Complete Hausa Novels

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 10 of 51

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“

*RAYUWA* page1⃣9⃣to2⃣0⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

D.B.W.A

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

Komawa kitchen d'in tayi suka k'arasa girkin, bayan sun gama Hadiza ta zuba a kula tace Hibbah ta d'auka sukai parlor. D'auka tayi suka shiga parlor'n lokacin ma babu kowa a parlor'n, tsayawa tayi Hadiza tayi gaba ita kuma tabita a baya dinning area suka nufa Hadiza ta jere kayan akai tacewa Hibbah"ki rik'a lura da abubuwan da nakeyi don wannan duk aikin kine," Hibbah ta d'aga kai tare da cewa to.
Haka suka k'are jera abincin akan dinning suka koma kitchen suka d'auki nasu Wanda Hadiza ta ware musu, d'akin da hadiza tace nasune suka koma Hadiza ta zuba musu sukaci tare. Hibbah sai taji matar ta burgeta yarda take janta a jiki ba kyara bare hantara, Hibbah tayi shiru tana tunani da tana k'auyensu da yanzu ta dawo daga islamiyya inna ta d'ora mata tallah, sai kuma ta tuna ashefa ta bar gidansu tana gidan gwaggo. Tana can duniyar tunani ta tsinci muryar Hadiza cikin d'aga murya tana cewa "Hibbah! Wai me yake damunki ne? Tunanin me kikeyi?" Numfashi Hibbah ta sauke tace "ba komai baba," Hadiza ta kalleta tace "a'a Hibbah da akwai wani abu, kinga fa abincin da kike ci kin dena, kin tafi tunani fa kuma hawaye a fuskarki ko dai kewa gida kike yi?" Da sauri Hibbah ta d'aga kai, Hadiza tace "ai sai hakuri a hankali ma zakiga kin saba da nan d'in musamman ma kika rik'e dokokin hajiya zaki zauna da ita lafiya don hajiya bata da wata matsala, sai dai yaranta wannan 'yammatan su biyu sune masu matsala, suma idan kika bi duk abinda suka ce miki suma baki da matsala dasu." Hibbah ta girgiza kai cike da gamsuwa tace "to baba na gode, amma menene dokokin hajiya da 'ya'yan nata?"
Hadiza tace "gaskiya hajiya macece mai son tsafta bata son k'azanta ko kadan, sannan tana son mutum mai gaskiya da rik'on amana, tak'i jinin rashin kunya tana son taga kana mutuntata da yaranta, idan kikayi haka sai kiga hajiya na sonki wata k'ilama tasa ki a makaranta kamar yadda tayiwa dije gata tasa ta a makaranta ta d'auketa tamkar 'yar cikinta daga baya dije tazo tana yi Mata d'auke d'auke, har yakaita da d'aukar sarkar hajiya ta gold." Zaro ido waje Hibbah tayi tace "sata?" Hadiza tace "wallahi kuwa, shiyasa ma hajiya ta koreta," Hibbah ta girgiza kai tana mamakin wannan lamari can tace "insha allah zanbi duk dokokin hajiya kuma Zan kula da dukkan ayyukana." Hadiza tace "Allah yasa," "ameen" Hibbah ta fad'a tana mikewa ta d'auke plate d'in dasukaci abinci takai kitchen tare da wanko hannunta,
Tana shigowa d'akin Hadiza tace "kizo kiyi wanka ki canza wad'an nan kayan, sannan wannan kanma ki wankeshi kizo nayi miki kitso na gaya miki hajiya fa bata son k'azanta," Hibbah tace "to" a zuciyarta kuwa cewa tayi baba Hadiza bakisan *RAYUWA*r danayi bane shiyasa kike ganin k'azantata, towel Hadiza ta d'auko mata sabo tace "ga wannan dashi zaki rika wanka" Hibbah ta amsa tare daa godiya. Kayanta ta shiga cirewa ta d'aura towel d'in da Hadiza ta bata ta shiga band'akin, tsayawa tayi kallon band'akin ya tsaru kamar ka kwanta, ta gama k'arewa toilet d'in kallo itadai bata ga ta inda ruwa zai fito ba sai wata 'yar tukunya data gani Fara da ruwa a kwance a wajen kuma wannan bata ga ta inda mutun zai tari ruwa ba. Hakan yasa kawai ta juya ta fita daga toilet d'in, ta nufi kitchen ta Kira Hadiza ta nuna mata yadda zata yi.
Hanyar kitchen d'in ta nufa cikibis sukayi da Faruq ta sunkuyar da kanta tare da matsa masa ya huce ji tayu shiru mutum bai huce ba hakan yasa ta d'ago kanta don ganin me ya tsayayi. Gani tayi ya sha'afa yana kallon ta, kallon idanun sa tayi sannan ta kalli jikinta gani tayi Ashe kirjinta ya k'urawa ido yana kallo. Sai a lokacin ta tuna ashefa towel ne a jikinta kuma shima tsayinsa bai huce iya gwaiwarta ba da sauri ta juya zata koma d'akinsu, shima Faruq cikin sauri ya janyo hannunta ta fad'a jikinsa wata gigitacciyar k'ara ta saki wanda hakan yayi sanadiyyar fitowar Hadiza da sauri daga kitchen tayo dakin nasu inda anan ne taji k'arar. Aunty Aysha ma da take parlor a zaune tajiyo k'arar itama cikin sauri tayo wajen.
Tsayawa Aunty Aysha da Hadiza kukayi suna mamakin yadda Faruq ya rukunkume Hibbah suna kokawa, yana kokarin zare towel d'in dake jikinta. Kasa jurewa Aunty Aysha tayi ta buga masa wata muguwar tsawa, da sauri Faruq ya cika Hibbah, Hibbah wadda hawaye kebin fuskarta da sauri tayi d'akinsu. Aunty Aysha ta karasa kusa dashi ta yarfa masa Mari tace "Faruq baka da hankali ne daga kawo yarinya zaka nuna mata halinka, da kake kiciniyar k'wace mata towel din jikinta fyade kakeson yi mata kome? Tambayarka nake ka bani amsa." Hadiza data ke gefe tace "kiyi hakuri Aysha ki daina d'aga murya kar hajiya taji," "ai gara taji baba hadiza " tana gama fad'in haka tabi bayan Hibbah.

Aunty Aysha na shiga taga hango Hibbah acan k'arshen katifar dake d'akin ta kifa Kai da gwaiwa tana ta rera kuka, k'arasawa kusa da ita Aunty Aysha tayi ta zauna a kusa da inda take tare da d'ago kanta tace "kiyi hakuri Hibbah don Allah," Hibbah cikin kuka tace "Aunty Aysha ki daina bani hakuri don allah ni nasani ahaka zan k'are *RAYUWA*ta, ko wanne namiji burinshi kawai yaga ya yaga min rigar mutunci....." Ta kuma sakin kuka Aunty Aysha tana lallashinta tare da bata hakuri.
Hadiza ce itama ta shigo ta zauna a gefen katifar tace "haba Hibbah mai yasa zaki fita da wannan d'an towel d'in a jikin ki?" D'ago kanta Hibbah tayi tace "wallahi baba Hadiza banyi hakan da niyya ba ni shaf nama manta da abinda ke jikina nafito na tambayeki yarda ake kunna famfo d'in band'akin bansan yarda ake kunnawa ba." Hadiza ta kalleta yarinyar ta bata tausayi tace "kiyi hakuri Hibbah wannan ma tsautsayi ne kinji?" Aunty Aysha tace "ba wani tsautsayi baba hadiza, tun yaushe yake wannan halin? Ni wallahi nayi tunanin Faruq yabar wannan halin tuntuni ashe be daina ba. Kiyi hakuri Hibbah yanxu zanje na fad'awa momy komi don yaga yanxu daddy baya zama shiyasa kenan ya cigaba da halinsa." Murmushin takaici Hibbah ta k'ak'alo tace "babu komi fa baba Hadiza Ku daina bani hakuri, aini haka tawa k'addarae take kuma na karbeta hannu bibbiyu, kuma don allah aunty Aysha karki fad'awa kowa" ta mik'e tare da cewa "Dan baba Hadiza kunna min famfon bansan ya ake kunnawa ba." Hadiza ta mike tare da cewa "to", tare suka shiga ta nuna mata yarda zata kunna sannan ta fito, koda ta fito ma ba zama tayi a d'akin ba ta fita tabar Aunty Aysha ita kad'ai a d'akin tana tunanin furucin Hibbah.
Tana nan zaune Hibbah ta fito daga wanka ta wanke kanta, gashin duk ya barbaxu a fuskarta ruwa sai d'uga yakeyi. Kallon Aunty Aysha tayi tace "au Aunty Aysha kina nan har yanzu?" Murmushi Aunty Aysha tayi tace "ina nan Hibbah akwai abinda nake so na tambaye ki ne," Hibbah ta kalleta da d'an mamaki a fuskarta tace "wace irin tambaya zakiyi min Aunty Aysha?" "So nake don allah ki bani tarihinki, kuma don allah karki boyemin komi," shiru Hibbah tayi ta ta tsaya da shafa man datake yi. Aunty Aysha tace "kiyi hakuri Hibbah kiyi wani furucine Dana kasa fassara shi shiyasa nake bukatar jin labarinki," hawayene ya fara kwaranya a fuskarta tace "haba aunty Aysha wai me yasa kike bani hakuri? A k'asanki fa nake zan baki tarihina yanxu." Nan ta shiga karanta mata labarinta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.