humaira ya dubeta yau ta soma kiran sunanshi domin bata faÉ—a sabida kara irinta É—an fari.
"Innah da gaske mana nake kedai ki mana fatan alkairi wallahi innah tunda na saki yarinyar kawai rayuwa nake amman komai baya min daÉ—i".
YafaÉ—a cikin damuwa.
"Yo daman kai waya gaya maka ana saɓawa Allah a zauna kalau? ai saki baya daga cikin abinda Allah yakeso musamman idan anyishi cikin ganganci da kuma sauri shin wai mai ma yasa tun lokacin bakai tunanin mayarta ba?".
Ransa aɗan ɓace idanunsa jajir ya dubi innah.
"Wallahi innah lokacin na kasa controlling na kaina ne sabida abinda ya faru".........tas ya kwashe duk abinda yagani alokacin da abinda humaira kemai ada ya sanar da ita.
"Inna na rufeki ne sabida kada kiga baƙinta har watarana nazo nace zan mayarta kiƙi yarda, sannan kuma nima daga baya nai nadamar saurin sakin danai domin anan shine kaɗai laifina tare kuma da rashin bincike inna se jiya data ganni a datti wanda banga ƴa macen dazata ganka a haka ta kulaka ba inba mai tsananin sonka ba innah inkinga yadda Aisha taita kuka akaina abin ze baki mamaki".
Ya dakata yana lumshe idanunsa.
Innah kuma cewa tayi.
"Allah sarki yaro ashe har yau kana nan da wannan xurfin cikin naka? shin mai yasa bakai kokarin sanar dani komi ba alokacin ai da tuni maganar ɗanka na wajan huɗu ake da humaira domin bazan zuba ido aurenku ya salwanta ba da tabbas zanyi iya karfina domin ganin na tare wannan ɓarnar".
Da sauri ya tari numfashinta.
"Innah bazaki iya ba! domin babu wani mahalukin daya isa ya tarewa wani bawa ƙaddarar da Allah ya ƙaddara zata sameshi sabida haka ƙaddarar aurena da humair tun fil azal samammiyace dan haka innah babu wanda ya isa ya gyara abinda Allah ya raba gashi nan se yanzu da lokacin dai daiton yayi Allah ya ƙullah komai cikin nutsuwa".
Mayar da ajiyar zuciya innah tayi.
"To hakane yaro Allah na tuba da wancan kalamin nawa na É—azu, to amman mai yasa kai lokacin daka ganta da wannan bakai nazarin wani abuba kawai ka saketa sannan mai yasa baka tambayeta akan mai ya kawosa ba? dan kawai kafin ta aureka suna soyayya seya zama cewar da auren nata ma zasuyi kenan? kai ganganci yaro domin zartar da hukunci babu bincike bakaramar illah bane arayuwa hakanan yana kawo nadama mai yawa".
"Wallahi innah sam kaina bai kawo hakan ba se bayan dana rabu da ita sannan naga rashin adalcina nayin biris da bincike akan abinda ya kawo afkuwar hakan amman yanzu alhamdulilahi tunda zata koma É—akinta".
A É—age ta dubeshi tana murmushi.
"Amman koda ta dawo É—in yana da kyau kai bincike akan abinda ya haidar da waccan matsalar domin muddin bakai bincike ba ina mai tabbatar maka da cewa wallahi setaga tafi ta baya illah".
Gabansa ne ya faÉ—i baki sake kuma yana kallon mahaifiyar tashi.
Ƙarar wayarsace ta dawo dashi a tunanin daya afka.
Bayan ya ɗaga bayani ogansa kemai akan amfa gano ɗayan mutumin nan na naija wanda suke haɗaka da habu ɗan ƙwai wajan garkuwa da mutane, yanzu yana son ya kuma turamai da bayanan cigaban da aka samu anan ɗin.
agurguje yaywa inna sallama ya fita daga gidan ya kama hanyar hotel a daren ranar ya kammala tura bayan sa sannan ya afka tunanin mafita akan umarnin da innah ta bashi wanda zuwa washe gari yagama yanke shawarar zebi komi a sannu har Allah ya bashi sa'a gefe É—aya kuma ga tarin damuwar kewar yaranshi wanda kullum ya kira sakeena a waya setace mai bata kusa wanda hakan ya kuma hasko mai akwai abinda yaran ke fuskanta game da zaman gidan nasu tare da ita.
MONDAY MORNING.
Cikin shiga ta alfarma ya kintsa kansa kallo É—aya zakai mai kasan yana matukar farin ciki ayau É—in amma tsabar basar da abu arai yasa baxaka fahimta ba.
Waya sukai dasu salim suna mai shaƙiyanci wai ungulu ta koma gidanta na tsamiya haka yayta biye musu kafin ya sauka ya faɗa mota seda ya biya gidan innah yay break fast sannan sukai waya da tsoho kakansa wanda yay masa fatan alkairi wajan karfe goma yabar gidan innah ya wuce nan kofar gidansu humaira anan suka haɗu da abokansa aka hau gaggaisawa tare da tsokanar juna kafin su wuce wajan daurin auren wanda ya sami halartar mutane masu yawan gaske.
Ƙarfe sha biyun ranar litinin wanda yay dai dai dai ga 1/1 dubban mutane suka shaida daurin auren UMAR MUHAMMAD SARKIN GIDA DA AISHA YUSUF NUHU, akaro na biyu.
Bayan gama daurin aure kuma walima suka wuce wadda abokansa sukai masa bazatar haÉ—ata domin baya da masaniya akanta.
Anci ansha an hantse daga nan tafiya yay ya kuma cire kayansa ya kuma komawa wajan bincikensa.
Cikin amincin Allah ayau dai a mahaukacin tuburan yajewa habu ɗan ƙwai domun seda ya sami sa'ar faɗawa cikin gidan wanda daman burinsa kenan..........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.