Complete Hausa Novels

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 42 of 51

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page4⃣8⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

Suna zuwan wanka sukayi kawai suka shirya Faheem da Kausar kuwa saida zukaje gida suka kintsa a can Kausar ta tawowa da Hibbah kayanta, Aunty ma saida taje gidanta anan ta kira Sagir mijinta take fad'a masa abinda yake faruwa yayi mata izinin zuwa kuma yayi mamaki ashe su *dangin juna* ne shiyasa Allah ya dasa musu k'aunar junansu.
Su Aunty suna dawowa Daddy yasa Adamu ya fito da mota Daddy da Abba suka shiga baya, yayin da motar Faheem kuma Kausar ta karb'i tuk'in shi kuma yana gefenta mamy momy da Hisham suna baya.
Motar Aunty kuma Hibbah tana kusa da ita Nawaz yana kan cinyarta sai Safiyya da Saudat a baya, sai hira suke cike da k'auna a haka suka k'ara gidan Alhaji Sani.
Sunyi sa'a yana gida don shigowarsa kenan daga masallaci motocinsu sukayi parking a gidan, yayi mamakin ganin zugarsu haka da yawa amma duk da hakan bai hanasa tarbarsu cikin karamci ba yayi musu iso cikin gidan direct ya shiga dasu har parlor.
A parlor suka tadda Umma ita kad'ai kana zaune tana sauraron karatu Wanda kana shigowa parlor'n zakaji yana tashi. Tana ganin su Aunty sun shigo ita dasu Hibbah, Saudat, Safiyya da Kausar ga kuma mamy da momy ta tsayar da karatun ta taresu da murna suka zazzauna akan kujerun parlor'n tana ta yi musu sannu da zuwa.
Ta cika musu gaba da abinci kala kala ga lemuka sannan suka shiga gaisawa, anan su momy suke fad'a mata basu kad'ai bane tare suke da mazajensu amma su suna tare da Alhaji zasu shigo daga baya Umma tace to shikenan dama da hijab d'inta a jikinta ita a lokacin ta idar da sallah.
Sun d'an tab'a abinci suka shiga hira kamar sunsan juna, karb'ar da umma tayi musu ta burge su sosai sunji dad'i, suna cikin hira su Abba suka shigo da sallama suka amsa musu, kallonta Abba ya tsaya yi zuciyarsa na harbawa da k'arfi tabbas babu tantama wannan itace Aysha k'anwarsa don ga muryarta nan ga kuma kamanninta nan sak dana hajiyarsu.
Ya ilahi! Ikon Allah kenan dama ashe zai kuma sanya Aysha a idanunsa, suka zauna ta kawo musu abubuwan tab'a baki, sai binta da kallo yake tabbas itace ga tafiyarta nan ma.
Kallon da Abba yake mata ya fara b'ata mata rai don duk inda tayi saiya bita da kallo don haka lokaci d'aya umma ta had'e rai. Bayan sun d'an huta Alhaji Sani ya fad'a mata wajenta suka zo ba wajensa ba umma ta mayar da hankalinta kansu tana son jin meke tafe dasu don ita tayi tunanin ma akan maganar auren Faheem da Hibbah ne.
Daddy ne yayi gyaran murya ya gyara zama ya shiga bata labarin abinda ya faru ya kuma tabbatar mata da cewa Hibbah 'yarsu ce basu sani ba. Umma hawayen farin ciki ya sauko mata "alhamdulillah naji dad'in wannan al'amari ikon Allah kenan ashe 'yar kuce shiyasa Allah ya sanya k'auna a tsakaninku har kuka inganta mata musamman ma Aysha yadda kike kula da Hibbah babu Wanda zaice ba 'yar uwarki bace ita ashe k'anwarki ce jinin Ku d'aya"
Daddy ya d'ora da cewa "bayan batun Hibbah akwai wani dalili mai k'arfi da ya samu zuwa gidan nan" ya mik'a mata hotunan da Abba ya d'auko nata da su Alhajinsu, ta amsa tana gani cike da tsantsar mamaki tabbas wannan suna Kama da ita lokacin tana yarinta don baza tace Hibbah bace don dad'ewar hoton amma kuma ita tunda take bata tab'a sa irin wad'annan kayanba.
Ta dubi Daddy cikin nutsuwa tace "Alhaji gaskiya wannan bani bace don banma tab'a saka irin wad'annan kayan ba da na tab'a saka su to babu tantama nice" Daddy yayi murmushi "tabbas kece a jikin hoton nan Aysha" nan Abba ya bata labarin duk abinda ya faru. Umma ta sunkui da kai tana tunani ita dai tasan tabbas a k'auyen katselle aka haifeta, ta yaya zasu zo su bata wani labari daban bayan kuma ga mahaifanta nan a raye baba da gwaggo. Ta dubi su Daddy "kuyi hakuri gaskiya wannan labarin ma ba ni bace a cikinsa don ni iyayena suna nan a raye basu mutu ba" Daddy ya kuma murmushi "Umman Hibbah kina nunawa kamar baki yarda da mu ba ko? To idan ba damuwa ki shirya yanzu muje wajen su iyayen naki na k'auye mu tambayesu zasu fad'a miki gaskiyar abinda yake faruwa, mun tambayi Alhaji ya amince mu tafi tare yanzu kawai shiryawa zakiyi mu tafi."
Umma tayi shiru tak'i tashi daga wajen balle taje ta kintsa, Hibbah ce ta matso kusa da Umma ta rik'o hannayenta "Umma don Allah ki tashi muje don tabbatar da abinda su Abba suke zargi, Umma Abba yana son 'yar uwarsa yana sonki a kusa dashi ki taimaka masa don Allah" Umma ta kalli 'yarta ta "naji na amince zan biku" "yauwa Umma mun gode" Umma ta mik'e ta shiga d'aki ta d'auko duk wani abu dazata buk'ata ta fito suka nufi k'auyen katselle.

Motarsu tayi parking a k'ofar gidan su Hibbah don Daddy ne ya rok'i alfarma su fara tsayawa k'ofar gidan d'an uwansa don yana son ya fara ganinsa. Yara suka zo suka baibaye motocin, suka fito daga ciki suna kallon yanayin k'auyen Daddy ya kalli Hibbah "Hibbah shiga ciki kiyi mana iso" ta dubi Daddy duk yanayinta ya koma na tsoro sai k'ifta idanu take "Daddy tsoro nake ji inajin tsoron Inna lami wallahi" Aunty ta dafa kafad'arta "tawo muje babu abinda ta iya tayi miki" Hibbah ta gyad'a kai Saudat tace "nima zani" Safiyya da Kausar har suna had'a baki "ku tsaya ni" suka tsaya suka k'araso suka shiga gidan hannun Hibbah yana cikin na Nawaz.
Sukayi sallama Rahmatu ce ta amsa musu tana zaune a tsakar gida tasa turtsetsan cikinta a gaba, ta nuna musu tabarma suka zauna ta gaishesu ita sam bata gane Hibbah ba tace "kuyi hakuri yanzu innar zata dawo ta fita ne" Hibbah tace "ba komai ai zamu jirata sai dai bamu kad'ai bane akwai iyayenmu mata da maza a waje suna son ganin baba, ya dawo ne?" Rahmatu ta tsaya tana kallon Hibbah tana son gano wani abu tattare da ita, bata gane fuskarta ba amma muryar tana ta tunanin ko Hibbah ce amma kuma tana mamaki anya Hibbah ce. Hibbah ta katseta "wai Rahmatu aure kika yi ne na ganki da ciki?" Rahmatu ta zaro ido "Hibbah kece kinga yadda kika koma kuwa, Hibbah ki yafe min kinga yadda *RAYUWA* ta mai dani ko hausawa sunce idan zaka gina ramin mugunta ka Gina shi kajere wata Rana kai zaka fad'a, gashinan Inna taso lalata miki rayuwa Allah bai bata iko ba sai Allah ya dawo mata da abin kaina Hibbah ba aure nayi ba....." Sai ta saki kuka ta rik'o hannun Hibbah "Hibbah ki yafe min don Allah Inna ta b'ata min *RAYUWA* garin son kud'i Inna ta sani na koma karuwar k'arfi da yaji gashinan yanzu sun b'ata min rayuwa sun guje ni, cikin nan da yake ni kaina banson na waye ba a tsakanin sale direba ko kuma Musa d'an Inna delu. Hibbah kowa ya guje ni Inna kullum a cikin hantarata da kyarata take, duk son da baba yake yi min yanzu ya daina k'awaye na sun gujeni kowa a k'auyen nan k'yamata yake yi, Hibbah nayi nadama nayi Dana sanin biyewa Inna dana yi gashinan yanzu na lalata rayuwa ta" Hibbah ta shiga share mata hawaye itama hawayen na bin fuskarta "baki yi min komai ba Rahmatu na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe mana" "na gode 'yar uwata na gode, su waye wad'annan?" Hibbah ta dubi su Aunty "y'an uwan mu ne danginmu ne su bamu sani ba" "danginmu kuma kamar ya dama muna da 'yan uwa a birni?" Rahmatu ta tambaya cike da mamaki.
"Eh Rahma kuna dasu mana muma bamu sani ba sai yau d'innan" Aunty ta bata amsa, Rahmatu sai taji sunan wani iri don ba haka ake kiranta da shiba, Aunty ta shiga bata labarin duk abinda ya faru.
Rahmatu tayi mamaki sosai "Hibbah ashe rabon kije birni ki samo mana dangin mu ne yasa Inna ta turaki can ikon Allah, to ku shigo dasu ai ba'a barsu a waje ba ko?"
Wayar Hibbah tayi k'ara ta duba bak'uwar number ta gani, da kamar bazata d'auka ba sai kuma ta d'aga "hello my heart desire ya ake ciki ne kun barmu a waje" ai Hibbah suman zaune tayi jin furucin Faheem ta kasa magana yace "hello kina jina?" "Ammm.....dama......dama yanzu zanzo na shigo daku" ta fad'a cike da in ina ta kashe wayar, Aunty tace "keda waye kike masa in ina?" "Ba kowa Aunty Daddy'n Nawaz ne yace sunji shiru" Saudat ta kwashe da dariya "to ai saiki tashi kije kar kisashi ya kuma ziyartar Dr" Hibbah ta kai mata duka suka sa dariya.
Ta fita ta shigo dasu Rahmatu ta kuma shimfid'a musu wata tabarmar suka zauna ta gaishe su, Hibbah ta gabartar mata da kowa a cikinsu, Rahmatu ta nuna Umman Hibbah "Hibbah kardai kice min wannan Umma ce?" "Itace Rahmatu" Rahmatu ta zube a gaban Umma tana neman yafiyarta ta fad'a mata duk abinda ya daru da ita.
Umma tace "babu komai Rahmatu ni baki yi min komai ba ina innan taki?" "Ta fita amma yanzu zata dawo...." Kafin ta rufe baki Inna lami ta shigo tana kallonsu da mamaki................

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.