Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 12 of 51
Saman suka hau nan Hibbah ta kuma ganin abubuwa iri iri sunje tayiwa momy godiya, mommy ta nuna Mata ai babu komi ita dai fatansu Hibbah tarik'esu da amana kamar yadda suma zasu rik'eta cikin aminci. Hibbah taji dad'in kalaman momy nan ta kuma yiwa momy godiya suka sauko. Da suka dawo Hadiza na d'akin Hibbah cikin happy ta nuna mata kayan da aka bata, Hadiza tayi ta yaba kyahun kayan.
Aunty ta kalli Hibbah tace "taso muje ki rakani wajen tailor mu kai masa kayan" Hibbah tace to tare da mik'ewa ta d'auko hijjab d'in data zo dashi zata sa Aunty tace "haba Hibbah karki badani mana kinyi kwalli kuma zaki d'auki wannan hijjab d'in kisa, bara na d'auko miki mayafi a kayana kisa taso muje d'akina." Binta tayi kamar jela suka kuma komawa sama, wannan karan d'akin Aunty'n suka nufa direct wardrobe d'inta Auntyn ta nufa ta d'auko mata mayafi fari da wani ta kalmi me dan tudu shima fari tace "gwada wannan mugani zaiyi miki," sawa Hibbah tayi sai gashi yayi mata amma kuma yad'an yi mata yawa, Aunty tayi dariya tace "tab Hibbah kin fini karamar k'afa." Dariya Hibbah tayi tace "ai kuwa dai gashi ammafa kamar yayi min tsayi Anya zan iya tafiya dashi?" aunty tace "gwada tafiya dashi muga" Hibbah tad'an fara tafiya dashi ad'an tsorace, aunty ta kwashe da dariya tace "ki saki jikinki kiyi tafiya," a hankali take takawa dashi tana zagaye d'akin har ta d'an saba idan kaga yadda take tafiyar sai ka rantse yanga takeyi. Aunty ce ta ja hannunta suka karasa gaban gadonta, tana cewa "zo na gyara miki wannan d'aurin d'ankwalin ba haka ake d'aurawa ba," kunce mata d'aurin tayi taga ta cure gashinta girgiza kai Aunty tayi ta dauko kum da man kitso ta shafe mata kan dashi ta taje ta d'auko ribbon tayi mata packing gashin sannan tayi mata d'auri mai kyau ta shafa mata powder da lipstick ta bata kwalli tasa, dana kalli Hibbah saida na kuma kallon ta don wani mugun kyau danaga tayi Masha Allah ashe komai nason gyara.
Aunty ta kalleta tace "Hibbah kin ganki kuwa yadda kikayi kyau Masha Allah kamar baki tab'a *RAYUWA* a k'auye ba," ta fada tana dariya. Murmushi Hibbah tayi na jin dad'i tace "Auntyna bani da bakin yi miki godiya na gode Allah ya saka da alkhari na gode," hannu Aunty ta d'ora akan lips d'inta tace "shiiit bana son yawan godiya Hibbah, tashi muje yamma nayi," da haka suka fita sukayiwa momy da Hadiza sallama gidan saiya zama shiru ba kowa dayake su Safiyya duk sun tafi islamiyya, suka fito daga gidan Adamu driver Aunty tayiwa magana ya fito da mota suka wuce. A mota Aunty take tambayar Hibbah tace "Hibbah a k'auye izunki nawa?" Hibbah tace "izzuna goma sha bakwai," d'an zaro ido Aunty tayi tace "dama k'auye karatunsu yana sauri haka?" Girgiza kai Hibbah tayi tace"ba'a makaranta kawai muke karatu ba ummana ce take yi min k'arin karatu idan ta biya min yau gobe zan kawo mata hadda," Aunty ta girgiza Kai alamar gamsuwa tace "kenan duka bakwai d'in yana kanki yanzu," d'aga kai Hibbah tayi alamar eh.
Bangaren Faruq kuwa yana komawa d'aki ya fad'a gado takaici da mamaki duk ya rufeshi ya soma tambayar kansa wai me yake damuna me na gani a jikin yarinyar nan da har na kasa jurewa na kasa saita kaina, juyi ya kumayi yace yarinyar dabaza ta huce sa'ar Saudat ko Safiyya ba at least baza tafi 13 or 14 years ba amma duk nabi na rud'e a kanta bayan ga manyan babies nan a gari dasuke kawo min Kansu ba wadda na rud'e akanta sai wannan 'yar yarinyar, murmushin mugunta yayi yace kin janyowa kanki Hibbah don kota halink'ak'a saina d'and'ani wannan dirin naki kafin na koma hutu tunda kikasa har Aunty Aysha ta gane halina na nan. Janyo pillow yayi ya rumgume siffar Hibbah na kuma tariyo masa cikin kwanyarsa, yace yarinya k'arama amma ta had'a abubuwan da wasu manyan babies din ma basu dashi duk da cewa yanxu suka fara tasawa abubuwan nata, amma tana da diri mai kyau da d'aukar hankali, ya tuno yadda ya ganta d'aure da towel sai ya kuma matse pillow gam a jikinsa, haka yayi ta tunaninta har dare ba mafita daya rufe idanunsa ita yake gani ga wata muguwar kasala da sha'awar kasan cewa da mace data saukar masa kasa jurewa yayi, ya tashi ya shiga toilet ya sakarwa kansa ruwa na wani lokaci kafin ya fito ya tsala wanka cikin k'anan kaya ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshi ya zari key din motarshi ya nufi club.
Su kuwa su Hibbah sunje sun kaiwa tailor d'inkunan yace nanda kwana biyar zai kawo, daganan Aunty tace zasu wuce super market zasuyi siyayya, wani babban shop na kayan mata suka shiga Aunty ta yiwa Hibbah siyayya ta had'a da kud'in hannunta duk tayo mata siyayya haka suka d'auko hanyar gida da kaya nik'i nik'i. Suna shigowa gida ana kiraye kirayen sallah don haka kai tsaye Aunty tabi Hibbah bangarensu suka ajiye kayan anan ma sukayi sallah sannan Aunty ta shiga nuna mata yadda zatayi amfani da komi har pad tace mata wannan idan kina al'ada shi zaki dinga amfani dashi ta nuna mata yadda ake sakawa.
Sai bayan isha'i malam Jamil yazo bayan sun gaisa dasu momy ya tashi ya nufi d'akin da suke karatun a ciki, su Saudat suka mike kowa ya d'auki kayan karatunsa suka bi bayansa dayake hadda sukeyi a wajensa suna zuwa suka shiga Bashi hadda.
Aunty tazo tayi kiran Hibbah suka tafi d'akin, bayan sun gaisa da malam Aunty tayi masa bayanin komai yace "ba matsala Aysha insha allah za'ayi yadda kikace kuma gobe in allah ya kaimu su tafi tare dasu Safiyya makarantar sai ayi mata komai zan karbi sunanta yanzu", Aunty tayi masa godiya ta koma ciki. Su Saudat sai harararta suke yi suna jin haushin yayar tasu wai akan me zata dinga had'a su da 'yar aiki. Malam Jamil ya kalli Hibbah yace "mene sunanki?" Hibbah tace "sunana *Hibbah Mukhtar Muhammed*" malam ya girgiza Kai alamar gamsuwa yace "izufinki nawa?" "Izufina sha bakwai" Hibbah ta Bashi amsa yace "hadda kikayi ko kuma biye?" Hibbah tace "hadda nayi," malam ya kalleta yace "zaki iya karanto min naji?" Kai ta d'aga, ya kalli Safiyya da take shirin fara Bashi haddarta yace "kiyi mana hakuri Safiyya bara ta biyamin naji," Safiyya tace "to malam" ya kalli Hibbah yace "bismillah" nan Hibbah ta shiga biya masa har ta gama yayi mamakin karatunta yarda take da tajwidi take fidda kowane hukunci ya jinjina mata, ya kuma yi mata k'arin karatu, saida ya tambaye ta shafi take so ko rabin shafi tace yadai biya mata kawai shafi d'aya ya biya mata, saida yaji ta iya sannan ya k'arbi haddar Safiyy...........
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page2⃣2⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.W.A
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
*Idan kaji ana a marmatsa giwa ce ta iso, gaba dai gaba dai uwar gayya karo da karo sai rago waye zai bada tauranshi _AYSHA ALIYU GARKUWA_ ke kad'ai kike baki da sa'a.*
*D*a haka malam Jamil ya gama biya musu karatu ya tafi.
Hibbah tana zuwa d'akinsu tayi ta bibiyar karatun batayi bacci ba sai da ta tabbatar ta haddace sannan ta samu tayi bacci mai dad'i cike da mafarkin ummanta, tunda take bata tab'a yin barci akan abu mai taushi ba kamar nayau don katifar tana da taushi.
Ta Saba k'arfe hud'u da rabi take tashi, haka yauma ta tashi, ta d'auro alwala tazo ta rik'a jero nafilfili tana godiya ga allah bisa wannan ni'ima dayayi mata. Kiran sallah assalatu ne ya d'agata daga wajen ta tada sallar asuba, bayan ta idar ta tashi Hadiza tayi itama sallah bayan ta idar ta zauna tana jan carbi, ita kuwa Hibbah karatunta ta bibiya sannanta d'ora da azkar na safiya dayake ta haddace su.
Sai gari ya fara haskr suka fito da Hadiza ta nunnuna mata inda zata share bayan tagama shara ta nuna mata yadda ake mopping da goge kayan kallo, ita kuma ta shiga kitchen don had'a breakfast.
Bayan ta gama gyara ko ina ta koma nasu d'akin ta gyara ta wanke toilet, Hadiza ta bata turaren wuta tace tasa a parlor kafin su tashi ta gyara musu can saman, Hibbah ta amsa tasa tuni parlor ya d'auki k'amshi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.