Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 20 of 51
A mota Nawaz sai surutu yake tayi shi kad'ai, yace "daddy aunty Hibbah gidan mu zamu da ita?" Faheem dayake tuk'i yace "eh Nawaz ita zata dinga zama tare da kai idan ka dawo daga school, tayi maka wanka ta koya maka homework ta dafa mana abinci," Nawaz jin ya ambaci homework yasaki ihun murna "yeeeh daddy nima na samu aunty," ya juyo yana kallon Hibbah yace "aunty Hibbah har unguwa zaki dinga zuwa dani momy na bata zuwa unguwa dani wai nayi girma, ai banyi girma ba ko aunty?" Hibbah ta d'aga masa kai tana murmushi tace "eh Nawaz zan dinga zuwa dakai," lokaci d'aya taji k'aunar yaron ta shiga ranta, shi kuwa Nawaz cigaba yayi da wasanshi har suka k'araso gidan Mai gadi ya bud'e gate d'in gidan yana yiwa Faheem sannu dazuwa.
A parking lot ya ajiye motar suka fito, Faheem yayi gaba shi kuma Nawaz ya zo ya rik'e hannun Hibbah suka parlor yana ta yi mata surutu. Suna shiga suka tararda Faheem a parlor yana k'ok'arin kunna TV, bai kallesu ba ya kunna TV ya dawo ya zauna yana kallon labarai, a k'asa Hibbah ta zauna Nawaz yana kan cinyarta, Faheem yad'an kalleta kad'an ya kawar da kansa yace "Hibbah sunanki ko?" Hibbah ta d'aga kai "eh" yace "Hibbah aikin ki a gidan nan shine girki, gyaran gida sai kular min da Nawaz pls ki rik'e amana," Hibbah tace "insha allah daddy," Faheem ya cigaba da kallo yace "sannan maganar zuwa school d'inki idan kika gama aikin da wuri sai kije yanzu dai samo min wani abu naci," Hibbah ta mik'e ya kalli Nawaz yace "son nuna mata d'akin da zata zauna da kitchen," Nawaz ya mik'e ya rik'e hannun Hibbah ya kaita har d'akin dayake yasan suna extra daki ta ajiye mayafinta, sannan ya kaita kitchen. Gaskiya ta raina tsaftar matar gidan kitchen duk yayi datti kaya duk a barbaje komai a wulakance yayi kaca kaca, nan ta shiga gyara kitchen d'in ta d'auke kayan ta wanke ta share tayi mopping kitchen din yayi fes, sannan ta d'ora girkin..........
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page2⃣8⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.W.A
*DEDICATED TO AYAHA ALIYU GARKUWA*
*Ina taya duk musulman duniya murnar shiga sabuwar shekarar Muslunci, allah ya bamu alkharan wannan shekara ameen.*
*Ina kuke DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION FANS wannan page d'in nakune muna godiya da k'aunarku.*
Nan da nan gida ya d'auki k'amshin girki, ta had'a lemon kwakwa, bayan ta gama ta juyo shi a kula ta kai dinning ta ajiye ta koma d'auko lemon ta tawo da plates da spoons sai kuma cups tazo ta ajiye akan dinning d'in, ta zubawa Faheem daban ta zubawa Nawaz shima nashi ta rufe ko wanne da wani plate d'in. Ta dawo parlor ta tsugunna a gaban Faheem tace "daddy na gama ga abincin can a dinning," ba tare daya kalleta ba yace "ke kin d'ibi abincin?" Ta girgiza kai alamar a'a yace "kije kici" "to" ta fad'a tana komawa wajen dinning din, ta d'ebo a plate d'in tazo zata huce Faheem yace "ina zaki?" Tace "daddy a d'aki zanci," ya d'aga kai tare da mik'ewa Nawaz na biye dashi suka k'arasa dinning.
Yana bud'ewa wani daddad'an k'amshi ya daki hancinsa ya lumshe ido tare da kai lomar farko bakinshi, kuma lumshe ido yayi gaskiya yaji dad'in abincin rabon dayaci irin wannan abincin tun yana gidan momy, ya kuma kai wata lomar bakinsa tare da kurbar lemon, Subhanallah ji yayi ya kuma rikicewa gaskiya yarinyar nan ta iya girgiki abinda yake fad'a kenan a ranshi.
Nawaz sai da ya gama wasansa sannan ya fara cin abincin yana ci yace "daddy abincin aunty Hibbah ba irin wanda kake siyo mana ba," Faheem yayi murmushi yana shafa kan Nawaz yace "haka ne Nawaz abincin Hibbah yayi dad'i, amma kaci abincinka banda surutu kar ka kware kaji," yace "to daddy amma kullum ita zata dinga yi mana abinci ko?" Faheem ya d'aga masa kai, ya cigaba da cin abincin har suka gama, suna gamawa Nawaz ya ruga d'akin Hibbah lokacin itama ta gama ci, ya shigo yana cewa "Aunty Hibbah abinci da dad'i daddy ma yace da dad'i," Hibbah tayu murmushi taji dad'in furucin Nawaz tace "Nawaz idan aka shigo d'aki sallama ake fara yi kafin ayi wata magana," Nawaz ya d'an karyar dakai "to kiyi hakuri aunty abincin ne yayi dad'i," Hibbah tayi murmushi tace "to naji amma tashi kaje kayo sallama tukunna," Nawaz ya mik'e ya fita yaje yayo sallama, ta amsa masa sannan ya shigo ya zauna akan k'afae Hibbah yace "aunty Dan Allah ki cigaba da yi mana irin wannan abincin yayi dad'i," Hibbah ta kalleshi tace "da gaske daddy yace girkina da daddy Nawaz?" Nawaz ya d'aga Kai "eh aunty yace da dad'i," tace "Nawaz ai dole na cigaba da yi muku irin wannan abincin," Nawaz yayi ihun murna "yeeeh zamu dinga cin abinci me dad'i," Hibbah ta d'anyi dariya tana kallon yarda yake murna tace "daddy ya fita ko yana parlor?" Nawaz ya mik'e "bara na duba," ya fita jimawa kad'an ya dawo "aunty baya nan ya fita," Hibbah tace "yauwa Nawaz," ta mik'e zata fita Nawaz yace "aunty ina zaki?"
"Zan wanke kayan aka b'ata ne Nawaz" "Aunty idan kin gama zaki yimin assignment d'ina ran Monday zamu koma school," ta d'aga kai tare da fita.
Ta had'o kayan ta wanke ta gyara ko ina parlor ma tasa turaren wuta sai k'amshi ke tashi ta koma d'akin nata taga Nawaz ta tattaro littattafansa na makaranta ya barbazasu, tana zuwa ta shiga nunnuna masa yaron akwai k'ok'ari nan da nan yake fahimta, bayan sun gama Nawaz ya dinga yi mata shirme tana biye masa, yaje ya d'auko mata wani hotonsa ya ajiye mata a gefen gadonta wai yabata haka dai yayi tashirmensa har yamma.
Bayan tayi sallar la'asar ta shiga kitchen tayi musu dinner, ta koma d'akin tayi wanka ta canza kaya tana nan zaune akayi kiran sallar maghrib ta tashi tayi sallah. Shi kuwa Nawaz yana gani ta shiga kitchen ya fita wajen iliya mai gadi yana ball.
Sai bayan sallar maghrib suka shigo da daddyn shi, suka nufi dinning suna cin abincin Kausar ta shigo da sallama ta ajiye Jakarta akan kujera itama ta zube a kan kujerar tace "wash Allah, daddyn Nawaz yau har ka yo take away d'in kenan," Faheem bai kulata ba saida suka k'araso inda take da yake sun gama cin abincin ya zauna a d'aya daga cikin kujerun parlor'n yace "a'a aini yanxu na wuce wannan wajen, Aysha ce ta bani shawarar kawo mai kula min da gida ta kular min da yaro tunda ke kin zab'i aikinki akan mijinki da iyalanki," maganar ta yiwa Kausar zafi "haba daddy'n Nawaz kaima fa kasan yanayin aikina, kayi min uzuri mana," "wane uzuri zanyi miki Kausar? Bayan hakurin zaman da nake yi dake yanxu," maganganunsa sun fara yi mata zafi ta kalli Nawaz a tsawace tace "Nawaz kira yarinyar da tazo Kace ta kawo min abinci," Nawaz ya kalleta a d'an ta yace "to momy bara na k'arasa kallon wannan film d'in," "dallah ka tashi kaje ka kira min ita," Kausar ta fad'a tsawace da gudu Nawaz ya fita duk ya tsorata.
Faheem ko kallon ta baiyi ba sai wani cika take tana batsewa, Nawaz ya dawo Hibbah na biye dashi suka shigo parlor'n da sallama Faheem ne kawai ya amsa ita kuwa ko kallonta bata yi ba tace "ke zubo min abinci," Hibbah tace to" ta nufi dinning ta zubo mata abincin ta kawo gabanta ta ajiye, tana shirin tafiya Kausar tace "keehh" Hibbah ta juyo ta kalli Kausar tace "na'am aunty," cikin mamaki Kausar ta mik'e "ke meya kawoki gidana?" Ta kalli Faheem "badai wannan ka kawo min a matsayin 'yar aiki ba," yayi mata kallon gefen ido "a ina kika ganta? Ina ce a cikin gidan nan kika ganta kuma na miki bayanin ai ko?" Tace "haba Faheem ya ina tambayar ka kana yi min magana a duk'unk'une," bai kulata ba ya kalli Hibbah yace "tashi kiyi tafiyar ki," "ke dawo karki sake ki koma min cikin gida mayya kawai," cikin masifa Kausar take mata magana, cikin tsawa Faheem ya d'aga mata hannu "ya isheki Kausar baki isa ki hana Hibbah zama a gidana ba, ni na kawota cikin gidannan kuma ko kinaso ko bakyaso dole ne ta zauna," ya kalli Hibbah yace "ki tafiyarki ciki babu Wanda ya isa ya hana ki zaman gidan nan," Hibbah ta nufi cikin d'akinta.
Kausar kuwa takaici ne ya isheta tasan halin Faheem sarai yanxu zai dizgata a gaban yarinyar nan, ta suri jakarta tana ta mita ta shiga ciki.
Faheem ko kallonta baiyi ba ya cigaba da kallon news, Nawaz ya kalli daddyn shi yace "daddy ni yau a wajen aunty zan kwana," Faheem ya kalleshi "a'a Nawaz zakaje ka takurawa Hibbah ne da surutu ne kawai," "daddy bazan yi mata surutu ba," "to shikenan kaje ka canza kayan naka sai kaje Ku kwanta," Nawaz ya tashi yana murna yaje ya canza kayanshi ya tafi d'akin Hibbah, ya shiga da sallama waya yaga tanayi tace "aunty kiyi hakuri zanzo amma ba yanzu ba, saina daina xuwa islamiyya tukunna," daga can aunty tace "yaushe ne zakuyi walimar ne Hibbah?" "Next week Sunday," Hibbah ta hawa aunty amsa, "to Allah ya kaimu," "ameen Aunty," Nawaz ya matso kusa da ita "aunty bani mu gaisa da momy Aysha,," Hibbah ta mik'a masa wayar suka gaisa da aunty sannan sukayi sallama ta kashe wayar.
Ta kalli Nawaz tace "Nawaz daddy ne yake Kira na?" Ya girgiza kai "a'a aunty nazo mu kwana tare ne," "ok to zo muyi alwala sai mu kwanta," suka mik'e suka d'auro alwala suka yi addu'a tare da kwanciya.
Da safe Hibbah ta tashi tayi duk wani aikin gidan sannan tayi wanka tayiwa Nawaz ta shiryashi sukayi breakfast ta wanke cups d'in, da rana ma haka tayi musu girki hakama da dare.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.