Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 24 of 51
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:23 PM] Maman Najma Author P1: Yana mamkin meya kawo ta gidan ya Faheem.
Hibbah kuwa tana shiga gida d'akinta ta nufa ta zube a kan gado ta shiga rera kuka, tana mai jin zafin abinda Faruq yayi mata ace a gaban saurayinka yayi maka wannan rashin mutuncin wannan wace irin *RAYUWA*ce? Ta kuma rushewa da kuka tana kuma tunano *RAYUWARTA* ta baya. Nawaz ne ya shigo rik'e da chocolate a hannunsa yana sha ya mik'o mata "Aunty kinga uncle ya bani chocolate," da sauri ta goge hawayen ta tana murmushi tace "to jeka sha Nawaz nima bara na shiga kitchen," ta mik'e ta nufi kitchen ta had'a musu dinner ta gyara kitchen d'in, tana gamawa taji ana kiraye kirayen sallah tayo alwala tazo ta gabatar da sallar, ta d'ebo abinci ta zauna suna ci ita da Nawaz sai shirme yake mata ita kuwa duk abin da Faruq yayi mata ne yake damunta har ta kwanta tana tunanin abin.
Washe gari Monday ta tashi da ciwon kai sakamakon kukan da taci jiya da dadaddare, ta tashi tayiwa Nawaz wanka ta shirya shi school bus na zuwa ya tafi, ita kuwa bata da niyyar zuwa saboda ciwon kan dake damunta don tana gama shiryashi ta koma ta kwanta sai wajen sha d'aya ta tashi tayi duk ayyukanta tana cikin yin mopping taji motsin mutum a bayanta tana waigawa taga Ashe Faheem ne tace "barka da safiya daddy" bai ma jita ba dun ya sha'afa wajen kallonta tunda suke zaune da ita sai yaune ya tab'a k'are mata kallo lokaci d'aya yaji wani abu a zuciyarshi, hazak'ar Hibbah da ayyukanta suna burgeshi sam bata nuna gajiyawarta akan duk abinda Kausar zata sata ga d'awainiyar da take yi masa da yaro. Ta kuma cewa "daddy barka da safiya," ya d'anyi firgit ya kalleta "lafiya" ya huce d'akinsa ya shiga ya d'auko takardun daya manta ya huceta, ita kuwa ko a jikinta ta k'arasa aikinta tayi wanka ta shirya tsam kamar mai fita wajen party ta shiga kitchen ta d'ora musu abinci yana yi ta juye ta jere a dinning ta koma d'aki ta d'an kwanta a hankali bacci yayi awon gaba da ita.
Cikin barci kamar a mafarki taji ana shafata taji kamar an danneta a hankali ta bud'e idanunta wa zata gani Faruq ne a kanta wani wawan ihu ta saki tare da tattaro k'arfinta ta tunkud'eshi ya fad'i k'asa da gudu ta ta fito parlor kicib'is sukayi da Faheem daya dawo hannunsa rik'e dana Nawaz da gudu ya rjn
[10/26, 9:24 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page3⃣1⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.W.A
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
Jabeer yad'an fahimci wani abu akan fuskarta amma bai son yi mata bin k'wak'k'wafi ya d'auko wata leda a cikin mota ya bata don Nawaz tuni ya tafiwajen daddy'n shi. Tayi masa godiya sukayi sallama ta shiga ciki, bata iske kowa a parlor'n ba ta shige d'akinta tare dayin 'yar ajiyar zuciya.
Labarin zuciya a tambayi fuska tana tsoran Faheem in dai ya ganta da wani jikinta yakan bata wani abu Wanda ta kasa tantance komene shi, tana son ko sau d'ayane su gaisa da Jabeer don ya fahimci irin manufofinsa, don d'an mutunci ne aurene ya kawoshi ba wai wani shashanci ba. Ta yunk'ura ta bud'e ledar wani k'amshi ya daki hancinta mai dad'i, wani material ne marun mai shegen kyau da mayafinsa da takalmi sai turare da mayuka da kud'i dubu biyar, wani card mai hoton zuciya yafi tafiya da hankalinta, ta d'akko ta bud'e kalaman k'auna ne taci karo dasu Wanda suka sanyaya mata zuciya, karo na farko da taji ta gamsu ta amince da auran Jabeer, don miji ne na k'warai ta lumshe idanu, hak'ik'ashi d'in ne take gani Jabeer yana da kirki yana Mata so na tsakani da Allah.
Faheem yana shiga d'aki yayi wurgi da jakar hannunsa ya d'ora kansa a pillow rikitaccen abun yana da rikirkita tunani da wahalar fahimta, zuciyarshi ta Gaza sarrafuwa yana da juriyar gaske akan duk abinda ya jarrabtu gareshi amma me yasa ya kasa daurewa? Allah mai iko ya dafe zuciyarsa abinda yake ji a cikinta bazai iya fad'a fatar baki ba, ya runtse idanunsa shi bai tab'a samun irin wannan matsalar Mai zafi a cikin zuciyarsa ba, ya lalubo wayarsa tare da earpiece yasa a kunnensa k'ira'ar sudais ne ke tashi harshensa nabin surar tiryan tiryan ya haddace ayoyin nutsuwa ya samu da yak'inin wani abu ba makawa zai iya kasancewa dashi.
***
Su Hibbah suna ta kiciniyar fara exams (WAEC) ta maida hankali tuk'uru wajen karatunta dan ganin result d'inta yayi kyau, sabon malami aka kawo musu don yi musu lesson d'in waec, ranar wata laraba kamar yadda suka Saba ita da fauzy suna zaune a cikin ajinsu suna solving wani physics dayake babu malami a cikin ajin, wata yarinya ce ta shigo tare da neman excuse tace "wai Hibbah Mukhtar Muhammad tazo inji uncle Sadeeq," suka kalli juna ita da fauzy sannan ta kalli yarinyar "kice masa ganinan," ta fad'a tana mik'ewa, direct office d'inshi ta nufa da sallama ta shiga ya amsa ta gaisheshi, bai amsa ba sai nuna mata d'aya daga cikin kujerun office d'in.
Ya dubeta yayi mata murmushi "barkanki da safiya 'yar kyakykyawa muryarki tana da d'an karan dad'i," ita dai Hibbah batace komai don a d'osane take akan kujerar, kanta a k'asa tana murza zoben hannunta shi kuwa ya zuba mata idanu ta tsargu da kallon da yake mata.
Matashi ne dogo siriri fari idanunsa a tsatstsaye suke irin na mashahuran 'yan duniyar nan, inyana kallon mace dole gabanta ya fad'i gashi kamar maye idan ya k'ullawa mace. Uncle Sadeeq shu'aibu kenan tunda yazo ya k'ella ido akan Hibbah ya kasa nutsuwa duk da yaga yarinyar bata hannu bace, amma idan ya k'ullawa mace saiyasan yadda yabi ya yaudareta, balke mace irin Hibbah ina zai iya bari, ai kota wane hali sai ya bi harta sallama masa don yaga kamar tsoranshi take ji.
Ya dubeta "Hibbah kenan gaskiya kina da baiwa dan nidai ban tab'a con karo da irinki ba gashi muryarki akwai sanya mutum kasala," yana wani murmushin k'eta irin nasu na salon yaudara, ya janyo take away d'insa dankali ne da k'wai sai k'atuwar kaza ya Fara ci, "bismillah, ko na baki ne a baki? Kinsan ke ta dabance" ta kalleshi mamaki yake bata sosai "na gode ni Zan koma class," "haba Hibbah me yasa? Ko kin gaji da hirar tawa? D'auko min maltina a fridge," haushi taji kawai tasan d'an iskane ba mutumin kirki bane ta mik'e ta nufi fridge din.
Ya k'urawa bayanta ido dama hikimarsa kenan idan ta tashi ya k'are mata kallo duk da hijjab d'inta yayi masa garkuwa amma hakan bai hanasa bin k'wak'wk'wafi ba. Ta ajiye masa zata tafi yayi saurin cewa "no no baby zauna tukunna ban gama ba ai," ta kuma had'a rai don dai babu yadda zatayi ne da tuni ta ci masa mutunci. Yayi dariya "smile mana Hibbah akwai lefi don nace ina sonki kinyi min ne, naga har yanzu a tsorace kike Dani ki saki ranki, ina sone mu more *RAYUWA*rmu, abinda za'ayi yanzu zan baki address d'ina ko?" Waro ido waje tayi tace "uncle me kake fad'a haka gaskiya ni ba 'yar iska bace," ta kuma bata rai tayi tunananin zaiji haushi yace ta tafi sai ma taga yayi dariya "no problem mai sonka shi yake binka don haka ni idan abu yayi min bana damuwa kiyi min kwatancen gidanku ni zanzo," ta kuma zaro ido wai ita awa takai wannan gidan Faheem ai ta shiga uku, to tamayi me da d'an bariki, "akwai dokoki da yayana ya kafa a gidansa ni bana tsayawa da kowa," ya fashe da wata muguwar dariya, da sauri ta fita tana tunanin kodai tab'ab'b'ene, ya bubbuga table d'in dake gabansa yace "ta yaro kyau take bata k'arko idan kinsan wata ai bakinsan wata ba."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.