Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 8 of 51
Suna shiga gidan sukaci sa'a Rahmatu na nan, delu tace "shikenan nan ma Rahmatu nanan kinga saita shiga ta kirata koh," kallonta lami tayi tace "toh allah yasa taje kema kinsan halinta." Delu dai batace komi ba suka k'ara cikin gidan.
Kujera delu taja ta zauna hakama lami amma ita tata kujerar kusa da Rahmatu ta kaita tare da kwantar da murya tace "yauwa Rahmatu Dan allah shiga gidansu Abu ki kira min Hibbah kice tazo yanxu." Kallon ta Rahmatu tayi a wulak'ance tace "tab ni wallahi na gaji babu ida zani" matsowa lami ta kumayi kusa da ita tace "haba autar inna kije mana don Allah" Rahmatu ta zumburo baki "wai me zakiyi mata ne bakince ta bar gidan ba, kuma kince ta tsaneni to me kikeso kuma tayi mana a gida?" Lami tace "aike baxaki gane ba aikatau za'a kaita birni kinga kenan duk kudin da aka bada na aikinta namu ne daga nan ma saina saimiki wayar da kikace kina so koh?" Daga Kai Rahmatu tayi cikin happy tace "eh wallahi inna ammafa kinyi dabara bara naje" ta fada tana mikewa da gudu tabar gidan. Lami tace "oh ni lami naga Randa Rahmatu zatayi hankali" delu tace "gaskiya kam."
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: πππππππππ
*RAYUWA* page1β£5β£to1β£6β£
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
πππππππππ
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.Z.W.A
Su Hibbah suna zaune a tsakar gida suna gyara waken alala ita da Abu da gwaggo, sai gay Rahmatu ta shigo gidan kamar an wurgota ko sallama babu ta kallesu d'aya bayan d'aya, sannan ta maida kallonta ga Hibbah tace "ke zo inna na kiranki," tana gama fadin haka ta juya ta fita abinta.
Tsorone ya bayyana k'arara a fuskar Hibbah ta kalli Abu tace "Abu kinji wai Inna naje ni wallahi tsoro nake ji." Abu tace "kuma ke zuwa zakiyi? Kika sani ma ko wani muguntar ta kuma had'a miki kawai zaki kwashi jiki kice zaki," gwaggo tace "ke inna ruwanki kika sani KO uban ne yace ta dawo?" Abu tace "tab, gwaggo kin dai fimu sanin halin matar nan wallahi ko yace ta koma sai tayi yarda tayi tace karya maida ta." Murmushi gwaggo tayi tace "hmmm Ku yara ne bazaku gane ba, ai zata maida tane don ta ci mata gaba da tallanta, ko kuna tunanin wannan mara kunyar 'yar tata Rahmatu zata daukar mata talla?" Hibbah wadda tayi shiru tana sauraronsu tace "wallahi gwaggo nima abinda nayi tunani kenan," ta mike tsaye tare da cewa "bara naje naji gwaggo," "waike yanxu xuwa zaki yi?" Abu tayi saurin katseta, Hibbah cikin damuwa tace "to ina da wani mafita ne banda naje d'in?" Abu ta tab'e baki tace "tab wallahi da nice baza ni ba," gwaggo tace "kinga karki biye mata yi maza kije kiran innarki kinji." Daga kai Hibbah tayi tace "to." Ta fice a gidan.
Gidansu ta nufa tana shiga taga inna lami tare da aminiyarta inna delu suna hira harda shewa, wani yawu ta had'i kut, zuciyarta ta fara bugawa tasan tunda taga inna delu a gidan to wata muguntar ta had'a.
A hankali ta k'arasa cikin gidan da sallama babu Wanda ya amsa mata saima mugun kallon da innar ta bita dashi tare da cewa "kefa a taki k'aramar k'wak'walwar kinyi tunanin na dawo dake gidan nan ne KO?"ta Saki wata dariya suka tafa da delu ta cigaba"ni Neman kud'i zanyi dake don haka ki tashi kije ki had'o tsummokaranki kizo zaku tafi da delu." Da sauri Hibbah ta d'ago kanta tace "ina inna?" "Gidan ubanki nace gidan ubanki kujimin yarinya da rashin kunya dole sakinji KO ina ne, ki tashi ki hada kayanki nace, kuma wallahi saura idan ankaiki kice zaki zo ganin gida wallahi saina kasheki kinsan halina sarai Zan iya kasheki." Jikin Hibbah na rawa ta tashi ta shiga d'akinsu kayanta tashiga had'awa hawaye na sintiri a fuskarta cikin ranta take tunanin wannan *RAYUWA* tata a raba ka da mafiyarka da mahaifinka yanxu kuma zaa rabaka da danginka da kowa naka akaika can wani waje kayi *RAYUWA* ba tare da kasan kowaba acan. Wani hawayen ya kuma gangaro mata
Ta share da bayan hannunta ta karasa had'a kayan nata da basu fi kala biyar ba duk dun kod'e ta k'ulle a d'an kwali ta fito, taje gaban inna ta tsugunna tace "inna na had'a kayan." Inna ta watsa mata harara "kindai ji abinda nace kika kuskura kika dawo k'auyen nan saina kashe ki wallahi tashi ku tafi," hawaye ne yake gangarowa daga idonta tasa hannu tana sharewa amma duk da haka bai daina zuba ba. Rank'washi inna ta Kai mata aka tace "kujimin da munafukar yarinya annamimiya uwarki nayi miki daza ki Sani a gaba kina yimin kuka? Uban me nayi miki? Daza ki daina arhar hawayenki ma daya fi miki don wallahi, kinji na rantse babu Wanda ya isa ya hanani kaiki aikatau birni, shegiya mai bak'in hali." Ta fad'a tana kuma kwad'eta. Kuka ta kuma Saki harda magina ta kalli inna delu wadda sai murmushi take kana gani kasan na mugunta ne tace "meye kike kallona da wad'annan mayun idanun naki mayya kawai, ni tashi dallah mu tafi kina b'ata min lokaci ina da wajen zuwa da yawa." Cikin shashshek'ar kuka Hibbah ta kallesu tace "inna dan Allah kuyi min hakuri ku barni a cikin 'yan uwana da dangina, karku rabani da mahaifata don Allah wallahi bana so.........." Wani wawan mari inna t Kai mata "don ubanki har kina da bakin magana, ki kalli tsabar idona kice wai na barki cikin danginki? Ina kike da dangin? Shegiyar yarinya zatayi min bak'in ciki tun wuri gara ki fidda ran zaki kuma *RAYUWA* cikin danginki har abada!" Sun kuyar dakai Hibbah tayi tana kuka sosai.
Inna delu ta mike tace "keh! Tashi mu tafi," ta kalli aminiyar tata tace "to lami zamu huce sai kuma na kawo miki albashin nata kuma duk wani alheri da aka bata a gidan naki ne." Cikin happy lami take washe baki tace "to shikenan sai na jiki allah ya kiyaye hanya, ke kuma" ta nuna Hibbah "kindai ji abinda na fada miki kika kuskura kika dawo k'auyen nan kinji dai furucina tam," mikewa Hibbah tayi tana share hawayen dayake tayi Mata sintiri ta kalli katangar su Abu ta tuno nan ne kad'ai yanxu ya ragemata kuma gashi suma an rabata dasu, Dama a dangin babanta bata san kowa. Abu ta hango tana lek'o gidan, kallonta ta tsayayi kafin ta d'auki k'ullin kayanta tabi bayan inna delu. Har bakin zaure inna lami ta rako su suna shirin fita daga gidan saiga su Abu da gwaggo sun shigo.
Gwaggo ta kalli Hibbah tace "ina kuma zaki da kaya haka?" Daga gefe inna lami tace "aikatau zan kaita birni saboda ni na maidata tamkar jari ne, Neman kud'i zata je tayi a dinga aikomin kuma na fad'a mata karta kuskura ta waiwayi k'ayen nan koda wasa eyyeh." Kallonta gwaggo tayi cikin mamaki tace "tabbas Abu maganarki ta tabbata, yanxu lami bakya gudun yarinyar nan ta fad'a mugun hannu ko kuma su gidan a ka kaita su koreta ina zata dosa wata Sani acan? Da zakice karta kuskura ta waiwayi mahaifarta?" Inna lami cikin rashin kula tace "oho ita ta sani ni KO karuwanci zatayi taje tayi nidai kawai ta kawo min kud'i. Ai ita 'yar kishiya jarice baka saurin illata ta nima sai yanxu naga kuskurena na korarta danayi jiya shiyasa nace Rahmatu ta kirata." Harara Abu ta bugawa lami tace "to wallahi babu inda zata saboda ba 'yarki bace shine zakice zaki wani turata aikatau, ai kema kina da 'ya macen ki turata mana." Cikin masifa inna tace "keh Abu ki shiga hankalinki ko wannan kakar taki bata isa ta hanani Kai Hibbah aikatau ba balle wata ke 'yar ciki dallah kauce min da gani." Gwaggo tace "ke Abu babu ruwanki Karna k'ara jin bakiki," ta kalli inna "lami don allah badon ni ba kiyi hakuri karki tura yarinyarnan aikatau, kodan gudun b'acin tarbiyyarta........." "Wallahi Zulai babu Wanda ya isa ya hanani aikata birni," cikin tsantsar masifa lami ta katse gwaggo.
Ba Hibbah da Abu ba harta gwaggo tayi mamakin yarda inna ta fadi sunanta kai tsaye batare data sakaya ba. Da mamaki gwaggo tace "lami zulai kai tsaye ba sakayawa?" Da masifa tace "to ba sunanki bane koba sunanki Zulai ba?" Girgiza kai gwaggo tayi tace "lallai lami," Hibbah ce ta k'araso kusa da gwaggo tace "gwaggo kiyi hakuri nasan ni haka tawa k'addarar *RAYUWA*r take na karb'eta hannu bibbiyu, Zan tafi aikatau birni na bar dangina, gwaggo ki kwantar da hankalinki nasan kina tsoron kar tarbiyata ta lalace ne. Insha Allah babu abinda zai canzani kedai kiyi tayi min addu'a nima inanan Zan cigaba dayi." Gwaggo taji dad'in kalaman Hibbah sosai cikin dauriya tace "to shikenan Hibbah allah ya miki albarka," Hibbah tana kallon Abu tace "ameen gwaggo," lami tace "mukuma allah ya tsine mana koh?" Babu Wanda ya kulata, Hibbah tace "Abu zan tafi nasan ni daku mun rabu har abada kiyafe min 'yar uwata kinji." Abu batasan danda hawaye ya zubo Mata ba tace "baki yimin komi ba Hibbah ni ya kamata na nemi yafiyar ki," cikin shashshekar kuka Hibbah tace "nima bakimin komi ba Abu." Suka had'a Kai suna kuka lamarin dayasa gwaggo itama hawaye.
Kallonsu inna lami da delu sukayi suka tabe baki delu tace "gaskiya lami lokaci na tafiya fa." Da zafin nama ta fincike Hibbah daga jikin Abu tace"dallah ki huce ku tafi."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.