Complete Hausa Novels

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 40 of 51

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page4⃣6⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

Aunty ce tayi saurin tarota ta fad'o jikinta, Faheem besan sanda ya diro daga gadon ba yayi wajenta da sauri yana ambaton sunanta su momy ma suka matso suna jijjigata, mamy ce ta d'auko ruwa ta fara shafa mata a fuskarta. Abba kuwa da hanzari ya fita ya kira Dr, suna shigo Hibbah tana farkawa Dr ya k'araso ya shiga dubata ko da wata matsala, ya gama dubata ya tabbatar musu da lafiyarta sannan ya fita.
Hibbah tayi shiru kawai kallon Daddy take yi tana son ta gano wani abu game da Daddy tana kuma tambayar kanta, me ya kawo babanta birni dama babanta yana da aure a birni amma bai tab'a gayawa su Inna ba kuma akace bai tab'a haihuwa ba sai akanta idan haka ne su Aunty Aysha kuma 'ya'yan waye? Bata da amsoshin wad'an nan tambayoyin nata ya zame mata dole ta tambayi daddy don shi kad'ai ne zai iya amsa mata wad'annan tambayoyin.
Daddy da Abba sun shiga tunani Daddy ya tafi wani tunanin akan Hibbah yana son yasan wani abu game da wannan razanar da tayi ta ganinshi don ta bashi tsoro, yayin da Abba kuma ya tafi tunani wacece wannan mai irin murya da kamannin k'anwarsa Aysha kodai 'yar Aysha ce? Ya tambayi kansa sai kuma ya girgiza kai a'a, a iya saninsu Aysha tun tana k'arama ta b'ata kuma baya tunanin yanzu tana raye, lallai ya zame masa dole yasan ko wacece ita. To amma me ta sani game da Daddy da har zata suma don tagansa mene a tsakaninsu? Dukkansu su biyun basu da amsoshin tambayar su don haka Daddy ya d'ago Kai ya dubi Hibbah dake kwance itama duk tunani ya dameta.
"Hibbah ki fad'a min mene dalilin da yasa don kin ganni kika tsora har kika suma?" Hibbah tayi shiru tana nazari kenan baba bai ganeta ba kodai ba babanta bane kama ce? Ta dubi su momy duk jira jira sukeyi tayi magana, cikin yanayin tsoron da bai saketa ba tace "Baba, baba baka gane ni ba Hibbah ce fa, Hibbah 'yarka daka kora" sai kuma hawaye ya fara bin fuskarta.
Daddy cikin yanayin nuna damuwa yace "Hibbah kiyi hakuri bani bane Wanda kike fad'a" Hibbah ta rik'e kanta don ya fara mata nauyi wannan wace irin *RAYUWA* ce ka haifi 'yarka amma ka kasa gane ta? Me ta canza da baba zai kasa ganeta? Faheem dake kusa da ita ya dubeta cikin kulawa "Hibbah kiyi mana bayani yadda zamu fahimce ki, kinsamu a cikin hargitsi" Hibbah hawaye nabin fuskarta damuwarta ta k'aru "babu komai Daddy zan cigaba da rayuwata ba tare da babana ba dama tun tasowata nafi sabawa da ummana akan babana saboda baya sona bai damu da rayuwarmu ba........." Sai kuma ta saki wani irin kuka. Daddy ya kasa fahimtarta ya kasa gane maganganunta, balle kuma Abba da idan tayi magana yake jin gabansa yana bugawa.
Faheem kam wannan kukan da take yi jinsa yake har cikin ransa, Aunty ta janyo Hibbah jikinta tana rarrashinta. D'akin yayi tsit sai sanyin AC dake ratsa d'akin, Abba ne ya katse shirun da cewa "Hibbah dukkanmu nan bama gane abinda kike fad'a, amma ko zaki fad'a mana sunan mahaifin naki may be mu ganeshi," da kamar ba zatayi magana ba saboda kukan da yaci k'arfinta, dak'ar ta iya rage kukan cikin muryar kuka tace " *MALLAM MUKHTAR MUHAMMAD*" da hanzari Daddy ya nunata "kina nufin kice min Mukhtar yana raye!?"
Daddy ya fad'a cike da rud'ewa, kansa ne ya fara juya masa a hankali ya kama gefan gadon ya zauna yana jin k'aunar d'an uwansa tana kuma ratsa zuciyarsa. Abba ma gefen Aunty ya zauna yana kuma tuno rayuwarsu ta baya gefen zuciyarsa kuma cike yake da rud'ani don ya k'osa yaji wacece Hibbah so yake yaji asalinta don kamar da suke yi masa da Aysha k'anwarsa ta b'aci. su mamy da momy ma suna cike da rud'ani ashe Hibbah'yarsu ce basu sani ba.
Faheem, Aunty, Kausar dasu Hibbah sun kasa fahimtar komai game dat abinda yake faruwa, Faheem cikin damuwa ya dubi su Daddy "Daddy don Allah kuyi mana bayanin abinda yake faruwa mun kasa gane abinda kuke nufi" Daddy yayi shiru k'aunar d'an uwansa na kuma ratsa zuciyarsa ya dubi su Faheem "Faheem yau zan bayyana muku komai game da rayuwarmu." Kowa ya maida hankalinsa kan Daddy, ya cigaba da cewa
"Kamar yadda kuka taso a garin kano muma a cikinsa muka taso iyayenmu mu uku suka haifa sab'anin yadda kuka sani, nine babba sai mai bina Mukhtar sai kuma mamynku Rukayya, mun taso cikin so da k'aunar iyayen mu sun jajirce wajen ganin sun inganta rayuwarmu ta hanyar bamu ilimi na duka b'angarorin. Ni da Abbanku mun taso tare kamar tagwaye komai tare mukeyi, haka ma Mukhtar da abokinsa Ibrahim sam ba'a jin kan d'aya daga cikinmu, muna level 4 a jami'ar bayero university kano inda muke karantar business administration dukanmu, Allah yayiwa mahaifinmu rasuwa mutuwar data gigitamu dukkannin mu, munyi kukan rashinsa sanadiyyar mutuwarsa ya janyowa hajiya hawan jini.
Bayan rasuwar mahaifinmu duk wata d'awai niya ta gidan ni da Mukhtar ne muke yinta da yake dama mahaifinmu kafin ya rasu ya d'oramu akan kasuwancinsa da yakeyi a kwari sai muka cigaba da juya dukiyar.
Shekarar mahaifinmu d'aya da rasuwa muka kammala degree d'in mu, hajiya kuma ta matsa mana akan muyi aure dama duk muna da wad'anda muke so yayinda Abbanku kuma yake son Rukayya, ba'a d'au wani dogon lokaci ba akayi bikinmu.
Auran da mukayi sai Allah ya kuma hab'b'aka arzik'in mu, don haka hajiya tace mu raba gadon da Alhaji ya bar mana idan yaso kowa saiya tada jarinsa munyi na'am da abinda hajiya tace don haka aka raba gadon aka bawa kowa hakkinsa muka cigaba da juyawa.
Kafin shekara arzik'in mu ya kuma burink'asa amma duk cikinmu Mukhtar ya fimu iya business don a lokaci k'ank'ani yayi suna a cikin garin kano har ya fara fita k'asashe babu wanda baisan *Alhaji Mukhtar Muhammad shagari* ba kowa ka tambaya zai nuna maka.
Shekarar mu d'aya dayin aure Allah ya azurta matanmu nida Abban Ku da samun haihuwa kuma duk maza, sab'anin Mukhtar da matarsa Aysha Allah bai basu haihuwa ba. Ranar suna nasawa Faheem Muhammad sunan mahaifinmu kenan shima Abban ku yasa sunan haifinsa Ishaq shine suke kiransa da Haisam.
Haka yaran suka taso cikin kulawa musamman ma Aysha da Mukhtar sunfi kowa basu kulawa. Cikin ikon Allah shekarar su Faheem uku allah ya azurta Aysha da samun ciki, kowa ya tayata murna sai d'auki akeyi da murnar wannan cikin, cikinta yana da wata shida Rukayya ma ta kuma samun nata rabon, a lokacin ne kuma Ibrahim abokin Mukhtar yayi aure.
Kasuwanci yana cigaba da bunk'asa yayinda mak'iya suke yiwa Mukhtar bak'in ciki da d'aukakar da Allah ya bashi. Ranar wata laraba da bazan tab'a manta wa ba a rayuwa ta rana mafi muni a garemu ranar dana rasa d'an uwana na kuma rasa mahaifiyata ga kuma Aysha matar Mukhtar itama mukayi rashinta.
Mun saba kullum da daddare bayan sallar isha'i muna zama da iyalanmu mu tattauna matsalolinmu, ranar tunda muka zauna Mukhtar yake cewa kansa yana masa ciwo Aysha ta kawo masa magani ta bashi yasha duk da cewa a lokacin tayi nauyi, bayan d'an wani lokaci kawai muka ga Mukhtar yana yi mana wasu abubuwa tamkar wani mahaukaci lokaci d'aya ya canza ya koma yana yi mana hauka tuburan sam ya fice a hankalinsa, hankalinmu ya tashi duk muka hargitse musamman ma Aysha wadda tsabar tashin hankali a lokacin nak'uda ta kamata, hajiya kuwa hawan jininta ya tashi muka rasa ya zamuyi kawai nida Abban ku muka samu dak'yar muka tura Mukhtar d'aki muka kulleshi hankali a tashe mukayi asibiti dasu hajiya.
Muna zuwa cikin gaggawa aka karb'e mu sakamakon wahalar da Aysha ta sha wajen nak'uda yasa ta rasa duk wani k'arfinta suka ce saidai ayi mata aiki, a lokacin lafiyarta kawai muke da bukata ba tare da tunani komai ba na saka hannu, Ana shirin yi mata aikin ta haifo 'yarta sai dai tana haihuwa Allah ya karb'i ranta munyi kukan rashinta don Aysha macece mai kirki da sanin darajar d'an Adam, don haka Ana kawo yarinyar nayi mata hud'uba da sunan mahaifiyarta.
Hajiya kuwa dak'yar likitoci suka samu hajiya ta farfad'o har ta d'an ware likitoci suka bamu damar shiga mu dubata, hajiya tayi murna da ganin yarinyar da Aysha ta haifa, ta tambayemu lafiyar Aysha da munyi niyyar b'oye mata saboda yanayin ciwonta amma Faheem yayi caraf ya fad'a mata Amminsa ta rasu don haka suke kiranta.
Nan fa jikin hajiya ya kuma tashi Dr da yaga jikinta ya dinga fad'a itama a lokacin tace ga garinku nan. Nan fa muka kuma shiga damuwa Rukayya da momynku suka fad'i a wajen a sume hankalinmu ya kasa kwanciya nida Abban Ku.
A tak'aice dai haka ranar muka yini cikin zulumi da rud'ani, washe gari muka tawo da gawawwakinsu hajiya gida abinda muka samu a gida yasa nima saida na ziyarci asibiti don nima ban tab'a tunani zan kuma rayuwa ba don zuwa mukayi kuka tadda Mukhtar ya b'alle k'ofar ya bar gidan. Abbanku shine yayi k'arfin zuciya yasa akayi musu sallah aka kaisu makwancinsu, ni kuma yasa aka kaini asibiti shi kuma ya zauna da sauran dangi suna karb'ar gaisuwa.
Bayan na samu sauk'i munyi cigiya a gidan radio dana TV amma bamu samu Mukhtar ba haka muka hakura muka mikawa Allah lamarin, abinda ya bamu mamaki ko da wasa Ibrahim bai zo mana gaisuwa ba balle yayi mana jajan rashin d'an uwanmu.
Ni na d'auki Aysha yarinyar Mukhtar na cigaba da rik'onta." Daddy yasa tissue ya goge hawayen daya zubo masa, sauran matan ma duk kuka sukeyi musamman su mamy ji suke mutuwar ta dawo musu.
Cikin kuka harda majina Hibbah tace "Daddy wace Aysha da Ammi ta bari?" Daddy ya d'ago ya dubi duk 'yan d'akin "kuyi hakuri yauzan bayyana duk wani sirri da muke b'oyewa, Hibbah Ayshan da aka haifa ba kowa bace illa.............

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.