Complete Hausa Novels

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 41 of 51

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page4⃣7⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

Ba kowa bace illa Auntynku Aysha, itace wadda amminku ta rasu ta barta, ni kuma na d'auketa momynku ita ta shayar da ita kuma babu Wanda zaice ba Zainab bace ta haifi Aysha, gashi ta d'auko kamannin Zainab tunda Aysha da Zainab uwa daya uba daya ne" duka 'yan d'akin sun firgita da jin wai Aunty Aysha ba 'yarsa bace, Aunty ta janyo Hibbah ta rumgume ta suka saki kuka duka su biyun mai ban tausayi sun jima a haka babu Wanda yayi yunk'urin rabasu kowa tausayinsu yake ji a zuciyarsa musamman ma Hibbah da ta taso cikin wahala da uk'ubar *RAYUWA*.
Hibbah ta d'ago daga jikin Aunty suna kallon juna "Aunty dama ashe ke 'yar uwata ce shiyasa kike tausaya min kika inganta rayuwa ta ki jiyar dani dad'in rayuwa aunty bani da kamar ki na gode Allah ya saka miki da.........." Aunty tayi saurin toshe mata baki "ko a da Hibbah babu godiya a tsakanin mu balle yanzu da muke *jini d'aya* ni dake, Allah za muyiwa godiya da har ya nufe mu da sanin gaskiya" Hibbah tayi murmushi tare da yiwa Allah godiya, ta dubi su momy sai murmushi suke yi ita da mamy.
Mamy tace "zonan Hibbah inji d'umin jikin d'an uwana" a hankali Hibbah ta k'ara kusa da mamy, mamy ta rumgume ta tana jin k'aunarta na ratsa jikinta, ta b'anb'areta daga jikinta tana kallonta "Hibbah yanzu ina d'an uwana yake? A ina yanzu yake *RAYUWA*?" Hibbah hawayen farin ciki nabin fuskarta "mamy yana wani k'auye a cikin k'auyukan Bunkure" mamy ta kalli su Abba da suke ta bin Hibbah da kallo cike da k'auna tace "Yaya yaushe zamuje mu gansa?" Daddy fuskarsa cike da farin ciki "ai yau za'a sallami Faheem tunda k'auyen ba nisa ne dashi ba sai muje yau Donni na k'osa naga d'an uwana" Saudat ta mik'e da sauri "bara naje na kira Dr yazo ya sallami Yaya mu tafi" Aunty tasa dariya "kai Saudat kin fiye zumud'i ki Bari yanzu ma zaki Ganshi ya shigo" "ai Aunty na k'osa ne muje wallahi"
Faheem yayi murmushi yana yiwa Hibbah wani kallon "Ashe dai ke k'anwata ce shiyasa na rud'e a kanki na kasa sukuni saboda bana son wani ya b'ata miki *RAYUWA*" "ba wani nan dama can kai kana sonta kana tsoran kar ayi maka k'wace ka rasata yasa har ka kwanta a asibiti wai ciwon zuciya" Abba ya fad'a cikin sigar tsokana duka suka sa dariya banda Kausar da Safiyya da sunma kasa had'a idanu da Hibbah saboda tsantsar kunyarta da suke ji.
Safiyya tafi Kausar kusanci da Hibbah don haka ta matso kusa da ita ta rik'e hannayenta "don Allah Hibbah kiyi hakuri ki gafarce ni wulakancin da nayi miki" Hibbah tayi murmushi "habba Safiyya wallahi ni baki yi min komai ba" Safiyya ta rumgume ta tana share hawaye cike da Dana sani tace "na gode sis Hibbah" Hibbah ma ta rumgume ta tana yiwa Allah godiya a zuciyarta ashe itama tana da gata haka, Saudat dake gefe cikin tsokana tace "lallai Safiyya wato yau Hibbah har ta samu matsayin sister" ta fad'a tana dariya Safiyya ta harareta "to ina ruwanki gulgul."
Kausar ma ta matso kusa da ita ta zauna a gefenta "Hibbah na sani na wulakantaki nayi miki rashin mutunci iri iri na d'aukeki kamar wata baiwa a gidana, yanzu gani a gabanki ba don ni ba don Allah kiyi hakuri ki yafe min" Hibbah ta shiga girgiza Kai "Aunty Kausar ni ya dace na baki hakuri ba ke ba, don kuwa a matsayina na 'yar aikin gidanki na aure miki miji kiyi hakuri Aunty wallahi babu laifina a ciki ban ma san da auren ba" Kausar tayi murmushi "haka Allah ya k'addara Hibbah hakan shine sanadiyyar kawo zaman lafiya a gidan Allah ya bamu zaman lafiya" Hibbah tayi k'asa da kai cike da kunya, don tunda akace ita matar Faheem ce take tsananin jin kunyar Kausar da kuma Faheem d'in.
Momy tace "alhamdulillah naji dad'in wannan al'amari Allah ya had'a kanku" suka ce amin.
Dr ya shigo don duba lafiyar Faheem ya tadda Faheem a zaune yana ta murmushi kamar ba shine Mara lafiya ba, dr cikin mamaki yace "a'a Faheem yana ganka haka garau dake kamar ba Kaine Mara lafiyar ba?" Aunty tayi caraf "dr ba dole ka ganshi haka ba tunda ya samu abinda yake so ai dole ya watstsake" Faheem ya harareta "Dr ba wani nan Allah ne ya kawo sauk'i" "to Allah ya k'ara sauk'i" "amin suka amsa. Dr ya mik'a masa takardar sallama da kuma ta wasu magunguna da zai cigaba da amfani dasu, ya amsa sukayi masa godiya ya fita, Daddy yace "kuyi sauri Ku had'a kayan mu tafi, ni so nake kawai naga Mukhtar"
Hibbah ta dubi Daddy idanunta taf da hawaye zuciyarta cike take da tsoro tana tuna furucin Inna *_kuma wallahi sauran idan an kaiki kice zaki zo ganin gida wallahi saina kashe ki, kinsan halina zan aikata,_* ta kuma tuno lokacin da gwaggo tace *_yanzu lami baki tsoran yarinyar nan ta fad'a mugun hannu ko kuma su gidan da aka kaita su koreta, ina zata wata sani scan da zskice karta waiwayi mahaifarta? Inna tace oho ni ko Karuwanci zatayi tayi ina ruwana._*
Hawayen fuskarta ya tsananta zuba gaskiya bazata iya zuwa k'auyen nan ba don tasan halin Inna lami tsaf zata iya kasheta, ji tayi an dafa kafad'arta da sauri ta waiwaya Kausar ce tace "Hibbah me kike tunani muna ta magana?" Ta share hawayenta ta girgiza kai "ba komai Aunty" Nawaz ya kwanto a jikinta "Aunty me yasa ki kuka?" Aunty tace "haba Hibbah ya kina kuka kuma kice babu komai don Allah ki fad'a mana me ya saki kuka me kike tunani?"

Hibbah ta k'ara goge hawayen dake zuba a idanunta,"Aunty kuyi hakuri wallahi ina tsoran komawa k'auye ina tsoron Inna lami nasan halinta zata iya kashe ni, tunda tayi min gargad'in karna kuma waiwayar garin" Hibbah ta fad'a hawaye na bin fuskarta. Faheem yana daga can gefe "karki damu Hibbah babu abinda ta isa ta yi miki Wanda Allah bai nufa zai same ki ba ki tuna baya taso ta lalata miki *RAYUWA* ta tozar taki amma da yake Allah ba azzalumin sarki bane sai ya hana faruwar hakan sannan ta turoki birni don ki zama k'ask'antacciya shima hakan sai ya zame miki alkhari don haka ki cire wannan tunanin daga ranki, mu duka nan muna tare dake Allah na tare dake babu abinda ta zai sameki da yardar Allah" Hibbah ta gyad'a kanta cike da gamsuwa ta kuma ji dad'in kalaman Faheem, "Kai Aunty Hibbah kin fiye tsoro da yawa" Saudat ta fad'a tana dariya, Hibbah tayi mata hararar wasa Safiyya tace "ai tsoro halal ne kuma kema kina yi Aunty Hibbah nima ina bayanki ki cigaba da jin tsoro wallahi mutumin da yace zai kasheka kuma kasan halinsa zai aikata ai dole kaji tsoransa"
Abba yace "haka ne amma Hibbah ina son nasan wani abu game dake, don ni har yanzu zuciya ta tana raya min wani abu game dake kuma inajin wani abu a tattare dake" dukkan ninsu suka maida hankalinsu kan Abba, ya cigaba "Hibbah tun d'azu dana ji muryarki nake jin zuciyata na harbawa danaga fuskarki kuma k'irjina ya tsananta bugawa idan kika yi magana kina tunamin wani mummunan abu daya faru a baya, kina tuna min k'anwata Aysha da nake matuk'arso" Hibbah ta kasa fahimtar inda kalamansa suka dosa "Abba ni wallahi ban fahimce abinda kake fad'a ba" Abba yayi d'an shiru yana tunani, su Daddy dasu momy kuwa duk so suke suji abinda ya faru da Abba mene shi kuma had'insa da Hibbah?
Abba cikin murya mai nuna tausayawa yace "Hibbah Aysha da kike kama da ita k'anwata ce iyayenmu d'aya mu biyu ne a wajen iyayenmu, mahaifimu d'an kasuwane tare suke kasuwanci da mahaifin Daddy'n ku.
Ranar juma'a da rana bayan sallar juma'a su Alhaji da hajiyarmu zasu yi tafiya zuwa k'auyukan dake zagaye da garin kano, Alhaji ya saba duk juma'a yakan je k'auyuka ya kai musu tallafi, sun saba da Aysha suke tafiya ni kuma a barni a gidansu Daddy lokacin Aysha tana da shekara biyar a duniya.
A hanyar su ta dawowa ne daga k'auyen suka had'u da 'yan fashi........... Inna lillahi wa inna ilai hirra ji'un" Abba ya fad'a hawaye yana bin fuskar sa yasa tissue ya goge hawayen sanna ya cigaba "suka buk'aci kud'i daga wajen su Alhaji lokacin Alhaji babu kud'i a wajensa don haka ya fad'a musu cewa babu kud'i a wajensa, babu ko imani suka harbeshi a k'irjinsa suka hajiya ma tare da driver'nsu amma basu harbi Aysha ba ogansu yace su k'yaleta. Haka suka barsu a k'asa a kan titi suka tafi da motar, Aysha ta zauna a wajen tana ta kuka daga baya kuma ta tashi ta shiga cikin garin don shaida musu abinda yake faruwa tun daga nan ba'a kuma ganinta ba. Bayan an kawo gawawakinsu na irin Neman da ba'a yiwa Aysha ba amma ba'a ganta ba.
Naji mutuwar iyayena nayi kukan rashin Aysha, daga lokacin ne Alhajin su daddy ya d'auke ni ya cigaba da rik'eni." Abba ya kuma share hawayensa yana kallon Hibbah yace "shiyasa zuciyata take raya min ko Aysha tana raye ke 'yarta ce" Hibbah da itama hawayen take yi na tausayawa Abba tace "Abba saidai muje wajen Umma a tambaye ta amma ni nasan a k'auyen mu Ummana ta taso don iyayenta ma suna raye har na baro k'auyen" Daddy shima cike da tausayi yace "babu matsala sai muje muji ta bakinta, ku tashi mu tafi"
Nan suka shiga had'a kayayyakin suka zuba a mota suka huce gidan daddy...............

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.