Complete Hausa Novels

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 23 of 51

B'angaran Faheem kuwa yana shiga ya zauna kan gado gami da jefar da takardun yayi jim zuciyarsa zafi take da tana tafasa sai yaji gumi ta kowanr kofofin gashinsa kamar Mai had'iyar wuta, ya kasa sanin wannan abu ciwo ne ko lalura ne ya rasa meke masa dad'i, ya huro iska mai d'umi a bakinsa zafi dad'a k'aruwa yake a ko ina na jikinsa, mik'ewa yayi ya shoga toilet ya sakarwa kanshi shower snyin ruwan ya ratsa shi had zuciyaarsa, bai san iya lokacin da ya d'auka ba sannan ya fito ya kunna AC ya kwanta ya d'ora kansa bisa pillow ya lumshe idanunsa.
Yana tunanin wai shin me yasa ya damu kansa da yarinyar nan? Shi fa ba sabgarta yake shiga ba don me yake jin zafo don ya ganta da wani ina ruwanshi da sabgarsu? Don me zai tunzura haka don ta fit a bada izininshu bane ko kuwa metayi masa ya b'ata ransa har hankalinsa ya tashi haka?
Ji yayi anyi masa kiss gami da shafo sajensa, juyowa yayi ya rumgumota yayi ajiyar zuciya, ya lalubo abinshi duk lefinta ne da bata tarairayarsa bare ta kwantar masa da hankali in ya shiga damuwa.
Juyowa tayi suna kallon juna abinda ta gano a idanunsa ya tabbatar mata akwai rikici wani abu ya tab'o mata shi. Ta kuma k'ura masa ido "dear me yake damunka ne naka ka sauya ba kamar yadda nake dawowa na sameka ba," bai fad'a Mata abinda me zuciyarsa ba sai dai yace Mata wai baijin dad'i tunaninta da kewarta suke damunsa, nan ta shiga yi masa kisses masu zafi don k'ok'arin mantar dashi dan tasan lefin tane Sam bata bashi kulawa kullum ita tana wajen aiki kamar agogo..

***

Hibbah na zaune a d'aki taga mutum kawai a gabanta a karo na biyu ya kawo mata ziyarar bazata yunk'urun guduwa tayi ya kuwa yi azamar cafkota kamar 'yar tsana ya rik'e ko motsi bata iyawa, tasa kuka mai ban tausayi yau ta gamu da gamonta kashinta ya bushe in dai kisa ne yau Faruq ya karta. Ya tallafo hab'arta ya juyar da kanta gefe, tsananin bugun zuciyarta yasa taji zata fad'i don dai ya rik'eta ne amma da tuni ta fad'i.
Shi kuwa Faruq tamkar wata sabuwar halitta yake ganinta d'an hakin da ka rain a shike tsone maka ido, wai Hibbah ce macen da ya kasa jimiri da dakewa akanta so guda ne kamar Hibbah babu abinda yake buri fiye da ita a *RAYUWA RSA*, duk tsarinsa ya wargaje d'aya bayan d'aya abin har mamaki yake bashi ya tashi hankalinsa idan yana zancen zuci sai ya fito fili yaji yana sambato.
A yau tausayi take Bashi a yau ji yake ba mace mai k'imarta, a yanayin sonta da yake addabarsa, don't me why not baisan dalili ba? Ya sassauta murya "Hibbah why? Why Hibbah? Me yasa nake son ki wallahi babu dad'i akwai wani abu ne daga Allah, ni fa na haukace akanki Hibbah ke baza ki Sani ba har sumbato nake idan sonki da tunaninki sukayi min zabi, ranar dana ganki da wannan guy d'in kasa barci nayi Hibbah, son nan shu'umi ne ya canzani Hibbah ya canza min manufa a kanki ki manta da baya daya kasance kuskure ne don a da can ban iya tantance sha'awar da nake miki yanxu kyauta kika mallaka min kanki bazan iya yi miki komai ba sai Allah yasa aure a tsakanin mu Hibbah bud'e idanunki ki dubi masoyinki." Hawaye ne yake zuba a idanunta, yasa hannu ya lakuto hawayenta ya shanye kuma sassauta murya yayi "Hibbah kina sona kuwa?" Saura kad'an ta fad'i yayi saurin tarota kanta yayi gingirim.
"Hibbah" ya fad'a da rad'a, wani abu ke taruwa cikin idanunsa, tsorone yasa ta gyad'a mishi kai alamar wai tana sonshi don tasan Faruq sarai baida tausayi da imani kwanda ta bishi su rabu lafiya.
Ya kafeta da ido can kuma yayi murmushi "matsoraciya ban yarda da wannan amsar ba ki bud'e bakinki naji muryarki kiyi magana da yawunki," "uhmm ina sonka" muryarta a sark'e ta fad'a. Ya shiga tsantsar farin ciki "are you sure? Kin tabbatar alk'awari ne fa," ta rufe bakinta da hannunta yadda zuciyarta take bugawa zai iyasa jininta hawa saboda tsoro.
Ya ja da baya "ina k'aunarki Hibbah zan tabbatar miki da hakan idan kin samu nutsuwar zuciyarki, don Allah ki daina jin tsorona ki amince dani," ta gyad'a kanta, Nawaz ya k'ank'ame shi "uncle kullum kazo sai kasa aunty Hibbah tayi kuka saina fad'awa daddy na." Bata san sanda ta zube k'asa ba ta had'a kanta da gwaiwa, ya shafa kan Nawaz ya zare masa ido tare da d'ora hannunsa a kan leb'ensa yace "shiiit! Keep quiet surutunka yayi yawa parrot, tafiya zanyi gobe zan kawo maka ice cream da ball," Nawaz yayi dariya ya kad'a kansa.
Ya kashe bakin surutu tunda zai kawo toshin baki ya d'aga mishi hannu "uncle bye sai gobe," yayi murmushi tare tare da fita daga parlor.
Nawaz dafa bayanta "Aunty Hibbah uncle dukanki ko? Saina fad'awa daddy shima ya dukeshi," bata kulashi ba yace "kinji,"

Sallamarshi ta katse Nawaz ta kasa d'ago kanta bare yayi masa sannu da zuwa, ta runtse idanunta bugun zuciyarta ya tsananta, sai kuma taji wani sanyi yana kad'ata wani abune ta kasa fahimtarsa a duk sanda taji Faheem, bata san ya dinga ganinta da wani lefi, mutum ne mai k'ima a idonta.
Ya rumgume me Nawaz suka zauna hankalinsa yana kan Hibbah kome yake sata yawan damuwa? Nawaz ya kalli daddy'n nasa "Daddy, uncle ne ya so shine............." Nan take fuskarshi ta canza kamar an fad'a mishi sak'on mutuwa, d'if komai ya tsagaita a kwanyarsa, wani abu ke faruwa dashi fiye da wanda yaji ranar dayaga Hibbah da Jabeer, dole Faruq yafi tada masa hankali idanunsa sun sauya. Bai sake kallon ta ba, ta mik'e ta shige d'aki ta fad'a kan gado, wani bak'in ciki ya addabeta ya zatayi da *RAYUWARTA*, shiru ma magana ce a wajen Faheem tun a karo na farko yaja kunnanta da gargad'inta akan Faruq gashi ya kuma jin Faruq yazo wajenta dole ya zargi da yawunta da sanint Faruq ke zarya a gidan, haka tayi ta jin haushin Faruq zuciyarta sam bata jin dad'i.
Tun daga ranar basu k'ara had'uwa da Faheem ba, sun shiga wasan b'uya naushi ya kuma k'aruwa.

Shi kuwa Jabeer ko yaushe yakan tuntubeta a waya yaji wai yaushe zai zo ya ganta, ita kuma ganin Faheem baice da ita komai ba sanda ya gansu da Jabeer yasa bata damu ba ko kad'an tunaninta Aunty Aysha ta fad'a masa komai game da Jabeer, don haka ta bashi damar cigaba da mu'amalarsu.
Kamar kullum da yamma rana tayi sanyi ya shigo saidai bai samu damar shigowa harabar gidan ba saboda tsaro daya samu an canza wani mai gadi, kuma ya sanar dashi cewa Mai gidan ya kafa dokar shiga gidansa.
Waya ya zaro ya kira Hibbah ringing biyu ta d'auka yace "na k'araso ina bakin gate d'in," "to" ta fad'a tare da kashe wayar ta fito.
Tana sanye take da da atampa green light da ratsin baby pink ta lullub'o baby pink mayafi a waje ta iskeshi ta k'arasa suka yiwa juna murmushi, ya rik'o hannun Nawaz yana da san yara sosai yace "Hibbah kina jin dad'inki kullum kike min, ya batun mu kinsan rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya," ta sunkui da kanta "ai nace na amince, munyi waya da Umma tayi farinciki," yayi dariyar jin dad'i "to Hibbah na gode da karb'ata da kikayi, ni kuma sainaga abinda ya turewa buzu nad'i dan Zan turo manyana su gana," "kamar ya ban fahimta ba," wani kallo yayi mata harsaida taji kunyarshi "to ina neman izini zan turo manyana wajen iyayen mu, za'a ga Alhaji ko? Hibbah aurene ya kama ceki zaki fi samun nutsuwa hankalinki ya kwanta ki samu wadataccen 'yan ci"
Shiru tayi cikin nazarin jawabinsa babu shakka gaskiya ya fad'a domin har yau a rakub'e take gidan mutane matsayin mai aiki, amma in d'akin aurenta ne fa alfarmace da darajarta, ta kalleshi "bazan b'oye maka komai ba kamar yarda kaji a bakin Faruq ya fad'i matsayina a gidansu ni 'yar aikinsu ce, Aunty Aysha ita ce ta taimakawa *RAYUWATA* ta bani kulawa da ilimin da nake yi, dan haka kai tsaye bazan amsa maka ba har sai nayi shawara da Aunty dan bani da wadda ta fita a duniyarnan sai Umma," yayi d'an murmushi "naji bayananki kuma na gamsu, nidai na ganki nace ina son ki, ra'ayi nane na gamsu dake Hibbah don allah nake sonki," "na fahimce ka, kuma ka kuma bani dama dai na sanar da aunty," yayi dariya "kina son Auntyn nan da yawa," "ba doleba masoyinka ai masoyinka ne," ya kuma yin dariya "to na gode sai kuma yaushe?" D'as d'as k'irjinta ya data gano motar Faheem, a d'an sace ta kallo shi ko inda suke bai kalla ba, mai gadi ya bud'e k'ofar tare da d'aga masa hannu "barka da dawowa," hon yayi masa ya shiga ciki.............

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.