Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 39 of 51
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page4⃣5⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
*a gurguje pls*
Sagir mijin Aunty Aysha inspector ne shiyasa yayi ruwa yayi tsaki a kwana uku suka damk'e Faruq ta hanyar amfani da company'n Layin da yake amfani dashi don gano inda yake, sun sameshi ne agidan gonar Daddy dake wajen gari inda yake yunk'urin raba Hibbah da mutuncinta.
Bangaren Faheem Allah ya taimaka ya farka sannan su Abba suna bashi kulawa daidai misali, anyiwa Kausar waya ita hankali a tashe ta nufo asibitin, kwana ukun da yayi alhamdulillah ya samu lafiya musamman ma Daddy ya tabbatar masa da aurensa da Hibbah babu fashi tana nan a matsayin matarsa, tuni Faheem ya watstsake ya samu sauki don shi a yanzu ji yake babu wani abu da yake damunsa duk wata matsala yashi ta kau. Su momy ne suka zaunar da Kausar suka yi mata nasiha mai sanyaya jiki kafin su fad'a mata abinda yake faruwa, ta girgiza sosai dajin a dalilin aikin da take yi mijinta zai k'aro aure sannan kuma 'yar aikinta zai aura gaskiya wannan aikin bata ga amfaninsa ba tunda bata da lokacin Bawa mijinta kulawa. Da bata d'auki hakan wani abu ba sai yanzu, sai yanzu take ganin illar wannan aikin nata na bank ga 'ya mace tunda ta gani a kanta wace irin kulawa ce Faheem baya bata duk da ta fifita aikinta akan zaman aurenta hakan baisashi ya daina bata kulawa ba, babu abinda ta rasa a wajensa ga d'anta Nawaz data k'wallafa rai akansa shima sam bai Saba da ita ba yafi sabawa da Daddy'nshi da kuma Hibbah, ita kama shikenan bakin alk'alami ya bushe, me yasa bazata bashi kulawa kamar yarda yake bata ba? Me yasa ta zab'i ta k'untatawa iyalanta ta fifita aikinta akan mijinta da d'an? Lallai ta tafka babban kuskure wanda baza ta tab'a iya gyarashi duka ba tunda gashi a sanadin haka mijinta zai auri 'yar aikinta wadda tafi tsana.
Ranar da aka damk'e Faruq suna kamashi suka yiwa su Aysha waya suka fad'a mata ita kuma ta fad'awa su Abba, Daddy have su huce dashi yanzu zasu zo su amshesa, don sunyi shawara da su mamy sun yanke hukuncin kaisa gidan mari su kuma cigaba da yi masa addu'ar Allah ya shiryesa. Faheem ba k'aramin farin ciki yayi ba da aka samo masa Hibbarsa, ya kuma hi dad'i da hukuncin dasu Daddy suka yanke don hakan shine daidai. A lokacin Daddy da Abba suka je suka amshi Faruq suka wuce dashi gidan mari, yayin da inspector Sagir ya kawo ta asibitin wajen su Aysha bama su had'u da su Daddy ba, dama kuma bata tab'a ganin ko d'aya daga cikin daddy ko Abba ba.
Inspector Sagir yasha godiya da addu'a wajen su Aysha da su momy har ma da Hibbah d'in, yayin da Faheem yayi masa kyauta mai tsoka tare da yi masa godiya.
Tunda Hibbah tazo bayan Sagir ya koma bakin aikinsa su Aunty suke ta tambayarta abinda ya faru, Hibbah ta numfasa tace "Aunty Allah abin tsoro ne, sai ka jima kana shirya abu amma matuk'ar bai nufin hakan da faruwa ba babu Wanda ya isa yasaka hakan ya faru, Aunty ashe Faruq ya jima yana shirya hakan yayi amafani da Kalmar so wajen ganin ya aikata nufinsa a kaina ashe duk yaudarace yana sone ya aure ni daya samu abinda yake so sai ya rabu dani, don yaga bani da gata bani da galihu yanson ya wulakanta min rayuwa don kawai ya cika burinsa akaina." Sai kuma ta fashe da wani kuka mai ban tausayi, Aunty ta janyota jikinta "Hibbah kiyi shiru Allah yana tare dake shine gatan mu kuma nima ina tare dake" da hawaye tab a kan fuskarta ta d'ago tana kallon Faheem dasu mamy sannan ta dubi Aunty "na gode Aunty da kulawar da kika nuna min Allah ya saka da alkhari, Aunty wai da gaske ne Daddy ne mijina yaushe aka d'aura auren?" "Waya fad'a miki Hibbah?" Ta d'anyi shiru "Faruq ne ya fad'a min, don Allah Aunty idan da gaskene ki rok'a minshi ya sake ni don wallahi Aunty bazan iya auren mijin Aunty Kausar ba kuma na d'auki Daddy kamar uba taya zan iya zaman aure da mutumin da nake jin nauyinsa nake bashi girma fiye da kowa a duniyar nan Aunty kuyi hakuri don Allah bazan iya zaman aure bashi ba" maganar Hibbah ta d'aga hankulansu duka musamman ma Faheem da yaji wani abu ya tokare shi, Aunty ta dubeta duk tayi sanyi "Hibbah ki tausayawa rayuwar d'an uwana wallahi Yaya yana sonki sosai wannan rashin lafiya da kika ganshi duk a sanadinki yake yi saboda Daddy yace lallai saiya rabu dake......" Nan Aunty ta kwashe komai ta fad'a mata, Hibbah ta kafa ta gumi ta ma kasa cewa komai tana tunanin wannan hukuncin na ubangiji, wato abinda baka tab'a zato ba saikaga ya sameka, matsayin da baka tab'a tunanin zaka taka ba sai Allah ya baka shi.
K'ofar aka bud'e Kausar ce rik'e da kwandon abinci Saudat ta rik'o hannun Nawaz ita da Safiyya suna biye da ita, da gudu Nawaz yaje ya rumgume ta "Aunty kinga daddy bashi da lafiya baki zo kin dubashi ba kin gudu gidan ummanki, Aunty nima bazan kuma zama a wajen momy ba idan zaki tafi ki tafi dani zan biki" ta k'ank'ame Nawaz tana shafa kansa tace "Nawaz ba inda zan kuma kowa ina tare da kai" yayi tsallan murna "da gaske Aunty Hibbah?" Ta gyad'a masa kai ya kuma rumgume ta.
Kausar ta ajiye kayan ta tsaya tana kallon su cike da tausayin kanta tabbas tayiwa kanta da yanzu duk wannan soyayyar da Nawaz yake yi Mata da ita zai yiwa.
Ta kalli Faheem shima kallonsu yake yi yana murmushi, yaji dad'in kalaman Hibbah hakan na tabbatar masa data amince zata zauna dashi kenan, su Aunty ma dasu momy sai murmushin jindad'i sukeyi. Hibbah kuwa ta kasa d'aga ido ta dubi Kausar saboda nauyinta da take ji, kuma bazata iya kallon idanun Aunty tace bata son d'an uwanta ba hakan zai zama kamar butulci da cin fuska shiyasa bata da wani zab'in daya wuce ta amince da auren, ikon Allah kenan wai akanta har Faheem yake da ciwon zuciya gashi a gadon asibiti a kwance yana ciwon so.
Saudat ta k'araso kusa da Hibbah tana murmushi cikin sigar tsokana tace "Aunty Hibbah matar Yaya" dukansu suka sa dariya banda Kausar da duk abin duniya ya isheta duk danasani da nadama ta addabi zuciyarta, yayin da Safiyya take bak'in cikin faruwar wannan abun take kuma jin tsanar Hibbah a zuciyarta sai wurga mata harara take yi.
Hibbah tayiwa Saudat hararar wasa, Saudat tayi kamar bata gani ba ta cigaba "mamy da Aunty nasan kune akan komai don momy ba shiga zatayi ba, yanzu yaushe ne zamu sha bikin babban Yaya kusan mune manyan k'awaye" wani bak'in ciki ya tsayawa Safiyya ji take kamar taje ta doki Saudat, Hibbah tayi k'asa da kanta cike da kunya da kuma jin wani iri don gani take kamar cin fuska ne abinda Saudat take yi, tana yi ne saboda Kausar wanda ita tana ganin rashin dacewar hakan. Aunty tace "Kai Saudat irin wannan zumud'i haka ki bari su Daddy su dawo sai su tsaida mana rana" Saudat ta gyad'a kai "sai mu fara shiye shirye kenan." Tsayuwa ta gagareta ta samu gefen gadon Faheem ta zauna kanta a k'asa tana tunani yanzu shikenan Faheem ya zama nasu su biyu, ta d'ago kai ta dubeshi shima ita d'in yake kallon yana tausaya mata don yasanta akwai zafin kishi yayi mamaki ma da bata wani tashi hankalinta ba sosai yayi mata murmushi, ta kawar da kanta gefe.
Su Abba ne suka shigo da sallama suka amsa musu tare da yi musu sannu da zuwa, Abba ya dubi inda Hibbah take Nawaz yana zaune akan cinyarta kanta yana k'asa yana murmushi yace "surikarmu ki d'ago fuskar taki mu gani mana kinsa mana yaro kwanciya ciwon so, naga ma ya samu lafiya saboda ya ganki" cikin sigar barkwanci Abba yake maganar saboda Abba akwai shi da barkwanci, Hibbah ta kuma k'asa da kanta cikin kunya, su Daddy dasu momy sai murmushi suke yi Faheem kuwa shima k'asa yayi da kansa don jin nauyin maganar Abba.
Saudat tace "surikar su Abba ki d'ago kanki su ganki" ta fad'a tana mata dariya, mamy tace "kai Saudat kin takurawa surikata fa, zan fara rama mata" momy tace "gaskiya kam Saudat kin takurata da yawa ke a haka ake Matar Yayan?"
Daddy yayi dariya "nifa na k'osa naga fuskar wannan mai sa'ar data sace min zuciyar Faheem haka har ya kasa nutsuwa saboda rashinta" su aunty suka kwashe da dariya.
Gaban Hibbah ne ya shiga fad'uwa jin muryar da bazata tab'a mantawa ba zuciyarta ta shiga harbawa da sauri ta d'ago kanta don tabbatar da muryar da taji, a hankali ta d'ago kanta ta zubasu akan Daddy cikin mugun hargitsi da rikici ta tashi tsaye tana kallon daddy murya na rawa tace "baa.......baa? Baba kaine?" Jin muryarta ya hargitsa Abba muryar da yafi so a duk duniya kuma bazai tab'a manceta ba har *Abadan* ya jiyo cikin fargaba yace "Aysha....." Hibbah ganin fuskar Daddy yasata zubewa a k'as...............
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.