Complete Hausa Novels

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 29 of 51

Ranar ya nace mata yak'i tafiya ko zama zaiyi saiya dawo kusa da ita sai ya waske yana yiwa Nawaz wasa, shareshi take yi don bata son Faheem ya fahimci suna wani d'asawa ne da Faruq.
Ya shigo fuskarsa a had'e kamar bai gansu ba, gani tayi Faruq ya daina rawar kai, "Faruq Ku had'a kayan nan mu tafi gida sun bamu sallama," Faruq ya kalleta "mene kike wani d'ari d'ari nifa bana jin kunya a gaban Ya Faheem sai na miki kiss kinga daya ga haka sai yasan yadda zai nema min aurenki, su bani abuna ko kuma na ja musu maga na b'allo ruwa." Ta marairaice "ka tabbatar min ka tsaneni shiyasa kake bin duk wanda nake da k'ima a wajensa kake zubar min da mutunci, Allah sai ya saka min," maganar ta shige shi ya janyo Nawaz ita kuma ta had'a kayan suka fito.
A nota suka iske shi yana danna ways Sam ya rasa mai yake masa dad'i ransa a b'ace yake, Faruq ya bud'e motar yana sa kayan, Nawaz ya shige gaban motar.

Ya kalleta "muje ga mota ta mu tafi tare" ta dalla mishi wata harara ta tsuke baki, ya Sosa sumarshi yana dariya ciki ciki, ta rasa wanda zata bi don tana matuk'ar jin nauyin Faheem d'azu ma da k'yar take numfashi a cikin motarshi, amma da ta hau motar Faruq gara ta hau gara ta tafi a k'asa, gani tayi Faheem yayi tafiyarsa.
Faruq yaji wani dad'i a ransa shi yasa Faheem yake burgesa akwai jan girma yasan abu ya gani amma sai ya basar kawai don shi baison shiga sabgar yara.
Ta k'urawa danjojin motar idanu har suka b'ace a duhun daren, hannunshi taji cikin nata "my dear," a fusace ta k'wace hannunta ta soma tafiya ko waiwaye bata yi har ta d'anyi nisa don zuwa bakin titi daga asibitin da d'an nisa. Faruq ya shiga motarsa yana biye da ita "Hibbah mene haka wai kinsan halina idan kika b'ata min rai," ko kallon shi bata yi ba, kwatsam sai ga wash d'irka d'irkan karnuka sun sharp a guje suna haushi, turus tayi ta ci wani mugun burki zuciyarta tana harbawa ta k'ame babu abinda tafi tsoro kamar kare, sai kace zakuna haka suka tunkarota ta kasa gaba ta kasa baya, gashi sun nufota gadan gadan ai batasan sanda ta bud'e motar ta rufe ba, ta tusa kanta tana ambaton Allah. Faruq ya kwashe da muguwar dariya mai ban haushi yana kad'a kai don wak'ar Machel Jackson yake saurara yana ya fara tuk'insa cikin nishad'i, ya d'ago kanta "my baby kin fiya tsoro, idan munyi aure da kin b'ata min rai police dog zan d'auko su yayyaga ki" tayi banza dashi "Hibbah" ya Kira sunan a hankali, ta kalle shi "gaskiya kin fa tashe ni daga aiki wai sai kimin shiru kin mai dani mahaukaci wato nayi ta sambatun sonki ni kad'ai, ki tausayamin wallahi da gaske nake aurenki zanyi" ta mishi kallon nutsuwa sai yanzu taji zuciyarta ta gamsu da gaske yake amma kuma yafi buk'atar jikinta akan komai, Allah mai yadda yaso gata dai a hannun Faruq duk abinda yaga dama yayi da ita.
See Sweet suka iso yayi parking ya fita yaje ya siyo ice cream da fresh milk yana tahowa ta k'ura masa ido handsome bakinta ya furta, ya k'araso cikin motar.
Ya mik'a mata ledar, ta kalle shi "gaskiya ba zan karb'a ba na gode in don nice da bakayi asarar kid'inka ba," ya had'a rai ya jefa mata jikinta "sai ki jefar tunda baki so," ya tashi motar bai sake magana ba har suka gida, ta fito ta bar masa kayansa a mota.
Ya d'auko ya bita da shi, Faheem yana ta lallab'a Nawaz yayi barci ya dameshi bashi kansa ciwo yake masa. Hibbah tayi sallama yana jinta ya tashi, Faruq ya shigo ya zauna yana kallon news, yana tambayar Faheem kanun labaran Nawaz ya haye jikinsa yana tambayarsa me ya kawo musu a leda, ya mik'a masa wai ya kaiwa Hibbah.
Hibbah kuwa kitchen ta nufa tana zuwa ta hango Kausar tana aiki a ciki "aunty sannu da aiki," tayi mata wani kallo dama tana jin haushinta a dalilin tafiyarta yaronta ya samu matsala har ta kaisu ga yin 'yar hatsaniya da Faheem don har yanzu basu shirya ba, "Kama aikinki donni bazan iya ba dama na gaji" tayi ficewar ta.
Taji babu dad'i abinda Kausar take yi mata yayi yawa ka d'auki d'an Adam kamar dabba a wulak'ance, ta duba abincin ashe ma indomie ce take dafawa sai kuma dankali da ta soma ferayewa, ragowar mata shikenan abincin da ta iya. A bayanta ta ji shi ta juyo suna kallon juna, surarta ta ja hankalinsa duk da ba yau ya fara ganinta ba, ta juya amma ta kasa ci gaba da aikin don ita bata son kallo da takura.
Nawaz ya shigo "aunty yunwa nake ji" ta zobo masa indomie dayake tayi ta bashi, Faruq ya kuma matsowa "Hibbah yaya zan kwatanta soyayyarku da Nawaz ne, gashi shi kad'ai ne a wajen ya Faheem daya bamu shi nasan bazai bamu ba don shi yana son yara, amma wannan Matar tashi ta fini yahudanci wai bata son haihuwa" ita dai feraye dankalin take bata ce masa komai ba "kin San abinda na tsana kenan kiyi min shiru ina magana ko?" Tayi shiru, kawai yatsunsa taji a gefen cikinta yana mata cakulkuli, wata zabura tayi ta zille gefe tasa kuka "Wallahi zanje na fad'awa Daddy'n Nawaz wannan wulakanci da kake min ya ishe ni," "ni d'in mahaukaci ne zaki k'yale ni ina magana ni kad'ai?"
Kausar ta shigo tana wani muzurai "ke dalla ki bawa mutane abinci muna jin yunwa" taja tsaki, Faruq yayi mata wani kallo ya had'a rai, sim sim ta fita tana mita don tana shakkar Faruq. Yayi tsaki "stupid kawai 'yar rainin hankali ce matar nan, sai Yaya ya dinga min wa'azi ga rubbish nan a gidansa ya kasa sarrafata, dama ina ciki da ita" "to kai ina ruwanka da shiga tsakanin miji da matar sa haka yake son matarsa don gani yayi zai iya zama da ita" ya harareta "Allah ko uwar iyayi kin fini sanin hakan ko?" Tayi d'an murmushi "kaima ai ba kanwar lasa bace"
"Wai ni na rasa girman lefina da ake gani har kuna hangen nauyin zunubi na bazai kankaru ba, ba'a shiga tsakanin Bawa da ubangijinsa ni bana aikata manyan aiyuka bana shan giya bana sata, kisa bare fashi da makami, to menene a ciki kawai don mutum yayi rayuwar da yake ra'ayi tajin dad'i sai ace ya sab'i Allah? Ina sallah, azumi da bin iyayena to menene saura kuma?" "Haka ne to amma ina batun b'angaren Mata naji ka keb'ance shi ko shi baya cikin manyan lefuka? Ba wani inkari da zakayi don kai Gwani ne ta wannan fannin" ya sosa k'eta "kin gane Allah gafurur rahim ne, wannan va wani abu bane kawai lokaci ne daga na aure ki zan daina, don nasan zaki gamsar dani bani da lokacin bin wasu matan" ta dubeshi "hali zanen dutse, a duniya babu abinda nake k'yamata kamar miji mai neman mata, kai kuwa ya zame maka jiki duniya ma ta shaida haka, to saboda me ni kuma zankai kaina ga halaka?"
Wani abu ta gani a idanunsa da alama maganarta ta tab'ashi sosai, bai ce komai ba ya fita, tayi d'an murmushi ta k'arasa aikinta. Yana parlor bai tafi ba ta ajiye musu abinci ta koma d'akinta ta gyara don da bata nan yayi k'ura, saboda tunda ta tafi Nawaz ya koma wajen daddy'nsa da kwana. Tayi sallah a gajiye take ta kwanta cikin tunani daban daban, tun daga sanda Faheem yaje gidan Umma, tana jiyo kalaman Umma ko ya ta d'auki Faheem? Lallai yana da k'ima da girma a gunta bata tab'a yi mata maganganu masu zafi haka ba................

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.