Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 51
Aunty Aysha ta tausayawa Hibbah ta kalleta da hawaye a fuskarta tace "Hibbah insha Allah daga yau kinbar kuncin *RAYUWA*, kuma ba wani namiji dazai keta miki haddi na kyaleshi koda kuwa Faruq d'in ne wallahi sainayi Shari'a dashi. Kema yanxu kinzama 'yantacciya don na d'aukeki tamkar su Safiyya" Hibbah taji dad'in kalaman Aunty Aysha cikin happy ta rumgume ta tana godiya, Aunty Aysha tace "ke 'yar uwata ce Hibbah munzama jini d'aya ni dake" cikata Hibbah tayi tana murmushi, Aunty Aysha tace "tashi kisa kayanki." Mikewa Hibbah tayi ta jawo k'ullin kayanta ta d'auko wata kod'add'iyar atampa zatasa Aunty Aysha tace "baki da wasu kayan ne Hibbah wannan ai sun lalace," kasa Hibbah tayi da kai tace "Aunty Aysha duk cikin kayana wannan ne masu kyau." Tashi aunty Aysha tayi tace "jirani ina zuwa."
Sama Aunty Aysha ta hau ta nufi d'akinta ta d'auko wasu kaya dasukayi mata kad'an ta had'a zata bayar, ta dawo d'akin su Hibbah ta bata tare da cewa "gwada su mu gani," wani baby pink material ta bata ta gwada ai kuwa sai gashi skirt d'in yayi mata rigar take k'okarin sawa Aunty Aysha tace "Hibbah ina bra kuma a haka zakisa rigar?" Rufe fuska Hibbah tayi tace "bani fa da ita Aunty." Dariya Aunty Aysha tasa ta kuma fit.............
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page2⃣1⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.W.A
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
D'akinta ta kuma komawa ta d'auko mata bra ta Nuna mata yarda zatayi amfani dashi sannan ta bata waje ta saka, tana fita Hibbah tasa kayan saiga Hibbah ta dawo kamar ba ita ba. Tana gama saka kayan ta taje gashinta da kum d'in kan dressing mirror ta cureshi waje d'aya kamar yadda ta Saba ta daura d'ankwalin kayan ta tsaya a gaban dressing mirror tana k'arewa kanta kallo gani take kamar ba ita bace. Ita kuwa Aunty Aysha tana fita ta nufi bedroom d'in momy, da sallama ta shiga, momy ta amsa mata zama tayi kusa da momy tayi shiru ta rasa ta inda zata Fara, littafin da momy take karantawa momy'n ta ajiye ta kalli 'yar tata tace "Aysha fad'a min me kike so?" Da d'an mamaki Aunty Aysha tace "momy ya akai kika gano abinda ke tafe dani?" Murmushi mommy tayi tace "haba Aysha nifa uwace hak'k'i nane na fahimci duk wata matsalarku, kuma dukkannin ku idan kuna cikin matsala ina ganewa don haka meke damunki fadamin pls ina sauraron ki," kasa Aunty Aysha tayi da kanta tace "momy dama wata alfarma nakeso na rok'a a wajenki dan Allah," kallonta mommy tayi na fahimta tace "wace irin alfarma kenan Aysha?" Shiru Aunty Aysha tayi nad'an dak'ik'u kafin tace "momy akan wannan yarinyar Hibbah da aka kawo miki aiki yau," "to me kike so ayi mata?" Momy ta tambaya, Aunty tace "momy Dan allah so nake kisata a school both boko da islamiyya, na tausayawa yarinyar momy ta taso cikin k'iyayyar kishiyar uwa da kuma ta uba, ta rabata da uwarta yanzu mafa ita ta turota aikatau kuma ta gargad'e ta karta sake ta koma k'auyensu," momy cikin mamaki tace "kamar ya bangane ta rabata da mahaifiyarta ba, kince kuma ta taso da k'iyayyar mahaifinta, kiyimin bayani yadda zan fahimta" nan aunty ta fara bata labarin Hibbah kamar yadda Hibbah ta fad'a mata sannan ta d'ora da cewa "wallahi mommy yarinyar ta bani taudayi sosai, na tausayawa *RAYUWA*RTA shiyasa ma na d'aukarwa kaina alkawari kula da ita, najiyar da ita dadin *RAYUWA* koda ta hanyar bata ilimine momy pls ki taimaka min, ki bani k'arfin gwuiwa," momy tayi shiru tana jinjina hali irin na wasu matan komene ribarsu don sun sa uba ya tsani 'yarsa daya haifa? Mene amfanin ma bin bokaye da 'yan tsibbu? Ta kalli Aysha tace "bake kad'ai ba Aysha nima Zan bada gudun mawa wajen ceto yarinyar nan," d'ago Kai aunty tayi cikin happy ta kalli momy tace "da gaske momy?" D'aga mata Kai momy tayi itama tana murmushi. Aunty tace "na gode momy sosai allah ya k'ara girma da tsawon rai mai amfani," momy taji dad'in addu'arta tace "amin Aysha, in anjima idan malam Jamil yazo ki turata wajensa itama ya dinga yi mata lesson d'in kuma yaji izunta nawa, sannan bangaren boko kice masa ya Fara Mata daga faro," momy ta d'auko purse d'inta ta zaro dubu biyar ta mikawa Aunty Aysha tace "ga wannan idan yaxo ki Bashi kud'in nan yayi Mata komi harda uniform zai kawo mata, ita kuma makarantar bokon kinga yanxu suna hutu kuma kinga idan sun komai zasu shiga third term ne sannan kuma Hibbah tayi girma da primary, za'a barta har wannan term din ya k'are yana yi Mata lesson idan anshiga new session sai musan abinyi." Aunty Aysha shiru tayi tana mamakin momy bata tab'a tunanin haka ba batasan sanda rumgume momy ba tana ta zuba Mata addu'a mommy tace "abin alkhari be yin hakan Aysha, sannan ita delu tunda muguwace baza mu Nuna Mata muna kula da Hibbah, sannan zansa Hadiza ta samo min wata mai aikin tunda ita Hibbah karatu bazai barta tayi aikin ba inyaso ita ko da daddare ko a weekend ne idan aikin ya taso sai ta dinga yi." momy ta tashi daga kan gadon ta bud'e wardrobe ta d'auko wasu kaya daba'a d'inka ba atampa ce guda hud'u, leshi uku, materials kala biyar sai wasu abayoyi masu shegen kyau guda biyu ta ajiye a gaban Aunty tace "gashi ki kaiwa tailor'n Ku ya d'inka mata," ta kuma zaro wasu kud'in ta bata tace " ga wannan kisiya mata inner wears da kuma 'yan kayan kwalliya, da turaruka." Aunty Aysha cikin mamakin yawan kayan tace "momy dama kina da kayan daba'a d'inka ba ajiyayyu haka?" Momy tayi murmushi tace "a'a Aysha last week ne da hajiya Rukayya ta kawo min sune, ni kuma da kunya nace bazan amsa ba shine na amsa da ajiye," d'aga Kai aunty tayi alamar gamsuwa, nan aunty Aysha ta kuma yiwa momy godiya ta kwashi kayan ta sauko k'asa dakin su Hibbah Sam bata fad'awa momy abinda Faruq yayi ba.
Aunty Aysha ta shigo da kaya nik'i nik'i ta k'araso kusa da Hibbah ta zube kayan hannuta a kan katifa, ta juyo da Hibbah suna fuskantar juna tace "kai Hibbah kinyi kyau masha allah," hunnu biyu Hibbah tasa tan rufe fuska dashi tace "Kai Aunty na gode," aunty taja hannunta suka zauna a bakin katifa ta kalli Hibbah tace "albirishinrinki," Hibbah tana murmushi tace "goro Aunty." Aunty tayi murmushi tace "na fad'awa momy komai game da *RAYUWA*rki, tatausaya miki kuma tace zata taimakamiki," Hibbah cikin tsantsar happy tace "da gaske Aunty? Amma gaskiya na gode na gode Aunty allah ya k'ara girma da d'aukaka" Aunty tace "amin" ta zaro kudin da momy ta bata tareda janyo kayan tace "Hibbah wannan kud'in momy ta bayar tace a yi miki komai na makarantar islamiyya, akwai Wanda yake yiwa su Saudat lesson kema zaki dinga zuwa yanayi dake, makarantar boko kuma sai wata shekarar zaa kaiki, wannan kuma tace a siyo miki kaya kwalliya." Farin ciki ya hana Hibbah magana wai yau itace ta samu wannan gata har ta samu 'yancin yin karatu, katse mata tunani Aunty tayi da cewa "wannan kayan kuma badawa tayi tace a d'inka mikinsu," Hibbah cikin tsantsar happy ta shiga godiya sosai tacewa Aunty" don allah Aunty rakani wajen momy nayi mata godiya," aunty tace "to tashi muje," Hibbah ta mike suka bar d'akin.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.