Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 45 of 51
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page5⃣1⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
*Kulawarku da damuwa da littafina ya sani cikin farin ciki na gode sosai, masu kirana a waya basu samu ba da masu min magana ta what's up kuyi hakuri ina busy ne.*
Sai kuma baba ya ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya a hankali ya fara bud'e idanunsa ya sauke su akan na Daddy shima da Daddy kallon sa yake zuciyarsa duk ta karaya hawaye na zuba a idanunsa. A hankali baba ya d'ago hannunsa ya d'ora a saman fuskar daddy ya shiga goge masa hawayen yana masa murmushi "ka daina kuka d'an uwana ban Sonka da zubar hawaye" Daddy ma murmushi yayi "ai dole ne Mukhtar munyi kewar rashinka munyi kuka har mun gaji munsa a ranmu ka rasu sai yanzu muka sami Labarin kana raye kaga kuwa dole mu zubda hawaye farin ciki" baba yayi murmushi yana kallon duk mutanan wajen babu Wanda ya Sani a cikinsu banda momy da mamy sai kuma Faheem da yake ta kallo yana son gano waye? Ya dubi momy da mamy da suke ta matsar k'walla "autar hajiya da matar Yaya ku daina kuka Dan Allah ku matso gare ni" a hankali suka matsa kusa da baba ya rumgume su tamkar yara suka fara kuka yana d'an bubbuga bayansu.
Baba ya d'ago kansa yana kallon Abba suna yiwa juna murmushi da kuma hawaye a fuskokinsu, baba ya d'an saki su momy ya kuma duban Abba "babban Yaya wai wad'annan duk 'ya'yana ne?" Abba ya d'aga masa Kai "naka ne duka Abban Aysha" mamaki ne ya bayyana a fuskar baba yace "Abban Aysha wace Aysha? Ni banga Aysha ba da hajiya suna ina?" Da sauri daddy ya d'ago kansa jin mutanen da k'anin nasa yake tambaya hawayensa suka tsananta zuba, Abba shima hawayen yake yi yace "kayi hakuri Abban Aysha sanadin cutar da ta sameka a wannan daren Allah yayiwa hajiya rasuwa sanadiyyar hawan jininta daya tashi, Aysha kuma tashin hankali ne yasa ta nak'uda a lokacin ta haifo 'yarta mace shine aka saka mata sunan Aysha saboda ita ma Aysha bata rayu ba."
Inna lillahi kawai baba yake furtawa zuciyarsa na masa zafi a sannu rayuwar da sukayi da mahaifiyarsa da matarsa ya Fara tunowa sai kuma hawaye suka fara sauka a saman fuskarsa yasa hannu yana gogewa yana mai yi musu addu'ar samun rahamar ubangiji. Su Kansu su daddy hawayen suke yi saboda tuno mutuwar da sukayi sai filin tsakar gidan yayi shiru sun d'auki wasu lokuta a haka kafin baba ya katse shirun da cewa yana murmushi "wace Ayshan a cikinsu? Duk sun d'auko kama iri d'aya" daddy ya dubi Aunty "Aysha matso Gare shi zo ga mahaifinki" Aunty ta taso ta zo wajen baba, shi kuwa baba cikin happy ya rumgume ta k'aunarta na ratsa duk ilahirin jikinsa ita kuwa Aunty kuka take ga k'aunar mahaifinta na shigarta sun d'auki lokaci k'amk'ame da juna baba ya d'ago yana kallon su Kausar "yarana ku matso gare ni kuzo naji d'umin jikin yarana" ya fad'a yana bud'e hannayensa, matsowa su duka suka yi banda Hibbah dake gefe kusa da Umma tana ta kuka zuciyarta cike take da tsoron abinda inna ta fita yi shima Nawaz bai tashi ba yana jikin Hibbah yana goge Mata hawaye wai tayi shiru .
Su Saudat kuwa baba had'asu yayi ya rumgume su yana mai jin k'aunar 'ya'yan 'yan uwan nasa na ratsa shi, sun dauki lokaci kafin ya sakesu ya kalli Faheem "babban Yaya kar dai kuce wannan ne Faheem nawa" da murmushi Abba t?yace "shine Abban Aysha" baba ya dubi Faheem yana dariya "lallai na dad'e rabona da ku dubi fa yadda ka zama babban mutum, ina Haisam kuma?" "Haisam yana Abuja acan yake aiki" "to Allah ya bada sa'a ina dai fatan yanzu kun ajiye iyali ko?" Faheem ya d'an Sosa k'eya yana duban Abba.
Cikin dariya Abba yace "ka fad'a masa mana" Faheem ya kuma sunkui da kai daddy yayi dariya "duk sunyi aure dashi da Haisam d'in shi ya auri k'anwarsa Kausar da ka tafi Rukayya na da cikinta har ma da d'ansu Nawaz yanzu kuma ya kuma k'aro wata a sanadiyyarta ne muka gano inda kake." Baba ya dubeshi da mamaki "wace ita?" "Hibbah ce 'yar wajenka" mamaki ne ya kuma bayyana a fuskar baba gumi ya fara keto masa "Hibbah ina kike matso gare ni kiyi min afuwa ki yafe min muzgunawar dana miki ke da mahaifiyarki, kinga Rahmatu yadda mahaifiyarta ta cutar mata da *RAYUWA* ko?" Hibbah ta matso kusa da baba Nawaz ya biyota tace "baba baka yi min komai ba na yafe maka" "ina Ummanki Hibbah?" Ta nuna masa Umma.
Ya yunk'ura zai tashi daddy ya ruk'oshi, baba yayi murmushi don ya gane dalilin rik'eshin da daddy yayi "nafa samu sauki babu inda ke min ciwo" daddy ya sake shi ya k'arasa gaban Umma "kiyi hakuri Aysha ki yafe Min lefin da nayi miki don Allah" "nasan ba lefinka bane na yafe maka Allah ya yafe mana" baba yaji dad'i tace "na gode Aysha" ya dubi Nawaz "wannan ne abokin nawa?" Ya fad'a yana janyo Nawaz jikinsa ya kalli Faheem dake ta sunna Kai "Faheem wai kunyata kake ji ne? Ni ba surukinka bane fa" Faheem yayi murmushi yana kuma k'asa da kansa.
Baba yayi murmushi yana mamakin yadda Faheem shi bai yadda ba kunyar shi yake ji. Abba ya d'anyi gyaran murya "k'aramin k'anina (haka yake kiranshi) ka taya ni murna nima naga Aysha k'anwata" farin ciki ne ya bayyana a fuskar baba da kuma mamaki "a ina? Wace ita? Me yasa baku tawo tare ba?" Tambayoyin baba sun basu dariya Abba yace "mun tawo da ita mana" "tana ina? Ya baku shigo da ita ba?" Daddy ya kuma dariya saboda yadda k'anin nashi yake ta wani zumud'i "gata nan a gabanka, ai ba bak'uwa bace Umman Hibbah ce" "Umman Hibbah?" Baba ya tambaya cike da mamaki "eh ita ce" Abba ya bashi amsa sannan ya shiga bashi labari kamar yadda malam ya basu.
Baba ya jinjina kai ya dubi Hibbah " ikon allah kenan, Hibbah kinga *RAYUWA* ko? Kinga sanadin kaiki aikatau da lami tayi kin nemo danginki ko?" Hibbah ta d'ago tana kallon baba da murmushi tace "haka ne baba amma ya akayi kazo k'auyen nan?" Aunty ta kalli Hibbah tana dariya "shine kika rigani tambaya" Saudat tace "ai gara da ta tambaya aunty don na k'osa naji yadda akayi" baba yayi murmushi, Hibbah ta tsaya tana kallon fuskar baba tana mamakin yadda baba yau yake yawaita murmushi, ko dan yaga 'yan uwansa ne oho.
Baba ya katse mata tunani "ni kaina bansan yadda akai nazo nan ba nima kawai na tashi daga bacci ne na ganni a gidan su lami sai daga baya mahaifinta yake fad'a min a halin da ya since ni na hauka. Mahaifin lami shahararran malami ne a cikin k'auyen nan shine ya cigaba da bani magunguna har na samu sauk'i ya bani kud'i yace na koma garin mu saboda na bashi labari na.
Kasa komowa nayi saboda gaba d'aya ji nake na tsaneku bana son kuma rayuwa daku na fad'a masa ni bansan komawa cikin dangina ya tambaye ni dalili na fad'a masa cewar ni kawai bansan komawa bai takurani ba ya barni a gidansa na cigaba da zama. Ya koya min sana'ar da yake yi nima na shiga taimaka masa, Allah sarki malam shehu shekarar mu d'aya dashi Allah ya karb'i ransa kafin ya rasu saida ya rok'eni da na auri 'yarsa d'aya daya mallaka Fatima wato lami na amince masa duk da tarbiyyar lami sam bata yi min ba don sun shagwaba ta sam bata da kamun kai amma bazan iya bud'e baki nace masa bana son jininsa ba haka na hakura aka d'aura aurena da lami ya bani wannan gidan da muke ciki. An d'aura aurenmu da sati d'aya malam Shehu Allah yayi masa rasuwa munyi kukan rashinsa.
Ni na cigaba da Kular masa da dukiyarsa da matarsa baba mairo mata Mai mutunci da karamci, shekaramu d'aya da aure itama baba mairo Allah ya karb'i rayuwarta sanadiyyar ciwon cikin da tayi ta fama dashi.
Tunda mukayi aure da lami bata tab'a haihuwa ba shine sanadiyyar auren Aysha da nayi har ta Haifa min Hibbah amma abin mamaki na kasa kula da su hasali ma tsanarsu nayi sam bana son ganinsu, sai gashi kuma Aysha tazo tana cin amanata. Ina kasuwa malam Haruna mijin k'awar lami yazo yana fad'amin cewar Aysha fa tana ta rayya da maza don ganin idanunsa shi shaida ne na zo gida Sam babu bincike na saki Aysha ashe tuggu lami ta had'a ita da kawarta delu, sai daga ba malam Haruna yazo yana neman yafiya ta ya fad'a min cewar sharri suka yiwa Aysha" baba ya d'ago ya kalli Umma da Hibbah "Ku yafe min don Allah" "na yafe maka ni tuntuni" "baba ni baka yi min komai ba"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.