Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rayuwa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 28 of 51
Ya bud'e mata gaban motar don yasan halinta sai ta zauna a baya, ta kalleshi gani tayi ya had'a rai babu alamar wasa a tattare dashi shiyasa ba musu ta shiga. Ya dad'e bai ji annashuwa ba kamar a yanayin nan ya kunna wakar Celine Dion yana sauraron baitukan wak'ar, yana tuk'i cikin nutsuwa, Hibbah ko numfashi bata yi k'wak'wk'wara ji take yi tamkar ta nutse, kunya ce nauyi ne rashin sabo ne, duk sunyi Mata dabaibayi don basu tab'a had'uwa haka gata gashi ba.
Ya dubeta a nutse domin duk damiwarsa babu ita ashe Hibbah ce ta hana zuciyarshi nutsuwa, "Hibbah ta Nawaz ya kikayi shiru ne na takuraki ko? Banji dad'i bane akan abinda ya faru ashe fushi ne dake haka, ki sani nayi miki fad'ane don kawai na damu dake ina kishinki tamkar k'annena su Safiyya ya d'auke ki badon haka ba babu ruwana da ra'ayin wani, ina data dai kin huce ko?" Bata ce komai ba, ya dubeta idanunta sunsha kuka kuwa, zata kuma iya ci gaba da yinsa idan har ya takurata sai yaji maganarta don a takure take ya Sani, shi kuwa so yake ta saki jiki dashi ta daina jin tsoranshi haka don haka ya rabu da ita, da haka har suka k'arasa asibitin.
Yana gaba tana binsa a baya, sama suka hau basuyi wata tafiya ba suka isa d'akin, suka shiga ta gaishe dasu momy lokacin Nawaz yana barci momy ta mik'e zata tafi wai dama shi take jira ya dawo yamma tayi sukayi sallama tayi masa fatan samun sauk'i suka tafi.
Jimawa kad'an Nawaz ya tashi yana ganinta ya mak'aleta yana k'yalk'yala dariya kamar zata sake gudu ta barshi, ta shafa kansa tana dubansa yayi 'yar rama ta share k'wallar data taru a idanunta. Nawaz ya rik'e hannayenta "aunty Hibbah shine kika gudu wajen Ummanki kika barni kinga inda doctor yayi min allura," ta tab'a wajen "sannu Nawaz Allah ya baka lafiya," "Aunty Hibbah nima zan biki wajen Umma."
Ta gyad'a Kai "to naji amma sai ka ji sauk'i zamuje," ta ja hannunsa suka fice barandar suna kallon titi dayaga abinda ya bashi sha'awa sai ya dinga nuna mata suna dariya, yana ta bata labarin abinda ya faru bayan tafiyarta.
Yana tsaye ya hard'e hannayensa a k'irjinsa yana kallonsu sun burgeshi da Bashi tausayi "Hibbah" ya ambata a zuciyarsa sunan mai dad'i, ga mamakinsa ashe maganar ta fito fili har tabi iska ta isa kunnenta kawai gani yayi tad'an juyo ta kalleshi, suka had'a idanu cikin wani yanayi a hankali ta d'auke kanta, wani sanyi take gani cikin idanunsa sai taji abin yana mata yawo a k'wak'walwarta.
"Hey! My boy," duk suka dubeshu, yayi zanzaro da hula Hana sallah a kansa, da siririyar sark'a tana k'yalli a wuyansa har taso ta shak'e sa, "Yaya ya jikin boy d'in?" "Alhamdulillah yaji sauk'i sosai," hankalinsa yana kan Hibbah bai ko damu da ganin Faheem ba, ya d'auki Nawaz ya rumgume shi tare da yi masa kiss a kumatunsa, shi kuwa ya mak'ale hannayensa a wuyansa tare da zagaye k'afafunsa a jikinsa, Faruq kenan yana k'aunar Nawaz shiyasa shima Nawaz yake k'aunar uncle d'in nasa.
Hibbah kuwa kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanata don har yanzu tsoransa take ji...............
*by*
*Mamyn Najmah*
[10/26, 9:25 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*RAYUWA* page3⃣5⃣
*NA*
*MAMYN NAJMAH*
🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
D.B.A.W
*DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA*
Ya kalli inda Faheem yake a tsaye bashi ba dalilinsa, ya matso kusa da ita abinda bata so kenan, shi a wajensa ba wani abu bane don ji yake kamar ya rumgume ta, wutar k'aunarta yana faman huruwa a zuciyarsa duk sanda ya d'ora idanunsa a kan idanunta baya iya sarrafa kansa, ya matso sosai kusa da ita, bata da niyyar kulasa, "Hibbah kinsan kuwa irin sonda nake miki? Kada ki maida hannun agogo baya bana so ki dinga tuna baya ban tab'a tsintar kaina a irin wannan love d'in ba Hibbah." Ya dafa kafad'arta, a taorace ta kalleshi suka k'urawa juna kallo na d'an wani lokaci abinda ta gani a idanunsa tad'an tsorata don tabbas binda ke zuciyarsa ya fad'a, ta ture hannunsa.
Yayi murmushi "wannan gangar jikin mallakina ce sai nayi yadda nake so da ita in munyi aure, don haka ki dena guduna , ni d'in nan zan baki mamakin yadda zaki yi dadi indan na zama mijinki," murmushi tayi don ita a ganinta wauta kawai yake tace "abinda kamar wuya, naji zancen kamar almara ta Yaya zaka aure ni? Ka tuna fa kaso k'unsa min b'ak'in cikin da har na mutu bazan manta shi ba, kuma badon komai ba kawai don zalinci da son Kai, karma ka Fara yaudarar kanka don yarda ba yadda za'ayi dakai wai kai masoyina ne, don Allah na rok'eka saboda girmanasa ka k'yale ni ka k'yale min rayuwa haka." Ya kad'a kanshi "duk abinda kika fad'a gaskiya ne ni kaina ina cikin mamaki da tuhumar kaina Yaya akayi na samu kaina cikin sark'ak'iya har na fad'a tarkon sonki, banji haushi ba ai na fad'a miki kyauta kika sadaukar min da kanki wallahi zuciyata bazata iya daure wani abu dake ba matuk'ar ba aure mukayi ba," "ni kana bani mamaki to wai taya zamuyi aure? Wannan shirmen tunani ne abinda bazai yiwu ba." Yaji zafin maganarta ya take k'afafunta da takalmin k'afarsa, ta runtse ido saboda zafi, Faruq mugune yasan takan mugunta. Ya tallafo tallafo hab'arta yana wannan murmushin nasa na k'eta "dube ni sai na aure idan yaso in na aure ki ki hak'a rami ki binne ni da raina ko kuma kii gunduwa gunduwa da nama na saboda tsabar k'iyayyar da kike min," ya k'ura mata idanu tak'i bud'e idanunta, ji yayu tamkar ya lashi kumatunta, ya hurawa idanun iskar bakinsa duk da a rufe suke.
Ta bud'e idon tana dubansa shed'anin mutum kenan gani take kamar baya hankalinshi, Anya ma Faruq baya shan k'waya don abubuwan da yake yi kamar bashi da tunani a k'wak'walsa, duk inda ake neman namiji mai kyau Faruq ya kai sai bashi da hali.
Ya lakuce mata hanci, ya matso da kansa kusa da ita sosai ya sassauta murya "ke d'innan yadda kika shiga raina, ni sonki nake Hibbah kamar nayi hauka don Allah me kika yi min ne?" Ta juyar da kanta gefe, ya sa dariya "kin mai dani dodo ko Hibbah?" Yayi k'wafa "wata rana sai kin rumgume ne kinmin kiss, ni kuma shagwaba zan tayi miki," ya d'an ja da baya "ki samu cikin addu'a Allah yasa muyi aure."
Ta gyad'a kai cike da mamaki don ita wasa ta d'auki abin "aure? Wani banbarakwai nake jin abin na fad'a maka abin da kamar wuya taya ma hakan zai faru?" "Insha Allah za'ayi, ki fad'a min *I love you* zanji dad'i," kamar ta kurma ihu take ji ta rasa wanda zata cewa tana so sai Faruq.
"Kinsan halina sai na rumgume ki a nan ni babu ruwana gara ki fanshi kanki kawai kiyi abinda nace," tasan halinsa sarai zai aikata "amma ko na fad'a ka sani tursasani kayi kar kayi tunk'awo dashi *I LOVE YOU*" ya tuntsire da dariya, haushi yasa idanunta sukayi narai narai ya rik'o hannunta ta fizge don zuciyarta zafi take, da sauri tabar wajen yana ta shek'a mata dariya babu abinda yake so kamar yaga yasa Hibbah a gaba har tayi kuka, sai yaji wani sonta da k'unarta na shigarsa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.