Complete Hausa Novels

Zuma A Baki Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma_A_Baki_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 32 of 33

Umar kuwa sosai ya sami shaidar karin girma tare da karramawa akan aikinsa sosai ya taso gida cikin farin ciki sabida yadda aikinshi yay kyau ma'ana an kama waɗan nan ƴan garkuwar ta dalilin binciken dayay harma an mikawa alhaji wada mai wake yaransa su habu ɗan ƙwai kuma an mika su ga hukuma wannan namijin kokarin da umar yay ne yasa hedqauter ɗinsu ta ƙara masa girma tare da shaidar karramawa harma da hutun sati biyu agida.
Haka ya taso gida batare dayaje dauko yaransa ba sabida lokacin ba,a tashesu a school ba.
Ahanya nekuma alhaji wada ya kirashi bayan sun gaisa yay masa godiya sosai sannan yace yana mai albishir daya basa sabon gidanshi dake kano anan unguwar gaida sannan kuma ya biya masa hajji bana kujera biyu.
Mamakin wannnn kyauta umar yay amman seyay masa godiya ya kashe wayar yanata mamaki daman wannan karon yakeson yasai fili ya soma gini kuma segashi Allah ya kawo masa ta hanya mafi sauki harda kyautar kujerar makka biyu wadda atake anan yay sadaukarwarta ga baba da innah.
Tabbas yasan yaywa alhaji wada kokari akan yaransa amman bai É—auka zemai irin wannan kyauta haka ba tabbas wasu mutanan sunsan alkairi komai kankantarsa.
Da É—aukin waÉ—an nan albishir ya fafari motar yay gidansa.

Nazeer karfe goman safiyar litinin tai mai agarin abuja bayan yaci dogon kudiri aransa kai tsaye a kofar gidan umar ya yada zango.
Sakina dubarar aiken mai gadi tai kafin ta leko ta shigo da nazir gidan sabida bata tunanin umar ze dawo a wannan lokacin.
ÆŠakinta takaisa taÉ—an tura kofar tana masa bayani.
Tunda ta soma masa magana ya kafe da mici micin idanunsa yana ayyana lallai sakina jakace.
Tashi yay tsam ya kamota ya wurgata saman gadon aurenta na sunna yabi ya haye kanta yana lasar fatar wuyanta.
"Lallai sakina ke dabba ce kin manta furucinki na karshe gareni? mai kika mayar dani daƙiƙi koko soko? to yau nazo dominki na dauki fansata wadda naketa shirinta segashi kin bani hanya mai sauki akan ɗaukar tata".
Da wani irin tsoro ta tureshi.
"nazir kana hauka da aurena mai zakai min dan Allah kada ka ketan haddi na tuba dan Allah dan Allah".
Dariya ya saki.
"Hmm sakina mai tsoro ga ban tsoro ke wace irin marar imanine da auranta zaki rabata da yaranta da mijinta akaro na biyu? alhalin ke bazaki iya rike masu suba? au ke kinsan darajar naki auren amman baki san na wani ba kawarki aminiyarki kika yaudara aidaman kinsan karshenki koba afaÉ—a ba"
"Niba burina nazo nai zina da matar aure ba domin duk barikina nasan gejin yinta nazone domin mijinki yazo ya kamamu ahaka har hakan tasa asirin da kika rufe ya tonu".
Wannan furuncin yay dai dai da lokacin da umar ya shigo gidan ya tura kofar dakin humaira yajita arufe seya nufi na sakina tura kofarsa yay dai dai da sanda yaga katon gardi akan matarsa akuma kan gadonsu.
Jikinsa yana rawa ya bugawa nazer tsawa wadda tasaka nazeer dira daga saman gadon jikinshi yana faman mazari.
Wata shaka yakaiwa nazeer wanda ya kusan kaisa kiyamata kafin ya haÉ—esu shida sakina yahau jibga abinka da tsohon É—an tauri gakuma kirar karfi seda ya tabbatar sun daku sannan ya watsosu falo.
Ihunsune ya farkar dani da gudu naja hijabi nai falo ganin yana kokarin kisan kai yasa nasha gabansa.
"Hy umar control your mind sekai kisan kai"

Idanuna arufe seda na bude nai katari da nazeer durkushe bakinsa yana É—igar jini sakina kau tana kwance tana mayar da numfashi.
Da mamaki na dubesa.
"Nazeer mai ya kawoka gidan nan?".
Da rarrafe yazo gaban umar ya rike mai kafarsa.
"Kai hakuri officer kozaka kasheni wallahi sena faÉ—i gaskiya.............................."
Komai AtoZ seda nazeer ya faɗawa umar tundaga haduwarsu da sakina da komai hatta kawancenmu kai wani abunma ban sani ba ni kuka ma kasa zuwarmin nai saɓanin ya umar dayake kuka kamar mace.
Kafin nazer ya fito da wayarsa ya kunna recording É—in daya dauka na makircin datake shirin haÉ—amin ya kunna afili a wannan karon kuka na saka wato bani da laifine yasa Allah yay gaggawar kawon sakayya domun wallahi inda nazeer bai amsa mata ba da wani xata nemo tunda bata da imani.
"Tayaya rayuwa zatai dai dai bayan na jikinka dashi ake cutar dakai tayaya duniya zatai lafiya bayan zamba acikin aminci yay yawa macuta sun yi yawa maha'inta sunyi yawa tayaya zamuga dai dai bayan muna bakin ciki ga junanmu hassada ƙyashi sun mana katutu ƙawarki aminiyarki kikaiwa haka wadda ta baki dukkan yarda wallahi nai tirr dake daman ina kan binciken silar bayyanar wannan saurayin a kofar gidana sekuma Allah ya sawwaqa komi lallai sakina kin cika macuciya sakamakon cutarki kije na sakeki saki biyu kuma gaki ga duniyar nan".
"Kaikuma kaje idan zaka shiryu ka dai daita rayuwarka kamar kowa kayi idan kuma bazakai ba kaje duniya ce tafi bagaruwa jima".
Gabana nazeer ya nufo yana kuka yana neman yafiyata akan yaudarar dayay min da kuma sanadin kisan aurena na farko.
"Nazeer na yafe maka wallahi kodan namijin kokarin dakaimin kaje Allah ya yafe maka amin".
Da gudu yabar falon yana kuka.
Itako sakina wata janyowa umar yay mata ya wurga waje bayan ya naÉ—a mata matsiyacin duka babarta ya kira awaya ya sanar mata sannan ya kira innah yana kuka yana shaida mata.
"Hmm yaro kenan aini tun ranar da humaira tabar gidan nan naji komi abakin sakinar inda take gayawa humaira bata san ina jiyosu ba wallahi yaro abin yay min zafi karka manta wannan dalilin yasa nace maka kaita bincike domin ni babbace bazance komi ba to Allah yasa rabuwar takuce tafi alkairi".
TafaÉ—a sukai sallama.
Zubewa yay agabana yana kuka a saman kafafuna.
"Dan Allah ki yafan aisha ban kyauta ba nai aiki daka ashe makashinki yana tare dake amman why baki taɓa sanar dani ba?".
Nima zubewar nai gaban sa ina kuka na cusa kaina a kirjinshi
"Allah na barwa nake addu'a gashi nan cikin sauki ya bayyana gaskiya karka damu daman rayuwar ta gaji haka ba,a taɓa samun nasara se an fuskanci kalubale nagodewa Allah dayasa tafiyar batai nisa ba da tuni an cutar dani fiye dana baya".
Rungumeshi nai mukai ɗaki na taimaka mai yay wanka har lokacin ransa yana ɓace.
Da dubara nake jansa da hira anan yake shaidamin abinda ya faru gareshi fatan alkairi nai masa tare da mikewa na fita na gyara falon na wuce kicin raina fess.
Tsahon kwanaki rayuwa muke mai cike da farin ciki kayan É—akin sakina yasa an fitar dasu É—akin ya koma nawa nasa kuma ya zama nasa kenan sekuma na yara.
Kwanci tashi har nai wata biyu agarin abuja maryam ta haihu bai barni naje ba haka akai bikin sadiya nanma ya hanani zuwa nuratu kam abuja aka kawota da zama kusan kullum ma muna tare domin tana yawan zuwa nikam tunda na koma banzo kano ba sabida yanayin danake fama dashi na juna biyu.
Bayan wata biyar.
Sakina kam da barance ta sami kudin motar kano gaba ɗaga rayuwa ta juya mata tai danasanin cin amana domin bata kwashe mata da daɗi ba agidansu kuwa uwarta tai mata tass takuma ce sedai ta bar mata gidanta da ƙyar makota suka saka baki ta zauna sedai abincin dazata cima setai wankau da gogau take samu takai bakinta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.