Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 31 of 51
Da yamma ya samu ya fita don anyi masa waya ana nemansa, yana fita Jabeer yayo mata waya yana waje, nan ta shirya ta ja hannun Nawaz suka fita. Bayan sun gaisa Jabeer yace "Hibbah banji inda shawarar ku ta tsaya ba akan sa ranar nan, sauraronki nake yi na samu Aunty Aysha naji bakinku yazo d'aya itama tace wai zata tattauna da Umma, abinda yasa na dame ki ni mutum ne mai d'aukar abinda nake so da mahimmanci ban son shiririta a al'amurana, idan kina ganin abin bazai yiwu ba ki fad'a min gaskiya kawai kar ki b'oye min" tayi d'an murmushi "kasan ba nike da kaina ba kuma nayi maka bayanin komai bani zan aurar da kaina ba, amma ka samu Alhaji Ku tattauna kaji ta bakinsa," "to naji dad'in hakan, kar kiga zak'ewata ina sonki da yawa shi yasa nake nuna miki damuwata kuma nasan kema kina sona, zan sameshi in Allah ya yarda."
Faheem ya dawo ya huce su, Nawaz ya bishi don taryarshi, al'adarsa kenan komai yake yi da yaji motar Daddy'n shi ya dawo to saiya taro shi, Faheem ya saba mishi da hakan yakan ji dad'i aranshi sosai.
Tayi ajiyar zuciya Faheem mai sata cikin rud'ani in dai ta ganshi sai komai ya sauya mata in a parlor take ta gudu d'aki, in tana tafiya ne taji kamar anyi mata dabaibayi dole take tsayawa sai ya huce sannan ta cigaba, ya katse mata tunani "ina son mu gaisa da yayan nan namu amma naga kamar bai da son mu'amala da mutane, a k'alla ya sha wucemu anan yasan kuma ina zuwa wajenki ne don na aureki amma ko duban inda muke baya yi bare ko hannu ya d'aga min, ni kuma inason mu gaisa dashi ya sanni sosai don yasan shima yana da ruwa da tsaki a cikin maganar aurenki tunda a hannunsa kike zaune" "gaskiya ne kuma mutumin kirki ne, kawai dai allah ne bai nufa zaku gaisa d'in ba sannan na fahimci bai da wani ra'ayi akan shiga maganar aure na tunda bai tab'a yin magana akan hakan ba, amma nasan idan lokaci yayi zai yi."
Ya gyada kansa "shikenan Allah ya tabbatar da alkhari na gode" ya bata wani k'unshi a rufe a takarda. "Kai baka gajiya yau da gobe sai Allah," "Ana gajiya da masoyi ne?" Mutuminta ne ya huce su a mota, Faruq d'an rikicin duniya da da inda zata je data gudu sai ya tafi saita dawo domin zai sa ta a gaba ne kawai sai ya sata kuka.
Sukayi sallama ta shigo gida, ta huce shi a cikin motar kamar bata ganshi ba, ya dad'a k'uluwa kishi ke cinsa kamar masifa, wai wannan Jabeer da jaraba tsiya yake duk yadda ya tozarta Hibbah a gabansa bai hakuri ba.
Ya fito yana take mata baya ya janyo mayafinta ba shiri ta yo baya kamar zata fad'i ranta a b'axe ta kalleshi zallar masifa ta gani a idanunsa yau ta tab'o Faruq, mai cin zalinta a bulus bare da dalili. Ya nannad'e mayafin a hannusa tana ja ta kasa k'wacewa, ya kuwa murd'e hannunta ta rintse idanunta ji tayi kamar zai b'allata tayi wata 'yar k'ara "wayyo Allah na!" Abinda ta tsana kenan wannan rashin mutuncin da Faruq yake yi mata tana d'aukarsa tsabar tsana ce da rashin galihu. "Zan nuna miki mahaukacin kishi na akanshi zan iya komai tunda kika jawo mutumin nan duk da irin tozarcin da nayi miki a gabansa ashe tsugunno bata k'are ba, matuk'ar na k'ara ganinki dashi sai na miki rashin mutuncin da baki tab'a zato ba, don ji nayi kamar nasa bindiga na harbi k'ok'on kansa." Faheem ne ya fito yaji kuma furucin Faru$q sarai amma yayi kamar bai san su ba yayi wucewarsa, wani bak'in ciki taji ya k'ulleta kamar ta fad'i ta mutu wajen. Babu mutumin da a duniya bata son mutuncinta ya zube a wajensa kamar Faheem tana ganin girmansa, gashi a yau yaji ya gani hujja ce da zai d'ora zarginsa akan gaskiya tana mu'amala da Faruq bawai iyakar soyayya ba, wani tunanin zai yi don Faruq dai bashi da halin k'warai akan 'ya mace, gashi ya rik'e hannunta gam bata da wani sauran mutunci a idanun Faheem, wannan wace irin *RAYUWA* ce...............
*#JUMMA'AT MUBARAK TO YOU ALLπππ€*
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:25 PM] Maman Najma Author P1: πππππππππ
*RAYUWA* page3β£7β£
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
πππππππππ
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.W.A
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
Wani sambatun banza yake yi mata ta tureshi a fusace "Allah ya isa cin zalina da rashin mutuncin kake min, k'arewar tsana k'in jini ka kashe ni ka huta, babu mutumin da na tsana a duniya irin ka.........." Kuka ya shak'eta, maganar ta shige shi domin alwashin ya daina mata irin wannan abun amma why? Why yaji kishinta haka? Kishinta ne ya tursasashi don abinda yafi wannan ma zai iyayi sai dai duk abinda za'a yi masa ayi masa, ta shige gida, a cikin d'akin ta watsar da kayan ta kwanta kan gado gami da kifa kanta a kan pillow, ta gaji da wannan wulak'ancin da cin zarafin na Faruq wai me ta tsare masa ne a duniya? Burinsa ya sata kuka ya zubar mata da k'ima da daraja a idanun mutanen da suka d'auketa mai mutunci, to ina k'iyayyar da ta huce wannan ina zata kai k'ararsa ne don a k'watar mata 'yancinta.
Faruq ya shigo ya rufe k'ofar yana kallon ta, sai yaji wani haushin kansa kai zuciya bata yi ba, sai ta ingiza ka kayi abinda zaka zo kana shiga damuwa, sam baiji dad'in kalaman Hibbah ba duk ta rikitashi har yaji ya tsani kansa. "Hibbah" ya sunkuyo kanta, wani d'an tsaki yayi kukanta take yi, "oh my God! Wai Hibbah ya za muyi da juna?" Ya tsugunna nan ya d'ago kanta, fuskarta sharkaf da hawaye, ya maida kan nata kan filo tare da kifa nasa shima, "ni dai babu yadda zanyi da k'aunarki Hibbah tunda kince kin tsane ni to ko guba ce ki bani nasha na mutu na huta da wannan azabar sonki Hibbah, wallahi zan iya yi miki kuka a yau don ki tabbatar da ina k'aunarki ba tsanarki nayi ba, ki sani ni gwarzon namiji ne babu abinda zai iya sani kuka amma saboda ke nace zan iyayi haba masoyiyata Hibbah" zunbur ta matsa daga inda yake ta koma can k'ashen gadon "zo na rareasheki Hibbah baki san yadda nake ji a zuciyar nan tawa ba."
"Allah yayi min tsari dakai shad'anin mutum irin ka, kai ba masoyina bane babban mak'iyi nane Wanda yak'i jini na, burinka nayi kuka raina ya b'aci na rasa kwanciyar hankali, shikenan farin cikinka me na tare maka?" Ya daki pillow'n da hannunsa yana huci idanunsa sun kad'a, cikin wata irin murya yace "ni ne shad'anin mutum zan tabbatar miki da hakan yanzu." Yayi wata zabura zai rik'ota ta tashi da gudu tayi hanyar fita yayi saurin cafkota, jikinta ya d'auki rawa badon ya rik'ota ba da tabbas zata iya fad'uwa saboda tsabar tsoro da fargabar mai zai faru, ya tsura mata idanu yadda yake ji a zuciyarsa yasan Hibbah ta kaishi k'arshe, so jarraba ne baya jin zai iya yi mata komai amma badon haka ba da yau saiya nuna mata shad'ancinsa.
Yayi murmushi "Hibbah ina sonki da yawa furucinki ya fusata ni, fushina akwai wahala don bani da dad'i komai aka yi min saina rama, haka nake sai dai idan ni nayi niyyar yafiya ke kad'aice mace ta farko data sauya akalar ra'ayi na, kin ganni kamar tab'ab'b'e dubeni" saita bi umarninsa, don a cikin tsoro take, suka k'urawa juna ido. Sai yayi dariya ya ja hannunta suka koma parlor suka zauna ya shiga goge mata hawayenta "kin yave min? Wallahi nayi miki alkawarin bazan kuma b'ata miki rai ba, sai dai idan abisa kuskure na aikata, yanzu me kike son nayi miki?"
Ta dube shi a nutse "Dan Allah karka sake kulani bare ka shiga harkata shikenan abinda nake son kayi min, kabar rayuwata ta huta abinda kayi min na yafe," "kina nufin baza ki aure ni ba?" Dam gabanta yayi wata mummunar fad'uwa zuciyarta ta shiga bugawa wai shi da gaske yake? "Aure fa kace Faruq kasan mene ma'anar aure? Taya aure zai k'ullu tsakanin mak'iya biyu? Ni fa abokiyar gaba ka d'auke ni, wace irin rayuwa zamuyi bayan nasan halayenka babu abinda ya sauya, ka kaga wuyanka sarka ce, kana nan akan batunka nason b'ata min *RAYUWA* saboda bani da galihu Allah ne gata ne."
Ga mamakinta sark'ar ya tsinke ya jefar "wallahi tunda bakya so daga yau nayi miki alk'wari na daina sakawa, bazan iya daina sonki ba Hibbah sonki zai iya kashe ni, ni ban iya son abu ba idan ina son abu ina sonshi ne da dukkan gaskiya ta ko da zan rasa raina, Hibbah da kin aure ni zan zubda duk wasu d'abi'u na da bakya so zan daina su" "to kai baka la'akari da matsayina ne da naka, ka manta ni 'yar aiki ce a gidan Ku, ka duba matsayinka na d'an masu kud'i ni kuma ba 'yar kowan kowa ba, ka shahara da farin jini a football ga farin jinin mata. Kaga wannan Jabeer d'in shine ya dace dani shine mai min soyayya tsakani da Allah, a gabandmsa ka tozartani da bayyana masa matsayina na 'yar aiki a gidanku, amma hakan bai hanashi k'aunata ba kuma idan Allah bai wulakanta ka ba babu mai tozartaka a duniya, a cewarsa koda yawo nake ina tsinyar abinda zanci, zai aure ni ballantana don ina aikatau a gidan ku ai ba sata nake ba ba maita ba, shine yasan darajata yake sona don Allah," idanunsa sun kusan rufewq saboda tsabar b'acin rai "kinsan yadda nake jin zafin maganganunki nan gara ki caka min wuka mai dafi, Hibbah ina ta fahimtar dake irin son da nake miki kin kasa fahimta ki daina tunanin matsayinki wai waye waye ni zan samu Ya Faheem na fad'a masa," ta waro ido waje "Daddy'n Nawaz ma fa yasan da batun Jabeer ya zanyi dashi kayi hakuri kawai," ya d'ora hannunta a kan k'irjinsa "Hibbah kiji yadda zuciyata bugawa idan kina min zancen wani zata iya bugawa ki kashe ni ki huta."
Ta zame hannunta "ni dai ka daina tab'ani ban so" "saboda ni kuturu ne ko, idan ban tab'aki ba wa kike son na tab'a kawai ki yi hakuri da halina duk abinda kike tunani yanzu kin huce haka a wajena, idan kuma nayi niyyar kusantarki sau nawa ina ritsaki a d'aki, kawai ni so nake kafin na tafi Germany a d'aura auren mu," ta tsorata da kalamansa ita gani take kamar Faruq baya hayyacinsa, ta tashi ya rigata yana dariya "nasan kina sona gulmace irin taku ta mata kina so kina kaiwa kasuwa, da munyi aure zan bud'e miki idanu na koya miki yadda zaki soni har ma kiji idan baki ganni ba na d'an wani lokaci ki kasa sukuni, dama wand'annan idanun na kuka ne abu kada'an kiyi ta kuka."
Tayi murmushi "kaji dashi dai ni aiki na zanje nayi," "muje na tayaki kinsan ni bana barin macen da nake so cikin damuwa ko yaya take shiyasa nake miki naci zaki ji dad'in rayuwarki dani" ta girgiza Kai "a'a na gode ka tafi kar Daddy'n Nawaz ya dawo" ya tab'e baki gami da yarfar da hannu "to meye a ciki, zan fad'a masa ma aurenki zanyi ai yasan komai tunda yana gani na tare da ke, kawai dai yana sharewa ne, ni bani number ki bazan iya barci ba sai naji muryarki" ta tsaya kawai tana kallonsa wai ita Faruq yake furtawa Kalmar so anya wannan ba salon yaudara bane, idan tayi la'akari da kalamansa na wannan jikin mallakinsa ne, jikinta kawai yake so ko da zai aureta daya gama cin muriyar jikinta zai yada ita ya koma har kokinsa da mata.
"Magana nake miki kin wani tsare ni da wannan idanun naki masu saukarwa da mutum kasala, idan kina kallona tsumani kike yi ina ji ina k'ara sonki, idan kika cigaba da kallona kema kinsan abinda zai faru," tayi dariya "Kai fitina ne da kai na gaji da fad'a maka bazan iya ba" "gara ma tun wuri ki sama mana mafita don karshen watan nan nake so a d'aura aure idan ba haka ba za'a haifi d'an da ba ido" ta shige d'aki ya bita da kallo gaskiya yarinyar nan ta tafi dashi da yawa, ga manyan babies nan a gari amma duk basu burgeshi ba sai Hibbah.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.