Complete Hausa Novels

Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 47 of 51

Ta fito suka tafi dandali Saudat tana ta yi mata mita suna ta fiya ita dai bata kulata ba don duk abinda Faheem yayi mata yak'i goguwa a kwanyarta da haka suka k'arasa dandalin Ana ta kad'ekad'e 'yammata suna ta rawa wasu kuma sunata zuba tad'i.
Suka k'arasa wajen suna ta kallon matan masu rawar, Saudat ta kalli Hibbah cikin tsokanar tata tace "Auntyna ke baza ki shiga kiyi rawar ba, da fa har dake ake yi ko?" Hibbah ta harareta bata ce komai ba, Saudat da Safiyya suka kwashe da dariya Saudat tace "kuma wad'annan k'olawan ne samarin Ku?" Saudat ta fad'a tana dariya har da rik'e ciki. Hibbah ta buga mata duka tana cewa "wallahi tashi mu tafi dama don kiyi min wulakanci ne yasa kika ce zaki zo ko?" Safiyya ita ma dariyar take tace "haba Aunty Hibbah ai ko da kina k'auyen nan kinfi k'arfin wad'an nan k'olawan" itama ta fad'a tana dariya, Hibbah ta tashi ta fara tafiya "idan kun gama dariyar ku same ni a gida" "ki tsaya mu mana Auntyna" Saudat ta fad'a cikin dariya banza Hibbah tayi dasu ta fara tafiya.
Ji tayi an dafata ta baya ance cikin yanayin mamaki "Hibbah dama zaki dawo k'auyen nan?" Da sauri Hibbah ta juyo jin muryar kharime tace "kharime" "na'am Hibbah yaushe kika zo?" Farin ciki ne ya lullub'e Hibbah tace "yau nazo kharime ina dije?" "Dije suna tare da salahu, Hibbah kinga yadda kikayi kyau kika koma 'yar gayu kamar dama a birni aka haife ki" Hibbah tayi Mata hararar wasa "kai kharime kin fiya tsokana" "Allah da gaske nake, kinsan Abu tayi aure kuwa?" Hibbah ta janyo hannunta suka zauna akan wani benci tace "eh gwaggo ta fad'a min ke yaushe ne naki?" "Ai idan zaki kai wani satin a garin nan to dake za'ayi" "da gaske?" Hibbah ta tambaye ta cike da zumud'i kharime tace "Allah kuwa"
Su Saudat suka k'araso suka gaisa da kharime, Hibbah an samu aminiya tuni suka zauna suna ta zuba hirar yaushe gamo, dije ce ta k'araso tana ta mita "wallahi kharime halinki saike gara ma ki canza hali gidan wani zaki" kharime ta kalleta tana dariya "Amaryar salahu me nayi kuma?" "Wato sai da kikayi yadda kikai kukayi magana da wad'annan 'yan birnin ko?" Dariya kharime ta kuma yi "Hibbah ce fa" "wace Hibbah karki raina min hankali mana" "Allah da gaske nake nima ta muryarta na ganeta" dije ta zubawa Hibbah ido lokaci d'aya kuma ta gane kamannin Hibbah, da sauri suka rumgume juna suka zauna Ana ta zuba hira.
Su Saudat kuwa zuba musu ido sukayi suna ta sauraron hirarsu, sun jima suna ta hira badon sun so ba haka suka hakura suka rabu akan gobe idan su Hibbah basu tafi ba zata zo su je gidan Abu.
Haka suka koma gida aka cigaba da hira kamar baza'a daina ba, ita kuwa Hibbah duk kunyar Faheem take ji shiyasa ma ta kasa sakewa a haka har dai suka yi bacci.

Inna lami kuwa sunkai wajen 3hours a ciki ita da boka kafin.............

*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*RAYUWA* page5⃣3⃣

*NA*
*MAMYN NAJMAH*

🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓

*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*

```watpad@mamyn_najmah2222```

Kafin su fito ya had'a musu wasu k'ullika ya bata "ga wannan ki barbad'a a wajen da kika tabbatar zata tsallaka daga yanzu da kika amsa karya awa d'aya baki yi amfani dashi ba sannan da kinje gida ki barbad'a tana tsallakewa da mintuna biyar ki share, karki karya k'a'ida ko guda d'aya idan aka samu matsala d'aya a cikin mu zai mutu ko ni na mutu ko ke ki mutu" babu ko d'ar a zuciyar Inna lami ta amsa suna k'ok'arin zube masa k'ud'i y katse su "wannan aikin naku yana da had'ari ku bari sai aiki yayi kyau sai ku kawo" nan suka tashi sukayi godiya suka tafi.
Suna tafiya suna ta hira a kan maganin da bokan ya basu, sunzo tsallaka wani d'an k'aramin titin da zai sadasu da k'auyen katsalle da yake titi guda d'aya ne sai ji kake k'uuuuuuuuuu wata k'atuwar dab tayi shoki da su delu ma'ana tayi sama dasu a take suka zube a wajen.

Can gidan kuwa ana kiraye kirayen sallah dukkanninsu suka tashi mazan suka nufi masallaci yayin da matan sukayi a gida bayan sun idar kuma suka shiga tattare gidan don Daddy yace yau zasu koma gida, suna shirin d'ora girki sai gashi gwaggo ta aiko musu da breakfast mai rai da lafiya. Nan suka amsa tare da godiya aka zauna aka nad'i girkin gwaggo bayan sun gama kuma sukayi wanka Ana ta shirin komawa birni.
Ita dai Hibbah bata so komawarsu ba taso zuwa gidan Abu kodan suka juna ta kuma fad'a mata abinda yake faruwa tasan abu zata tayata murna. Haka ba don tana so ba suka gama shiryawa suka nufi gidan gwaggo don d'aukota su tafi sannan su yiwa malam sallama, da suka je ma itama ta shirya suka kuma yiwa malam godiya suna shirin fita saiga Abu ta shigo ta gaishe dasu momy sannan ta rumgume Hibbah tana murnar ganinta ita ma Hibbah cikin d'auki da murna ta rumgume Abun, Abu tace "na tayaki murna Hibbah naji dad'in wannan al'amari ashe dama rabon kiga dangi ne ya kaiki birni" Hibbah ta kuma k'amk'ameta sai dai taji bata rumgume Abu sosai ba don wani abu ya tokare tsakaninsu Hibbah ta d'an saketa ta d'an matsar da ita daga jikinta tana son ganin mene abun da ya hanasu had'a jiki sosai. Ido Hibbah ta zaro da mamaki tana kallon Abu tayi k'asa da murya tace "Abu me nake gani ciki?" Abu ta d'an buge kafad'art "ni har kin bani tsoro wallahi ji nake wani abun ne, to cikin bashi bane ribar aure"
Hibbah ta rik'e baki tana mamaki wai Abu ceda ciki kenan itama dole ne ta k'unshi nata?" Ta girgiza Kai Anya kuwa zan iya? Abu ta dafata "tunanin me kike yi?" "Ba komai waya fad'a miki nazo garin nan?" Hibbah ta tambaye ta "Abban Amina ne ya fad'a min" kallon ta Hibbah tayi da mamaki "waye kuma Abban Amina?" Abu tace "au a shefa baki santa ba, 'yar da na Haifa ce ta rasu" "au wai kina nufin wannan cikin bashi ne na farko ba? Tab kina k'ok'ari" "k'ok'arin me?" "K'ok'arin d'aukar wannan cikin" dariya ma Hibbah ta Bawa Abu tace "kema zaki d'aukane" Saudat dake gefensu tana jin duk abinda suke cewa tace "tab har na hango Hibbah da k'aton ciki nan kina tafiya da k'yar" ta kuwa kwashe da dariya.
Hibbah ta harareta bata ce komai ba, Saudat ta cigaba "kinga dama Daddy yace nan da sati biyu zaki tare kinga kenan nan da wata tara zamu so suna" Abu ta kalli Hibbah da mamaki "au Hibbah kinyi aure kema?" Da Sauri ta katseta "k'arya fa take yi" Saudat tayi zaraf "wallahi da gaske nake sanadin auren ne ma yasa muka zo garin nan kuma ki tambayi su gwaggo" "na yarda ma wallahi, to ke Hibbah ai ba'a b'oye abin alkhari" ita dai Hibbah bata ce komai ba sai hararar Saudat da take yi.
Suna nan zaune sukaji sallama babban mutum ne wai baba yake nema, baba ya tashi ya fita abinda ya gani ne ya sashi juyowa gida da sauri ya shigo duk a hargitse kallon mamaki su Abba duk suke masa suna tambayar lafiya? Yama kasa magana waje kawai yake nuna musu ganin ya kasa magana yasa suka mik'e suka fita don ganin abinda ya rikita baba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.