Abnur Complete Hausa Novel
Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 10 of 24
*Page* *11*
Do anyone of you have any problem?
tambayan da ya fara yi kenan,
cikin girmamawa duka suka amsa da
"No Sir"
"Good"
sai da ya É—an kalle gefen da take, kafin ya mayar da kallonsa a kan dukkan ma'aikatan gidan dake gabansa,
"Let me go straight to the point, wannan da kuke gani"
ya juya ya kalleta, suma duk juya wa sukayi suka kalleta, kafin suka mayar da kallonsu gareshi.
"Amana ta ce!,so ina so ku bata dukkan wani respect she deserves,I hope you understand?"
"Yes Sir" suka haÉ—a baki wajen faÉ—a.
"You may introduce yourselves to her"
ya faÉ—a yana komawa ya jingina da kujera yana latsa wayarsa.
ÆŠaya bayan É—aya suka shiga gabatar da kawunansu, tun daga bodyguards É—in gidan, zuwa masu kula da flowers, masu gadi,masu kula da motoci,masu kula da tsaftace gidan, sannan su Asabe waÉ—anda sune suke da ragamar komai da ya shafi kitchen É—in gidan.
a dai dai nan Taufeeƙ ya shigo falon, da sauri ya ƙarasa yana faɗin
"Sorry Sir, I was late,wallahi..."
ÆŠaga masa hannu yayi bai ce komai ba, yana cigaba da abinda yake yi a wayarsa,
ganin abinda akeyi yasa Taufeeƙ yin shiru,har last person ya gama introducing kansa kafin Taufeeƙ ya karɓa da faɗin
"And I am TaufeeÆ™ Muntasir, his personal assistant,
Ni nake kula da duk wani abu na Sir Zannur,kama daga kayan sakawarsa,inda zaije, waÉ—anda zai haÉ—u dasu, da sauransu".
Ya kai ƙarshen maganan yana murmushi,kallonsu tayi tayi,ba tare da tace komai ba, can kuma ta nisa tace,
"Nagode sosai da gabatar da kanku da kuka yi a gareni, Ni sunana Noor, kuma Ni ma...."
"What the hell are you trying to say",
ya faɗa da sauri har yana ƙoƙarin ƙwarewa yana zare mata ido.
Da sauri tayi baya, tana kallonshi itama,ta kasa cewa komai,to miyene a ciki idan ta faÉ—a musu cewa ita matarsa ce.
TaufeeÆ™ ma da mamaki ya ke kallonsa, da sauri ya juyo ya kalli staffs É—in sa yace
"You may all leave"
juyawa sukayi suka fara ficewa a cikin falon suna tunanin to wacece wannan É—in a wajensa,
TaufeeÆ™ ya bisu da ido har suka gama ficewa, kafin ya juya ya kalli su Amina ya musu alama da ido,
da sauri suma suka tashi suka nufi kitchen,Amma harga Allah sunason sanin me ke faruwa.
Yasira da ta kasa nutsuwa, ta maƙale dan taji abinda yake faruwa, ganin bata shigo ba yasa Asabe leƙowa tana ɗaga murya tare da Faɗin,
"Wallahi Laɓe dai ba kyau ne dashi ba fisabilillahi"
da sauri Yasira ta ƙarasa kitchen ɗin, tana tsinewa Asabe a zuciyarta dan tasan Sir ya ji abinda Asaben ta faɗa.
Duk da yaji amma bai damu ba, mai da kallonsa yayi ga Noor dake tsaye tana kallonsa a tsorace,
"WHO do you think you are?
ya tambaya yana matsowa kusa da ita
ÆŠan matsawa bawa tayi itama ba tare da tace komai ba.
Cikin kakkausar murya ya sake faÉ—in "ki bani amsata, ke wayece a cikin gidannan".
Cikin matuƙar shakka da tsoronsa da taji ya shigeta tace "Ni matar....."
"Darn it!" ya faÉ—a yana buga kujerar gefensa, sannan ya É—ago jajayen idanunsa yace
"don't ever make that mistake,a duk rayuwarki kar ki kuskura ki taɓa furta ke matata ce, ke amana tace da Nenne ta barmin bayan haka baki da wata matsayi a zuciya ko kuma rayuwata,ina fatan kin fahimta?"
da sauri ta gyaÉ—a masa kai idanunta na kawo ruwa,
ta É—aga kai ta dubi TaufeeÆ™ da ya sunkuyar da kansa yana jin ba daÉ—i, he is sure Sir will regret this one day.
"Ke me ce ce a wajena?" ya sake jefo mata tambayan yana kafe ta da ido,
da sauri tace "Ni amanar kace da Nenne ta baka, bayan haka bani da gurbi a rayuwarka"
"Good, from now on, duk abinda kike buƙata ki tambayi Taufeeƙ,I don't think I have anything to do with you".
Daga haka ya juya yayi wucewarsa sama ya barta a nan a tsaye.
Ƙarasowa Taufeeƙ yayi yana kallonta kafin cikin matuƙar girmamawa yace,
"Madam kiyi haƙuri, komai zai wuce, i am sure shi kansa bai san me ya ke so ba,but Ni na san ko shi waye,ba zai taɓa wofintar da rayuwar ki ba.
A hankali ta ɗaga idanunta da suka ɗan yi ja kaɗan tana kallonsa sai kuma tayi murmushin ƙarfin hali tana faɗin,
"babu komai,Ni kaina bana so na zama komai a rayuwar sa,iya amanan da ya riƙe ma Nenne na ya ishe Ni, kuma bazan daina gode masa ba, bisa taimakon sa a gareni"
Daga haka ta juya da sauri tana tattare rigarta ta haura saman ta barshi anan tsaye yana tunani,shima juya wa kawai yayi ya nufi main kitchen na gidan.
Karo yaci da Amina dake fitowa daga kitchen É—in da manya manyan warmers zata kai dining hall,
Da sauri ta ja baya tana faɗin"Sir Taufeeƙ kana buƙatar wani abu ne".
Murmushi yayi yace
"jeki shirya table É—in sai ki kiramin Asabe, ku sameni a garden akwai maganar da zamuyi Ni da ku".
"Ok Sir TaufeeÆ™ angama, Allah dai yasa da É—umi É—umin ta zaka bamu"
"Idan kunzo zakuji ai" ya faÉ—a yana juyawa ya bar wajen.
Tunda ta shiga É—akin ta saka key tafaÉ—a gadonta tana jin kuka na taho mata amma bata so tayi,
dan bata ga dalilin yin su ba,
ita kanta sai yanzu take ganin wautar ta da har take ƙoƙarin nuna kanta a matsayin matarsa.
Miƙewa tayi ta zare rigar jikinta tana yin cilli da ita
"Bazan sake saka rigar Bama,to ma wa yace ya bani rigar, mtsww,ta sake hararar rigar.
Miƙewa tayi ta tsaya hankalinta a kwance dan dai ta san ta kulle ƙofar babu mai shigo mata, daga ita sai white clean bra ɗin jikinta da kuma gajeren wando iya gwuiwarta,
a hankali ta ƙara sa cikin toilet ta sako bathtub fari tass ta dawo tayi kwanciyarta tana sake tura baki.
Rufe laptop É—in yayi yana jingina da gado,a hankali ya furta
"wato ga mai da bathrub kaya"
sai kuma yayi murmushi yana lumshe idanunsa,fararen ƙafafuwan ta zuwa gwuiwarta da kuma fararen cikakkun breast ɗin ta da ke cikin bra kawai idanunsa suke hasko masa,
Da sauri ya buÉ—e idanunsa da har sun fara canza kala daga farare tass zuwa ja,
hannunsa ya sa ya shafa sumarsa,sannan ya gyara kwanciyarsa a kan gadon yana sauƙe numfashi.
Ƙarar wayar sa yasa ya janyota a hankali yana ɗagawa
"Habibi me ya ke damunka ne,what's keeping you this busy?"
Abinda Maami ta fara faÉ—i kenan.
Cikin kwantacciyar murya mai nuna akwai abinda ke damunsa yace
"Maami na!"
take Maami ta rikice ta soma jero masa tambayoyi
"son are you alright?,am sure you are not, me ya faru? faÉ—a ma Maami kaji, ko nazo Nigeria?,"
Cikin son ya kwantar mata da hankali yace
"Maami, babu komai fa, but akwai wani magana da nake so nayi dake, a very serious one"
Ya faÉ—a yana lumshe idanunsa
"Ina jinka Habibi tell me"
"Ba ta waya ba,zanzo Dubai"
When?
"Next week"
"Allah ya kaimu,but you are sure babu abinda ya sameka koh"
"Maaamiiiii"
Ya faÉ—a yana jan sunan,
Dariya tayi kafin a hankali tace
"Habibi bazaka gane ba,I won't be able to do without you, you are my life Habibi".
"I know Maami, and you are mine too,Abbu ya dawo daga ukraine?"
Ya tambaya da kulawa,
"Bai dawo ba but Gobe insha Allah Zai dawo"
"Ok Allah ya kaimu"
"Ameen"
"I guess I will hang up now Habibi, we will talk later okay"
"Uhm" ya faɗa ƙasa ƙasa
"Okay bye Maami loves you" Bata jira amsar sa ba ta katse wayar ta.
Ajiye wayar yayi yana miƙewa dan tafiya masallaci.
Yadda suka yi tagumi suka ƙura masa idanu yasa Taufeeƙ ɗan murmushi yana kallon su Amina yace
"kai haba duk kallon na me ne ne haka"
Cire tagumin Asabe tayi tana faÉ—in "to Sir TaufeeÆ™ ba dole ba, tun É—azu ka kasa faÉ—a mana maganan da ka kiramu a kai, kuma kasan waccar jarababbiyar yanzu zata fara nemanmu a kitchen".
Murmushi yayi sannan ya ce
"okay tom kuna jina"
suka amsa da
"eh" kafin ya cigaba da magana
Sai da ya faÉ—a musu duk abinda ya sani ga me da auren Sir Zannur kafin ya É—aura da faÉ—in
"Kunsan me yasa na faÉ—a muku"
Girgiza masa kai sukayi mamaki ya ƙi sake su,
"Ok,so nake ku ja ta a jiki, ku nuna mata komai,kunga Ni namiji ne, sannan bana tunanin Sir zai nuna mata komai,dan Allah kar ku bari tayi kaÉ—aici,
and kamar yadda kuka sani, mu biyar kaɗai muka sani banda ƴan ƙauyensu, please Kar ku faɗa ma kowa matar Sir ce kunji?"
Asabe ce ta sauƙe ajiyar zuciya tana faɗin "ai kuwa akwai shidan mu wallahi".
TaufeeÆ™ yace "waye?"
Waye kuwa banda Yasira itama tasan Matar Sir ce, dan sanda ka faÉ—a mana,ina kyautata zaton taji.
Shiru yayi sai kuma yace babu damuwa, na san yadda zanyi da lamarinta ku dai kuyi abinda nace .
"Baka da damuwa Sir"suka faÉ—a a tare.
Miƙewa yayi yace "I know I can count on you both nagode sosai"
Haba haba Sir TaufeeÆ™, ya kana haka, ai duk taimakon kai ne ko ba haka ba Asabe?
"Haka take"Asabe ta faÉ—a tana dariya.
Shi dai bai sake cewa komai ba ya juya ya bar garden É—in,
suma miƙewa sukayi suka bar garden ɗin suna jinjina maganan.
Yasira dake laɓe ta fito tana murmushi, a fili ta furta,
"Sir Zannur zan tabbatar da na mallakeka, kuma wannan shine mataki na farko da zan mallakeka, tabbass na san yanda zanyi anfani da labarin nan in samu abinda nake so".
daga haka ita ma tabi bayansu Amina dan dama tun fitowarsu ta biyo su dan tace musu su koma bakin aiki amma ganin inda suka nufa yasa ta bisu taga me zasuyi a wajen.
Washegari kamar yadda Zannur yayi umurni haka Taufeeƙ ya ɗauke ta, ya kaita sukayi shopping ɗin duk abinda zata ɓuƙata,
kama daga kayan sakawa,zuwan kayan shafa,da ma duk wasu kayan anfani na mata.
ganin bata san wasu abubuwan ba yasa ya haÉ—ata da ma'aikatan wajen kasancewar babban supermarket ne na manya, yasa matar ta zage ta kwasa mata komai kamar mahaukaciya,
and daÉ—in daÉ—awa ce mata da TaufeeÆ™ yayi she is important to Sir Zannur, kuma shi ya turo su,
ai kuwa sun sha shopping kamar na hauka har yamma tukun suka dawo gida.
Su Amina su suka shirya mata komai,
sannan suka nuna mata yadda ake anfani da komai, duk da yawanci kafin ma su faÉ—a take karantawa ta gane miye ne sai dai a nuna mata yadda ake anfani da shi.
Haka suka saka ta, ta shirya suka zagaya da ita gaba É—aya gidan,
a ranar ta sha mamaki ganin irin girman gidan,wani irin mutum ne shi kuwa? tambayar da ta yi ta yi ma kanta kenan.
Zuwa yanzu ta gama sabawa da gidan dan kuwa kwananta shida kenan,amma har ranan bata sake sakasa a ido ba,
TaufeeÆ™ ma sai jifa jifa take ganinsa,
su Amina sune abokan hirarta, har kitchen take zuwa ta zauna, suna hirarsu,
Yasira kam tsakaninta da ita gaisuwa,idan ta gaisheta ta amsa shikenan babu abinda ke sake haÉ—ata da ita.
What?
Maami ta faɗa ta ƙarfi tana miƙewa, me kike nufi?, You must be out of your senses, do you want to tell me Habibi yayi aure ba tare da nasani ba!?,wannan ma ai maganar banzace,
Shiru tayi tana sauraron mai maganan daga haka ta katse wayanta tana kallon farin balaraben dake gefenta da laptop akan cinyarsa yana operating,
idanunsa sanye da fararen medicated glasses.
Abbu, kanajin wata maganar banza, wallahi i won't take it,I am leaving for Nigeria tomorrow morning.
Ta faÉ—a zama kusa dashi,É—agowa yayi ya dubeta sannan cikin kulawa yace
"What happened Hilwa!"
Wai Habibi yayi aure,ake faɗamin, zancen banza, zancen hofi,Ni nasan hakan bazata taɓa faruwa ba da amincewata ba, saboda haka zan tafi Nigeria,dama ina so inga Habibi, jikina Yana bani Yana cikin wata damuwa.
Janyota yayi yana manna mata kiss a forehead kafin yace
"ok but ki kwantar da hankalinki,Zannur yana lafiya,and bazai yi aure bada yardar ki ba, so now smile"
Murmushi ne ya suɓuce mata,ya shafa kanta yana murmushin shima,shigewa jikinsa tayi tana faɗin
"Abbu what if da gaske yayi auren?,kasan Habibi Yana da Zurfin ciki.
"Ki kwantar da hankalinki everything that happens is for the best okay,zan sa ayi miki booking flight É—in don't worry".
Ta gyaɗa masa kai tana sake kwantar da kanta a ƙirjinsa, tana tunanin Allah yasa ba da gaske bane dan kuwa bazata taɓa yadda da hakan ba.
*💖ABNUR💖*
*By* *maimoon* 🤓
*Elegant* *online* *writers* 📚📖
*Free* *book*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.