Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 3 of 51
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: ๐๐๐๐๐๐๐๐๐
*RAYUWA* page6โฃto7โฃ
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
๐๐๐๐๐๐๐๐๐
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
*ุงููู ุงูุจุฑ ุงููู ุงูุจุฑ ุงููู ุงูุจุฑ*
*ูุงุงูู ุงูุง ุงูููุ ุงููู ุงูุจุฑ ุงููู ุงูุจุฑ ูููู ุงูุญู
ุฏ*
*ุงููู ุงูุจุฑ ูุจูุฑุง*
*ูุงูุญู
ุฏ ููู ูุซูุฑุง*
*ู ุตุจุญุงู ุงููู ุจูุฑุฉ ู ุงุณููุง*
_*Ina bawa mabiya littafin RAYUWA hakuri kasancewar yau zan dakata da yin typing sai bayan sallah idan Allah ya kaimu zan dora, allah yasa muyi sallah lafiya mugama lafiya.*_
_*Au na manta da sakon Aunty na ban fada muku ba, Aunty AYSHA ALIYU GARKUWA tace bayan sallaha karku manta ku tawo mata da nata naman๐.*_
Haka Hibbah ta yini tana kuka da tunanin yarda zata cigaba da *RAYUWA* a gidannan cikin wahala da ukuba. Sallah ce kawai ta tasheta daga inda take, alwala tayi tai sallar azahar sannan tayi la'asar kasancewar taji anata kiraye kirayen sallah bayan ta idar ta zauna ta rika kwararo addu'a tana kaiwa mai sama kukanta, addu'a take yi amma hawaye na zuba a idanunta. KO abinci ranar bata iya ci ba saboda tsantsar damuwar dake damunta na rabata da mahaifiyarta gatanta da akayi.
Umma kuwa suna zuwa gida Yaya Habu ya fadawa su gwaggo komi, sun firgita kwarai dajin kazafin da akayiwa 'yar tasu, ko kadan saki bai daga musu hankali ba saboda sunsan yanayin halin da 'yar tasu take ciki a gidan mijin nata. Kuma sun goyi bayan Yaya Habu daya tafi da ita cen Bunkure din zatafi samun nutsuwa sannan data gama iddarta idan Allah ya kawo miji tayi aurenta. Nan sukayi musu sallama suka huce.
Da daddare bayan sallar isha'i Hibbah na kwance a dakin ummanta zazzabi ya rufeta sai rawar dari take yi. Rahmatu ce tashigo dakin tana cewa "ke Hibbah kije sale driver na kiranki, cikin rawar baki Hibbah tace "Dan allah Rahmatu anso masa canjinsa wajen Inna, zazzabi ya rufeni bazan iya tashi ba." Harararta Rahmatu tayi "lallai ma ni zaki aika? Shima din abinda yasa kika nazo kudi ya bani amma badan haka ba babu inda zani, mtwss" ta karasa maganar dayin tsaki tayi ficewarta.
Tana fita dakin Inna ta shiga tana shan rake bako sallama ta haye kan gadon innar ta cigaba da shan rakenta, inna ta kalleta tace "me sunan baba me kike shane haka?" Shiru Rahmatu tayi bata amsa ba ta cigaba da shan raken. Inna ta kalleta tace "au saboda kar nace ki sammin shiyasa kikayi min shiru koh Rahmatu?" Cikin gajiyawa da maganar Rahmatu tace "ai dama nasan sai kince na sammiki bayan kuma kena fara cewa ki bani kudi na siya kika hanani" ta fada tana kuma gyara zamanta akan gadon innar.
Cikin yanayin lallashi Inna tace "haba me sunan baba ai ina baki kina siya, ki sammin kadan zansha." Turo baki Rahmatu tayi tare da mika mata tace "to gashi nan karki sha min dayawa, inkika sha da yawa allah saikin sai min wani," inna ta amsa tana cewa "bazan ma sha da yawa ba." Bantara tayi tasha zata kara, Rahmatu tayi saurin cewa "wallahi inna kika Kara saikin sai min sabo" mika mata inna tayi tana cewa "ai raken nakine akwai zaki, wa ya baki kudi kika siya?" Bata kalli inna ba tace "Sale direba ne yazo wajen Hibbah, shine zan shigo ya ganni yace na kira masa ita nace bazani ba shine ya dauko hamsin ya bani." Inna ta gyara zama tace "wai mene a tsakanin su ne dazuma kince ya bata Dari biyar a kasuwa, don ya barar mata da abinci kuma nidai nasan abincin dana dora mata na dari uku ne. Kinga kudin ma data zo tana ta uwarta bata ma yimin bayani ba ta bani kudin duka." Rahmatu tace "toni ina Zan Sani ni dai nasan kawai yana yawan kulata ko kuma yace zai tabata ita kuma ta haushi da masifa." Tana gama fadin haka ta mike tare da cewa "ni na tafi dandali" inna tace "sai kin dawo amma kafin ki tafi ki shiga ki kira min wannan shegiyar yarinyar tana nufin dan uwarta tabar gidan shine yau bazata fitar min da gyadata ba." "Inna tana can bata da lafiya" Rahmatu ta bawa inna amsa tana fita daga dakin. Murmushin mugunta inna tayi tare da bin bayan Rahmatu.
Shi kuwa sale ganin Hibbah bata fito ba yasa ya zauna zaman jira don yasan dole zata fito da gyada. Yana nan zaune yaga Rahmatu ta fito ya kalleta yace "Rahmatu ina Hibbah din?" Kallon shi tayi adan wulakance tace "tana ciki wai bata da lafiya" tana fadin haka tayi gaba. Shiru yayi yana nazarin koya shiga cikin gidan, yana kuma tsoran kar a kamashi don yasha alwashin yau dinnan saiya dan dani zumar Hibbah.
Inna ce ta katseshi da cewa "sale Kaine a kofar gidan namu?" Dan sosa keya yayi ya shiga gaishe da inna tare da cewa "nazo karbar canjina ne a wajen Hibbah na dazu dana bar mata". Inna jin anyi batun canji yasata murtuke fuska ta fara masifa "wane irin canji kuma?" Dan sunkuyar dakai sale yayi tunda yasan shi yake nema yace "eh dama dazune na zubar mata da abinci a kasuwa kuma na bata Dari biyar babu canji shine nace zanzo Na amsa." Dariya inna tasa harda tafa hannu tace "hmm yaro man kaza sale mene na boye min ni mai taimaka maka ne ka samu abinda kake so a wajen Hibbah, nasan komai kuma Zan taimaka maka ka samu Hibbah a Daren nan ma idan kana so amma da sharadi." Wani irin happy ne ya rufe sale cikin sauri yace "wane sharadi ne xan bishi matukar zan sami Hibbah" dariya inna ta kumayi tace "sai naji dumus a hannu" ba musu sale ya dauko 'yan dari bibbiyu ya irga guda shida ya bawa inna, inna ta amsa ta irga wani kallo ta bugamai tace "dubu daya da dari biyu ne fa kana tunanin wannan yakai darajar abinda zaka samu?" Cikin sauri ya kuma irgo guda hudu ya mika mata. Karba tayi tana ganin hudune cikin zafin nama ta warce sauran na hannunshi ta hada. Tace "kazauna anan idan kaga malam ya shigo sai kabi bayansa zakaga wani karamin daki dayake kallon dakin dazai shiga amma yayi nisa sosai da wanda zai shiga to tana ciki saika shiga." Sale cikin happy yace "to amma ummanta fa?" "Ummanta bata gidan" tana kaiwa nan tayi shigewarta cikin gidan cike da murna.
Ya kalli Hibbah yana dariyar keta, ita kuwa mugun tsoro ya bata cikin Sauri ta tashi zaune tana ja da baya. Binta ya shigayi shima, mikewa tayi dakyar ta shiga yin baya batason tazo bakin gadon ba sai ji kawai tayi ta fada kan gadon. Murmushin mugunta sale yayi yace "kin rage min aiki." Hawaye ne ya fara sintiri a fuskarta tana yin baya har taje karshen gadon. Hayowa gadon yayi yana murmushi, cikin kuka tace "don allah sale kayi hakuri karka rabani da muyuncina darajata don allah ka kyale...." Dariya yasa yace "wallahi Hibbah yau ba mai hanani kusantarki garama ki nutsu mubi komi a hankali idan ba haka ba kuma zanyi ta karfi Wanda ni zanfi son hakan." Kifa kanta tayi a tsakanin cinyoyinta tana karanto kowacce addua tazo bakinta.
Kayan jikinsa ya cire ya wurgar daga shi sai trouser ya tunka rota............
*by*
*MAMYN NAJMAH*
[10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: ๐๐๐๐๐๐๐๐๐
*RAYUWA* page 4โฃto5โฃ
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
๐๐๐๐๐๐๐๐๐
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
*ุงููู ุงูุจุฑ ุงููู ุงูุจุฑ ุงููู ุงูุจุฑ*
*ูุง ุงูู ุงูููุ ุงููู ุงูุจุฑ ุงููู ุงูุจุฑ ู ููู ุงูุญู
ุฏ*
*ุงููู ุงูุจุฑ ูุจูุฑุง*
*ูุงูุญู
ุฏ ููู ูุซูุฑุง*
*ู ุตุจุญุงู ุงููู ุจูุฑุฉ ู ุงุณููุง*
Sukayi tafiyarsu suna hira Hibbah tace "Abu wallahi akwai wani abu da yake bani mamaki da tsoro" kallon mamaki Abu tayi mata tace "wane abune wannan Hibbah?." Numfashi Hibbah ta danja tace "Abu kusan kullum sai nayi wani mummunan mafarki, wai Inna tasa baba ya kori umma daga gidan ni kuma ta biyoni da gudu da wuka a hannunta zata kasheni, sai wani balarabe Wanda ban taba ganinsa ba ya kwaceni a wajenta. Ita kuma ya jefata cikin wani katon rami me dubu idan ya jefata sai naga baba yaxo ya rumgume ni yana cewa na yafe masa" ta karasa maganar cikin tsananin damuwa. Abu tadanyi shiru tana nazarin kalaman Hibbah kafin tace "idan har hakan zai kasance gaske toda munfi kowa murna, mafarkin ki yana nuna nan gaba wani zai taimakeki ya ceto baba daga sharrin Inna. Amma abinda bangane ba shine korar umma da kikace Inna tayi daga gidanku." Cikin damuwa Hibbah tace "Abu nima abinda nake ta tsoro da wannan mafarkin da nakeyi kenan kar fa ya kasance gaskiya." "In allah ya yarda bazai kasance gaskiya ba, Umma tasan kina wannan mafarkin?" Abu ta tambaye ta, girgiza kai tayi tare da cewa "a'a bata sani ba" Abu tace "yakamata ki fada mata wata kila ita ta fimu fahimtar mafarkin naki" "hakane idan na koma zan fada mata" Hibbah ta fada.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.