Complete Hausa Novels

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 50 of 51

Satin Hibbah biyu a gidan Faheem har ta ware duk wannan kunyar tashi ta sauketa ta tsaya tana kula da mijinta yadda ya kamata. Shi kuwa Faheem kamar ba shiba yadda yake yiwa Hibbah wani lokacin har kunya take ji, daidai misali yana k'ok'ari wajen kwatanta adalci a tsakaninsu.
Faheem ya had'e Kausar da Hibbah a gida d'aya sakamakon Daddy ya kirashi yace ya had'e matansa waje d'aya don su kuma shak'uwa a matsayinsu na *jini d'aya*. Had'e sun da yayi sai suka kuma shak'uwa sosai Hibbah tama fi son haka saboda kullum tana tare da Nawaz d'inta, ita ma Kausar taji dad'i amma wani lokacin sai ta shiga d'aki tayi ta kuka tana da ta sanin rashin kula da mijinta da tayi aikinta kuwa tuni ta rubuta takardar ajiye aiki.

*3 month later*

Hibbah na gaban dressing mirror tana k'ok'arin sanya wani pink ashoke da aka nad'a Mata shi ta gama kwalliya sanye take cikin wani material mai shegen kyau gashi yayi mata matuk'ar kyau. Faheem dake jikin k'ofar d'akin ya zuba mata idanu yana kuma jin k'aunarta na ratsa duk ilahirin jikinsa ya k'araso gaban mirror ya karb'i ashoken ya saka mata da kanshi sannan ya juyo da ita "Masha Allah my hrt desire kinyi kyau sosai Anya kuwa zan barki kije wajen dinner d'in nan kuwa" Hibbah ta marairaice fuska "my boo kar muyi haka dakai Dan Allah ka barni naje, bikin Saudat da Safiyya ace banje dinner ba" ya girgixa kai "a'a my hrt desire kiyi zamanki kawai zansa a d'auko miki duk abinda aka gabatar a wajen" Faheem baiyi aune ba sai ganin hawaye yayi a fuskar Hibbah cikin kuka tace "Dan Allah my boo ni zan iya ma wanke kwalliyar Allah, kuma fa kace zaka dinga kaini kullum wajen bikin tunda kace bazanje na kwana ba" da sauri ya janyota jikinsa yana rarrashinta "ai zaki b'ata kwalliyar wasa nake miki" ya shafi cikinta "anya yarinyar nan ba ajiyata a jikinki kuwa naga fa sai wani haske kike yi kuma na Lura yanzu kina yawan ka sala, kwama biyun nan dana kusanceki fa naji kin canza" Hibbah ta rufe ido cike da kunya don itama ta lura da hakan kuma watanta biyu kenan bata ga al'adarta ba ga yawan tashin zuciya ga kasala amma sai ta dangana hakan da kawai janjin yanayi ne wai don da tana budurwa ne yanzu kuma tana da miji.
Ta karyar da kai "my boo ni bani da komai fa" "a'a gobe zamuje Dr ya duba min ke don ni ban yarda ba akwai ciki a jikinki" ya fad'a yana shafa cikinta. Hibbah ta ja hannunsa "mu tafi lokaci na k'urewa fa"
Haka suka wuce wajen dinner d'in su biyu don Kausar tana can ita da Nawaz, wajen ya k'ayato wuta a wajen kamar rana sai sautin kid'a dake tashi a wajen. Faheem ya samu waje yayi parking ya kai hannunsa kan cikinta yana dubanta yace "ni zan koma idan anjima zan dawo na d'auke ki, ki kularmin da ajiyata" ta kawar da kanta gefe "babban Yaya baza ka zauna a wajen ba" "a'a ai Ku kun wakilce ni" Hibbah ta bud'e k'ofar zata fita "to saina kazo" ya janyota "a hakan zaki fita baki bani sak'ona ba" tayi murmushi tare da yi masa Kiss a kan leb'ensa sannan sukayi sallama.

Ta k'arasa cikin wajen lokacin ma amaren basu zo ba, wajen su Aunty ta nufa suka shiga gaggaisawa sannan suka zauna ana ta hira Aunty itama da cikinta. Sai can mc yake sanarwar amare da angwayensu zasu shigo amare da angwaye sunyi kyau matuk'a sun kuma dace da juna, Hibbah da aunty suka tashi suna yiwa amare lik'i har suka k'araso wajen da aka tanadar dominsu suka zauna aka shiga hotona kafin kuma a shiga kad'e kad'e. Aka buk'aci angwaye da amare su fito filin rawa bayan sun fito Hibbah ta tashi ta shiga yi musu lik'i tana d'an rausayawa a hankali, hakan da takeyi sai ya janyo hankulan wasu samari abokanan ango su uku, d'aya a cikinsu yace "Salis kunga wataj had'addiyar baby da idanuna suka hango?" Dayan yace "ai ni tun shigowarta na ganta yanzu ma zanje na sameta" dayan da baice komai ba yace "ai ku naku wasa ba'a sanya a irin wannan bash Ku tashi muje" suka mik'e suka nufi filin rawar suka shiga yiwa Hibbah lik'i.
Faheem dake tsaye yana kallonsu ranshi a mugun b'ace ya nufi cikin gilin rawar, Hibbah tana hangoshi gabanta ya shiga fad'uwa don ganin yanayinsa gaba d'aya ya sauya. Yana zuwa ya d'auketa tamkar jaririya yayi waje da ita, waje kuwa ya d'auki ihu ana ta tafi wai babban yaya yana koyawa amare yadda za suyi soyayya, Kausar kuwa wani Abu ne ya tsaya mata a rai tama kasa cewa komai a hankali hawaye ya shiga mata sintiri.
Mota Faheem ya bud'e yasata sannan ya kunna motar suka nufi gida bai ce Mata komai ba har suka isa gida itama bata yi magana ba don a tsorace take.
Yana gama parking ya bud'e ya fita tare da banko k'ofar, da sauri itama ta fito ta biyo bayansa a parlor ta iskashi yana zaune ya d'aga kansa sama.
Ta k'araso ta tsugunna a gabansa "don Allah my boo kayi hakuri wallahi ni bansansu ba banma san suna min liki ba" ya dubeta yama kasa magana kawai ya kawar da kansa gefe Hibbah ta kuma matsoshi jikinsu na gogar juna tace "my boo kayi hakuri Dan Allah......" Sai kuma tasa kuka hawayenta na d'iga a k'afafunsa.
Ya d'ago da sauri ya d'orata kan cinyarsa yana goge hawayen fuskarta "my hrt desire kinsan ina da kishi akan iyalina amma kika shiga filin rawa a gaban gartin maza kina rawa har wasu suna hiran zasu sameki ku daidaita" ta shafo wuyansa ta baya tare da had'a bakinsu don tasan haka ne kawai zai sanyaya masa zuciya hot kiss take masa cikin k'warewa sun jima a haka don har Faheem ya fara fita hayyacinsa, sannan ta zame bakinta daga nasa "kayi hakuri Dan......" Bata k'arasa ba ya d'auketa ya nufi d'aki da ita don ya kasa jurewa.

*6 years later*

"Asra baza kizo mu tafi ba zamu tafi mu barki fa" Nawaz dake tsaye a bakin k'ofar d'akinsu Asra d'in, yanzu yana da shekara 12 kenan sanye yake da wata shadda anyi masa d'inki irin na samari sai zuba k'amshi yake.
Wadda ya Kira da Asra d'in ta fito yarinyace da bazata wuce shekaru biyar ba daka ganta kaga Hibbah don tsananin kamannin da suke da juna sanye take cikin wata riga mai hannun vest da wando jeans kanta anyi mata wata kalba mai shegen kyau an zubo mata dashi ta k'araso kusa da Nawaz d'in, cikin 'yar muryarta irinta Hibbah tace "kayi hakuri Ya Nawaz naje d'aukowa Uncle sweet din da Daddy ya siyo min jiya ne saboda bani da abinda zan bashi idan ya dawo" ta k'arashe maganar tana marairaicewa kamar zatayi kuka.
Nawaz ya janyo hannunta "to sarkin 'yan kuka tawo mu tafi su momy suna jiranmu a mota" suka k'araso Asra ta nufi gaban mota don ita take zama anan don ko wani ya shiga sai ya fito bazai zauna ba. Faheem ya dube su "Nawaz me kuka zauna yi ne a ciki?" "Daddy Asra ce ta tsayar damu" Faheem ya kalli Asra "me kika zauna yi a ciki ne Mamana? (Sunan momy ne da ita Zainab)" ta d'an had'a rai "Daddy ni ka daina cemin Mamana kace min Asra yafi dad'i" yayi murmushi don yasan bata son sunan yace "to Asra baby" tayi dariya "yeeh daddy sunan yayi dad'i" ta dubi Hibbah "Aunty mama bani Asrar na rik'e shi dan Allah" Nawaz yace "a'a salon kawai ki muntsine shi anki a baki d'in" Asra ta juyo ta harareshi "to ina ruwanka Daddy ka Ganshi ko?" Faheem ya kalli Nawaz "a'a Nawaz babu ruwanka, ke kuma Asra bana hanaki yi masa rashin kunya ba oya tell him sorry" ya fad'a yana kallon Asra data turo baki tace "sorry" faheem ya kalleta haka ake bada hakuri?" Ta juyo ta kalli Nawaz tare da had'e hannayenta waje guda "am so sorry I won't repeat it"
Faheem ya kunna motar suka nufi gidan Daddy, yana gama parking Asra ta bud'e k'ofar ta fito da gudu ta nufi cikin gidan tana kiran uncle Faheem ya girgiza kai su Hibbah suka fito Kausar tana rik'e da Asrar suka shiga cikin gidan.
Tana shiga ta d'ane jikin Faruq, ya d'agata sama yana "oyoyo my Asra ina Nawaz?" Tace "yana mota yanzu zasu shigo dasu Daddy" ya sauke ta ta mik'a masa sweet d'in dake hannunta "happy birthday uncle" "Tnx my Asra wannan ne gift d'in nawa kenan to na gode" tayi murmushi "mention not uncle you deserve more" ta fad'a tana hawa saman momy tana kiran k'walawa Saida 'yar wajen Aunty don sa'anni ne.
Su faheem suka shigo suka gaisa Faruq ya karb'i Asrar yana masa wasa sai k'yak'yata dariya yake Faruq ya kasa duban Hibbah don har yanzu kunyarta yake ji duk da tun wancan satin daya dawo ya nemi yafiyarsa kuma ta yafe masa amma har yanzu yana daya sanin abinda ya aikata a baya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.