Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 38 of 51
A sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta, Faheem ya kalleta "me Daddy yace miki?" Ta sauke ajiyar zuciya "Yaya Daddy yak'i saurarata yace muje yanzu yana nemanmu, na fad'a masa muna asibiti baka da lafiya yace k'arya ne idan bamu zo ba ranmu saiya b'aci" Faheem ya yunk'ura ya tashi zaune "kije ki Kira min Dr Umar yazo ya sallame mu muyi sauri muje," "a'a Yaya baka jin dad'i fa har yanzu ka bari ni naje ni kad'ai" ya kalleta "haba Aysha so kike na sab'awa su Daddy ne? Ai rashin lafiyata ba komai bace akan sab'a musun da zanyi don haka kiyi abinda nace ki Kira min Dr" ta kalleshi tana tausayawa Yayanta, lallai ba k'aramun so yake yiwa Hibbah ba a dalilinta ya samu ciwon zuciya, gashi kuma ya d'aukarwa kansa hukuncin barinta.
Ta mik'e da niyyar zuwa kiran Dr sai gashi ya shigo, suka gaisa ya shiga duba Faheem d'in bayan ya gama yayi 'yan rubuce rubucensa ya juya zai fita, Faheem yace "Dr inason ka sallameni yanzu pls" da mamaki sosai akan fuskar Dr Umar yace "saboda me? Kasan illar ciwon da kake tattare dashi kuwa? Kayi hakuri ka zauna a nan zaka fi samun kulawa" Faheem yad'an dubeshi "kayi hakuri Dr Daddy ne yanzu yayi min waya yana son ganina da gaggawa, pls ka taimaka ka sallameni yanzu karna sab'a umarninsa" Dr yayi shiru yana yaba biyayyar Faheem ga jyayensa "to shikenan Aysha biyoni office"
Ya fita Aunty tabi bayansa suka je office ya bata takardar sallama da ta wasu magunguna da ake buk'ata tayi masa godiya ta dawo d'akin ta had'a kayansu suka fito daga asibitin.
Wata bak'ar mota ce mai bak'in glass tayi parking a gabanta aka bud'e gidan baya tare da fizgota cikin motar aka rufe motar ta fita a 360. Cikin tsoro Aunty ta kalli Faheem tace "Yaya wannan ba Hibbah bace?" "Itace yi sauri mubi bayan motar" da sauri suka shiga motar Aunty ta figi motar a 360 suka bi bayan motar sai dai ina motar...................
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page4⃣4⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.W.A
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
Motar tuni ta b'ace suka kalli juna ita da Faheem wanda hankalinsa ya mugun tashi, ta karyar da kai "Yaya pls ka kwantar da hankalinka kaga baka da lafiya, insha Allah ba abinda muke zargi bane zai faru da Hibbah" ya gyad'a kai "muyi sauri Daddy yana jiran mu" Aunty ta juyar da kan motar suka nufi gidansu.
Babu kowa a babban parlor direct parlor'n Daddy suka nufa Faheem ne a gaba Aysha tana biye dashi suka shiga cikin parlor'n, dukkanin ilahirin gidan ciki manyan gidan iyayen nasu kenan. Faheem ya shigo da sallama Abba da su momy da mamy ne suka amsa Daddy ko kallonsa baiyi ba yana zagaye parlor'n, Faheem ya gaishesu Aunty ma haka nan ma Daddy bai kallesu ba. Faheem ya matso kusa da inda Daddy yake "don Allah Daddy kayi hakuri wallahi bani da niyyar.............." Katse shi yayi ta hanyar yarfa masa wani mugun mari cikin fad'a ya fara magana "Faheem ni zaka wulakanta ka nuna ban isa da kai ba, saboda kuna yiwa d'an uwanku bak'in cikin karya auri yarinyar da yake so shine kuka zage kai da Aysha kuka k'ulla makircinku har ka aureta ko? To baka isa ba tunda shima ya rasata dole kaima ka rasa, aikin banza da wofi yara sai bak'in cikin tsiya ni banma yarda da wannan auren ba tunda shi Abban Janan shine walilinku kuma ba zama yake yi ba za'ayi aure ne babu waliyyi?" Faheem ya sunkui da kansa yanaji rad'ad'i mai zafi a zuciyarsa baya so yaga ran iyayensa ya b'aci sam.
Abba dake zaune ya kalli Daddy cikin kwantar da murya yace "Daddy'n Faruq ka tsaya kayi bincike akan abinda ya faru kafin ka yanke hukunci, ni d'innan nine nayiwa Faheem waliyyi aka d'aura auren nan, ya kirani a waya yake fad'amin damuwarsa nasan Faheem akwai shi da zurfin ciki tunda har ya fad'amin damuwarsa to abin ya dameshi, ni na bashi shawarar yaje wa mahaifiyar yarinyar da maganar Allah bashi nasara daya fad'awa mahaifiyarta ta bashi aurenta a lokacin tace a d'aura, ya kuma kirana a waya ya fad'amin cewa ta amince kuma tace ya turo yanzu a d'aura auren Allah yasa ranar na shigo kano naje aka d'aura auren, don nima ina sauri ban ma shiga mun gaisa nayi mata godiya ba saidai na barwa mijinta sak'on gaisuwar. Bayan an d'aura auren mai makon naga Faheem yana farin ciki sai naga ya shiga damuwa na tambaye shi menene kuma yake damunsa, yace min yana tunanin yadda zaka d'auki zancen k'aro auransa bada saninka ba ga kuma Kausar da yayowa itama abokiyar zama ba shiri, na nuna masa karya damu indai Kausar ce, kai kuma zanyi maka bayanin komai Allah bai bani ikon kuma dawowa kano ba sai jiya da kayi min waya mukazo yau. To kaji abinda ya faru Daddy'n Faruq tun kafin ka fad'a min Faruq nason yarinyar nan Faheem yake dakon son ta a dalilin maganar da kayi musu jiya shi kuma ya yankewa kansa hukuncin sadaukarwa da Faruq ita bayan irin son da yake yi mata, sonta ne da fargabar rabuwa da ita ga kuma dakon sonta da yayi yasashi kamuwa da ciwon zuciya" daddy yayi shiru yana sauraronsa yace "naji kuma na fahimta amma yarinyar nan Faruq ya shaida min shi take so kuma ita ta amince da aurensa, don haka ke Aysha kece mai number ta ki kirata yanzu tazo ta shaida mana wa take so a tsakaninku, oya Aysha kirta kisa muna ji" Abba ya kuma kallonsa "haba Daddy wai sai yaushe ne zaka daina nunawa yaranka bambanci? Ka dinga yi musu adalci mana" "kayi hakuri Abba ka kyaleshi ai dama yayi niyyar barwa d'an uwan nasa ita to Dan nace a kirata ta zab'i zab'inta ai ba lefi bane" Abba ya gyad'a kai kawai dama su momy da mamy basu saka baki ba.
Aunty Wanda tunda suka shigo data zauna kanta yake a k'asa tana zubda k'walla tana tausayawa halin da Faheem zai shiga na rashin Hibbah a hankali ta d'auko wayarta a jaka ta shiga kiran Hibbah ta saka a speaker kowa yanaji tana fara ringing Hibbah ta d'aga cikin tashin hankali da tsoro ta Fara magana "Aunty ki taimake ni kasheni zaiyi ya kuma lalata min *RAYUWA* Faruq ya sato ni ya kawo ni wani waje zaiyi lalata dani Aunty don Allah ki taimaka......" D'if wayar ta d'auke. Aunty gaba d'aya ta tsorata da fargabar abinda Faruq zai yiwa Hibbah ta kalli kowa na parlor'n duk sun firgita suke ta kalli Daddy jikinsa yayi sanyi don tagumi ma yayi, ta maida dubanta ga Faheem gani tayi ya mik'e ya dafe kansa yana tangad'i zai fad'i kafin tayi wani yunk'uri har yazube a wajen.
Da gudu ta k'arasa kusa dashi ta shiga tana kiran sunanshi saidai ina baya ma hayyacinsa, su Abba suka k'araso kusa dashi suna tattab'ashi sam baya motsawa daddy duk hankalinsa ya tashi ya zaro wayarsa daga aljihu ya shiga kiran layin Dr Umar.
Ba jimawa ya d'auka Daddy baima jira sun gaisa ba yace "Umar kana asibiti ga munan zuwa Faheem ya fad'i" shima Dr Umar ya d'an ji tsoro saboda yanayin ciwon nasu ba'ason mutum ya dinga damuwa balle har takai ga ya fad'i "ina nan daddy garin yaya" Daddy bai tsaya bashi amsa ba ya kashe wayar. Abba da Daddy ne suka kamashi suka shiga dashi mota, Aunty da Abba suka shiga motar, Daddy momy da mamy kuma suka shiga wata motar.
Suna zuwa nurses har sun fito masa da gado aka d'orasa a kai suka shiga dashi Dr Umar yabi bayansu wani d'aki suka shiga.
Dr Umar ya kai kusan 1hour a ciki sannan ya fito daga d'akin, su Daddy da sauri suka nufoshi suna tambayar jikin nasa ya kasa magana yace "daddy kuyi hakuri muje office" yayi gaba suna binsa a baya har suka isa office d'in nashi, suka zazzauna akan kujerun office d'in.
Dr Umar ya dubi su Abba, dasu momy da hankalinsu ya gama tashi don a rikice suke, balle kuma Aysha da taketa kuka mai ban tausayi, yace "munyi k'ok'arin ceto rayuwarsa cikin ikon Allah Daddy gaskiya rayuwar Faheem tana cikin had'ari sosai zuciyarsa tana gab da bugawa, matuk'ar ba'a daina b'ata masa rai ba akwai abinda yake matuk'ar so a zuciyarsa amma kuma ana yunk'urin hanasa wannan abun, matuk'ar ana buk'atar rayuwarsa to Dan Allah Abba ayi yunk'urin yi masa wannan abun. Nan 4hours zai iya farkawa yana buk'atar hutu baza ku iya ganinsa ba" gaba d'ayansu sun kasa magana Abba ne kawai yayiwa Dr godiya suka nufi d'akin da Faheem ke ciki suna lek'ensa ta window har ya d'an fad'a duk tausayinsa ya cika musu zuciya.
Sagir mijin Aunty Aysha ne ya shigo cikin wajen ya k'araso kusa dasu ya gaishe dasu Abba da tambayar mai jiki, shima ya lek'a ta window yaga yanayin jikin Faheem d'in ya tsorata ya kalli Aysha "Aysha wai mene sanadin wannan ciwon" Aunty Aysha tasa kuka tama rasa me zata ce masa, hankalinta ya kasu biyo tana tunanin rayuwar d'an uwanta tana kuma tunanin rayuwar Hibbah a wajen Faruq, Daddy ne yayi k'arfin halin ya bashi labarin duk abinda ya faru ya d'ora da cewa "nayi nadama sagir nayi Dana sanin sangarta Faruq da nayi na lalata masa tarbiyya, na b'ata masa rayuwa sam bana ganin laifinsa idan yayi gashi yanzu yaya neman lalata Matar Yayansa Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un nayi nadama" ga mamakin kowa hawayene yake zuba a idanun Daddy.
Sagir yace "kayi hakuri daddy kabar min komai a hannuna ni da kaina yau zan fara binciken inda ya kaita yanzu zanyiwa yarana waya daga asibitin nan bazan je ko ina ba zan fara bincike akan Faru.................
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.